Wane ne sabon sufetan ƴansandan Najeriya Tunji Disu?

Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Najeriya ya sanar da naɗin Olatunji Rilwan Disu a matsayin sufeta-janar na ƴansandan kasar, bayan ajiye aikin tsohon mai riƙe da muƙamin Kayode Egbetokun.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar, Tinubu ya ce ya amince da ajiye aikin Sufeta-Janar Kayode Egbetokun "bayan ya miƙa takardar ajiye aiki bisa dalilai na iyali".

Tinubu ya gode wa tsohon sufeta-janar ɗin tare da yaba masa "bisa gomman shekaru da ya kwashe yana hidimta wa rundunar ƴansandan da kuma Najeriya".

A watan Yunin 2023 ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Kayode Egbetokun a matsayin sufeta-janar na ƴansandan ƙasar, da sa ran zai yi jagoranci na tsawon shekara huɗu, zuwa watan Yunin 2027.

Sanarwar ta ce "bisa la'akari da matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar, da kuma dogaro da dokokin ƙasa, Shugaba Tinubu ya amince da naɗa Mataimakin Sufeta-Janar na ƴansandan Najeriya Tunji Disu a matsayin mai riƙon muƙamin Sufeta-Janar na ƴansanda, inda zai fara aiki nan take.

"Kamar yadda dokar aikin ƴansanda ta 202 ta tanada, Shugaba Tinubu zai kira taron Majalisar Ƴansanda ta Najeriya nan ba da daɗewa ba domin duba cancantar naɗin AIG Disu, inda bayan haka ne za a tura sunansa zuwa ga majalisar dattijai," a cewar sanarwar.

Wane ne Tunji Disu?

An haifi Olatunji Rilwan Disu ne a jihar Legas da ke kudu masu yammacin Najeriya ranar 13 ga watan Afurilun 1966.

Ya shiga aikin ɗansanda ne a ranar 18 ga watan Mayun 1992, inda ake sa ran zai yi ritaya daga aiki a wannan shekara ta 2026.

Tunji Disu shi ne ya shugabanci sashen kai ɗauki da tattara bayanan sirri na rundunar ƴansandan Najeriya bayan sauke wanda ya gabace shi, Abba Kyari.

Haka nan ya riƙe muƙamin kwamandan Rundunar kai ɗaukin gaggawa ta jihar Legas.

Ya kuma taɓa zama mataimakin kwamishinan ƴansanda a sashen tafiyar da lamurra na shalkwatar ƴansandan Najeriya da ke Abuja.

Ya taɓa zama mataimakin shugaban sashen binciken manyan laifuka a oishin ƴansandan Najeriya, a jihar Rivers.

Haka nan ya taɓa zama kwamandan tawagar ƴansandan Najeriya da aka tura yankin Darfur naƙasar Sudan ƙarƙashin shirin tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

A ɓangaren karatu, Disu ya yi digirinsa na farko a harshen Ingilishi a Jami'ar Jihar Legas (LASU), sai ya yi digiri na biyu a harkar gudanar da mulki a jami'ar Adekunle Ajasin da ke jihar Ondo.

Ya kuma halarci kwasa-kwasai a Najeriya da ƙasashen ƙetare, kamar: Horo kan yaƙi da safarar ƙananan makamai a ƙasar Botswana, Horo kan zamba ta intanet a jami'ar Cambridge da ke Birtaniya, Kwas kan dabarun shugabanci a kwalejin horas da jami'an ƴansanda da ke Jos, Binciken ƙwaƙwaf da zaƙulo bayanai kan manyan laifuka a Jami'ar Legas, da dai sauran su.