Real Madrid na zawarcin Cambiaso, ƙungiyoyin firimiya na son Nmecha

Lokacin karatu: Minti 2

Borussia Dortmund za ta buƙaci a biya ta Euro miliyan 70 kan ɗanwasan tsakiyar Jamus mai shekara 25 da Manchester United da Chelsea ke zawarci, Felix Nmecha. (Bild - in German)

Liverpool da Manchester United da kuma Tottenham na bibiyar ɗanwasan RB Leipzig da Ivory Coast, Yan Diomande amma cinikin zai fuskanci tangarɗa saboda rashin tabbacin ko wanene wakilin ɗanwasan mai shekara 19. (Telegraph - subscription required)

Manchester City da Liverpool da kuma Real Madrid na zawarcin ɗanwasan bayan Juventus mai shekara 26 kuma ɗan Italiya, Andrea Cambiaso. (Caughtoffside)

Barcelona ta shirya tattauna yadda Manchester United za ta sayar mata da ɗanwasan gaban Ingila Marcus Rashford amma tana neman a sake lale a cinikin ɗanwasan mai shekara 28 (Sport, via Mirror)

Rashford ya zaɓi zama a Barcelona a madadin komawa Manchester United - duk da dai ya nemi a bashi damar riƙa fara wasa da shi a duk lokacin da ƙungiyar ke da wasa (Marca - in Spanish)

Manchester United ta mayar da hankali kan zawarcin ɗanwasan Napoli da Scotland Scott McTominay, mai shekara 29 (Teamtalk)

Barcelona ce kan gaba a jerin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗanwasan Bournemouth da Argentina, Marcos Senesi, mai shekara 28.(Football Insider)

Arsenal na shirin gabatar da tayin ɗanwasan bayan Ecuador mai shekara 24, Piero Hincapie daga Bayer Leverkusen (Teamtalk)

Juventus ta fara tattaunawa da mai tsaron ragar Tottenham da Italiya, mai shekara 29 Guglielmo Vicario, (Gazzetta, via Standard)

Aston Villa za ta bari ɗanwasan tsakiyar Ingila Morgan Rogers ya yi sallama da ita, amma za ta nemi a biya ta diyyar aƙalla fam miliyan 100 kan danwasan mai(GiveMeSport)

Newcastle United na shirin sayar da ɗanwasan tsakiyar ta mai shekara 25 wanda ke tashe a yanzu, Anthony Gordon, (Talksport)