Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Labarin wasanni daga 22 zuwa 27 ga watan Fabrairu 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Lahadi 22 zuwa 27 ga Fabrairu 2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. , Daga Jaridu

    Manchester United na tunanin sake sayen dan wasan tsakiya na Scotland Scott McTominay kan Yuro miliyan 80 (£70m) a lokacin bazara, inda Napoli ke shirin karbar kudin dan wasan mai shekaru 29 shekaru biyu kacal bayan ya koma kungiyar ta Italiya daga Old Trafford. (Fichajes)

    Real Madrid na sa ido sosai kan dan wasan tsakiya na Tottenham Micky van de Ven mai shekaru 24, yayin da ake ganin babu alamar cewa dan wasan Netherlands zai rabata hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da kungiyar ta Premier League. (Teamtalk)

    Brighton na fatan kammala yarjejeniyar sayen dan wasan gefe na Cologne mai shekaru 19 Said El Mala ta hanyar sayen dan uwansa, dan wasan gaba mai shekaru 20 Malek. (Times)

    Manchester United na duba yiwuwar daukar ɗan wasan tsakiya na Ivory Coast na Nottingham Forest, Ibrahim Sangare, mai shekaru 28, a ƙoƙarinta na neman wanda zai maye gurbin ɗan wasan Brazil, Casemiro, mai shekaru 34. (GiveMeSport)

  2. Za a buga gasar kofin duniya a Mexico duk da kalubalen tsaro - Sheinbaum, Gasar kofin duniya

    Shugabar Mexico, Claudia Sheinbaum ta ce akwai tabbacin samar da tsaro a lokacin gudanar da gasar Cin Kofin Duniya a bana a kasar, bayan kama da mutuwar shugaban kungiyar safarar miyagun kwayoyi da ake ta nema ruwa a jallo da ya haifar da tarzoma da kafa shinge da kone-kone da ta jefa fargabar tsaro, musamman a jihar Jalisco.

    Da aka tambaye ta ko gasar kwallon kafa — wadda ake sa ran magoya baya da yawa za su ziyarci birnin Mexico da Monterrey da Guadalajara — za ta iya zama barazana ga baki, Sheinbaum sai ta ce “babu wani hadari.”

    Ta kara da cewa al’amura na komawa yadda suke bayan mambobin kungiyar safarar miyagun kwayoyi sun kai jerin hare-hare a ranar Lahadi, bayan wani sumame da aka kai domin kama shugaban Nemesio Oseguera, wanda aka fi sani da “El Mencho,” wanda ya mutu a sakamakon arangamar.

    Shugabar ta ce an sake kafa wasu shingen a wasu hanyoyi da dare, amma jami’an tsaro na aiki domin dawo da zaman lafiya.

    Mexico na shirin karɓar bakuncin wasa 13 cikin 104 da za a yi a gasar Cin Kofin Duniya.

    Hudu daga cikinsu za a yi a birnin Guadalajara. Haka kuma kasar za ta karɓi bakuncin wasu wasannin gwaji kafin bikin buɗe babbar gasar tamaula ta Afirka ranar 11 ga watan Yuni.

  3. Loftus-Cheek zai yi jinyar kusan mako takwas in ji Milan, Serie A

    Watakila ɗan wasan AC Milan, Ruben Loftus-Cheek zai yi jinya kusan mako takwas bayan da aka yi masa tiyata sakamakon karya mukamuki bayan karo da ya yi da mai tsaron bayan Parma, Edoardo Corvi ranar Lahadi.

    An fitar da ɗan wasan tawagar Ingila daga filin a kan gadon ɗaukar marasa lafiya bayan da ya ji raunin a kusan minti na 10 a gasar Serie A da suka buga a San Siro.

    Milan, wadda ta sha kashi 1-0 a wasan, tana matsayi na biyu a teburin gasar, maki 10 tsakani da Inter Milan mai jagoranci, za kuma ta ziyarci Cremonese ranar Lahadi mai zuwa.

  4. , Daga Jaridu

    Casemiro zai sami damar komawa Amurka lokacin da kwantaraginsa a Manchester United zai kare, inda ɗan wasan tsakiyar zai iya komawa wata babbar kungiya a kasar ta Amurka (Telegraph)

    Liverpool na iya duba bukatar yin musaya da Real Madrid, da za ta kai ta ga daukar ɗan wasan gefen Brazil, Rodrygo, mai shekaru 25, yayin da ita kuma za ta ba wa Madrid din ɗan wasan tsakiya na Hungary, Dominik Szoboszlai, mai shekaru 25. (Fichajes)

    Kocin Chelsea, Liam Rosenior, ba ya son barin ɗan wasan gaba na Ingila mai shekara 23, Liam Delap ya tafi a wannan bazarar, a dai-dai lokacin da Everton ke sha'awarsa. (Football Insider)

    Crystal Palace za ta ba wa kocin Austrian Oliver Glasner damar ci gaba da jagorantar ƙungiyar har zuwa ƙarshen kakar wasa. (Football Insider)

  5. Torino ta kori kociyanta, Baroni ta ɗauki D'Aversa, Serie A

    Torino ta kori kocinta, Marco Baroni ta maye gurbinsa da Roberto D'Aversa, saboda mummunan sakamako da kungiyar ta samu da ya sa take da tazarar maki uku tsakaninta da ƴan karshen teburi a Serie A.

    Torino tana matsayi na 15 a teburin gasar, kuma ta samu nasara ɗaya kacal a wasa bakwai a baya-bayan nan, kuma shan kashi 3-0 da ta yi a hannun Genoa ranar Lahadi, shi ne wasan karshe da Baroni ya jagoranta.

    A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a daren Litinin ta ce: “Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Torino na farin cikin sanar da cewa ta mika ragamar horar da ƴan wasanta ga koci Roberto D'Aversa. Kuma tuni kociyan ya sanya hannu kan yarjejeniyar da za ta kare ranar 30 ga watan Yunin 2026.”

    D'Aversa ya fara aikin horar da tamaula a matakin ƙwarare a AC Milan, sannan ya buga wa ƙungiyoyi da dama tamaula a Italiya.

    Bayan ya yi ritaya, ya koma horarwa inda ya jagoranci Parma da Sampdoria da Lecce da kuma Empoli.ranar Lahadi mai zuwa a gasar Serie A.

  6. Sesco bai damu da ba a fara wasa da shi a Man United ba, Premier League

    Ɗan wasan Manchester United, Benjamin Sesko ya ce bai damu ba da ba a fara wasa da shi, sai dai ya shiga canji, hakan na kara sa shi ya kara sa ƙwazo a wasannin da yake yi.

    Tuni wasu ke ganin ya kamata kociyan riƙon ƙwarya, Micheal Carrick yake fara wasa da ɗan ƙwallon Slovenia a United.

    Sesco ne ya ci wa United ƙwallon da ta ci Everton ranar Litinin, kuma karo na uku da yake ci wa ƙungiyar ƙwallo da zarar ya canji ɗan wasa daga wasa huɗu.

    Carrick ya ja ragamar wasa shida tun bayan maye gurbin Ruben Amorim a United da canjaras ɗaya daga ciki.

    Kawo yanzu Carrick bai fara wasa da Sesco ba, illa yana saka shi canji ne - United tana matsayi na huɗu a teburin Premier League da tazarar maki uku tsakani da Aston Villa a matsayi na uku.

  7. , Daga jaridu

    Manchester City za ta fuskanci kalubale wajen ci gaba da riƙe ɗan wasan tsakiya na Spain Rodri a wannan bazarar, inda Real Madrid da Barcelona ke son ɗan wasan mai shekaru 29. (Bild)

    Fatan Liverpool na siyan mai tsaron baya na Roma Zeki Celik ya ƙaru bayan da wakilinsa ya yi watsi da yuwuwar komawar ɗan wasan na Turkiyya mai shekaru 29 Juventus. (Mirror)

    Arsenal da Chelsea suna matsa wa Barcelona lamba a ƙoƙarinsu na neman ɗan wasan gaba na Atletico Madrid Julian Alvarez mai shekaru 26. (Teamtalk)

    Juventus na sa ran daukar mai tsaron ragar Tottenham mai shekaru 29, Guglielmo Vicario, na Italiya a wannan bazarar, amma za ta fuskanci gogayya daga Inter Milan. (Gazzetta dello Sport)

  8. Hakimi zai fuskanci shari'a saboda zargin fyaɗe, Paris St Germain

    Mai tsaron bayan Paris St-Germain, Achraf Hakimi ya ce zai fuskanci shari'a, bayan da wata mata ta zarge shi da yi mata fyaɗe.

    Matar ta zargi ƙyaftin ɗin Morocco da yi mata fyaɗe a gidansa da ke babban birnin Faransa a shekarar 2023, lokacin tana da shekaru 24. Sai dai ya musanta zargin.

    Ofishin mai gabatar da kara na Nanterre a yammacin birnin Paris, ya fara bincike a karon farko a watan Maris a 2023.

    “A wannan lokacin zargin fyaɗe kawai ya isa a kai mutum gaban kotu,” in ji Hakimi a shafinsa na X.

    “Wannan ba adalci ba ne ga wanda bai yi laifi ba, kamar yadda ba adalci ba ne ga wadanda abin ya faru da gaske. Ina jiran wannan shari’a cikin natsuwa, wadda za ta ba da damar fito da gaskiya a bainar jama’a.”

    Har yanzu ba a sanya ranar fara shari’ar ba.

    BBC Sport ta tuntuɓi ofishin mai gabatar da kara na Nanterre, domin jin karin bayani.

    Paris St-Germain za ta karɓi bakuncin Monaco a wasan zagaye na biyu na cike gurbin zagaye na biyu a Champions League ranar Laraba.

    An haifi ɗan wasan mai shekara 27 a Sifaniya, amma ya zaɓi buga wa Morocco tamaula, kuma ya yi wasa 194 a Paris St Germain da lashe Champions League da Ligue 1 a kakar da ta gabata.

    Kokarinsa ya sa aka karrama shi a bikin Best Fifa Football Awards da aka gudanar a Paris, inda aka zabe shi cikin tawagar duniya ta ƴan wasa ta Fifpro na shekara.

    Morocco za ta kara da Scotland da Haiti da kuma Brazil a gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a Amurka da Mexico da Canada a wannan shekarar.

  9. Za a fara wasannin zagaye na biyu a Champions League, Champions League

    Wasannin da za a buga ranar Talata 24 ga watan Fabrairu:

    • Bayer Leverkusen da Olympiacos
    • Inter Milan da Bodo/Glimt
    • Newcastle da Qarabag
    • Atletico Madrid da Club Bruge

    Sakamakon wasan farko da suka buga ranar Laraba:

    Ranar Laraba 18 ga watan Fabrairu

    • Bodo Glimt 3 – 1 Inter Milan
    • Club Brugge 3 – 3 Atletico Madrid
    • Olympiakos 0 – 2 Bayern Leverkusen
    • Qarabag 1 – 6 Newcastle United
  10. , Daga jaridu

    Newcastle za ta sayar da ɗan wasan gaba na Jamus Nick Woltemade ne kawai a wannan bazarar idan ɗan wasan mai shekaru 24 ya buƙaci barin ƙungiyar. (Football Insider)

    Arsenal tana gaban Manchester City da Newcastle wajen neman ɗan wasan baya na Sporting mai shekaru 21 Ivan Fresneda. (Fichajes)

    Zuwan Fresneda zai iya sa ɗan wasan baya na Ingila mai shekaru 28 Ben White ya bar Arsenal. (Teamtalk)

    Manchester United da Arsenal su ne waɗanda ake sa ran za su sayi ɗan wasan baya na Jamus mai shekaru 22 na Eintracht Frankfurt Nathaniel Brown a wannan bazarar. (Caughtoffside)

  11. Za a bayar da dakika biyar kafin jifa da bugun falan ɗaya a kofin duniya, Fifa

    Za a fara kirga dakika biyar kafin a jefa kwallo cikin fili (throw-in) da kuma bugun falan ɗaya (goal kick) a gasar Cin Kofin Duniya ta bana, yayin da masu tsara dokokin kwallon kafa ke shirin bullo da sabbin matakai domin rage ɓata lokaci..

    An samu daƙile ɓata lokaci daga mai tsaron raga da aka amince kada ƙwallo ya wuce dakika takwas a hannunsa - hukunci sai a busa kwana a gidansa - hakan ne ya kara karfafa masu tsara dokokin Fifa kara fito da wasu matakan da za su rage ɓata lokaci a yayin tamaula.

    Ana sa ran za a amince da sabbin dokokin da aka a taron shekara-shekara da za a yi a Wales ranar Asabar.

  12. Loftus-Cheek zai yi jinya mai tsawo, bayan karya mukamuki, AC Milan

    Ɗan wasan tawagar Ingila, Ruben Loftus-Cheek, ya karya mukamuki, bayan da ya yi karo da mai tsaron bayan Parma, Edoardo Corvi, a wasan Serie A da suka buga ranar Lahadi, in ji kafafen yada labarai na Italiya.

    An dauki Loftus-Cheek daga filin wasa a kan gadon daukar mara lafiya bayan raunin da ya ji, yayin da yake kokarin karbar kwallo a kusan minti na 10 a filin San Siro. AC Milan ta sha kashi 1-0 a wasan.

    Ana sa ran ɗan wasan zai ji jinya mai tsawo, bayan da AC Milan ba ta fayyace ranar da zai koma taka leda ba.

  13. Advocaat ba zai ja ragamar Curacao gasar kofin duniya ba, Gasar kofin duniya

    Dick Advocaat, wanda ya jagoranci Curacao zuwa samun tikitin shiga gasar Cin Kofin Duniya a karon farko, ba zai jagoranci tawagar ba, bayan da ya yi murabus, saboda dalili na kashin kansa, in ji kafafen yaɗa labarai na Netherlands a ranar Litinin.

    Rahotannin sun ce tsohon kocin Netherlands da Belgium da Koriya ta Kudu da PSV Eindhoven da Sunderland da Rangers ya yi murabus ne saboda rashin lafiyar diyarsa.

    Advocaat, wanda ya shafe shekara biyu a matsayin kocin Curacao, an maye gurbinsa da ɗan kasar Netherlands, Fred Rutten.

    Kocin mai shekara 78 ya jagoranci tsibirin na Caribbean mai yawan jama’a kimanin 150,000 zuwa gasar Duniya a matsayin “abin ban mamaki” a cikin aikin horarwa na kusan shekaru arba’in.

    Da ya je wasannin da za a buga a Amurka da Canada da kuma Mexico, da ya zama koci mafi tsufa a tarihin gasar Cin Kofin Duniya.

    Rutten, tsohon mai tsaron bayan, Netherlands, ya taɓa horar da PSV da Anderlecht da kuma Feyenoord.

    Curacao za ta fara wasan farko a gasar kofin duniya a bana a rukuni na biyar da Jamus a Houston ranar 14 ga watan Yuni.

  14. An ɗage wasannin gasar tamaula a Mexico, saboda mutuwar El Mencho, Mexico

    An ɗage wasa hudu a babbar gasar tamaula ta Mexico, bayan ɓarkewar tashin hankali a kusa da Guadalajara, daya daga cikin biranen da za su karɓi bakuncin gasar Cin Kofin Duniya ta 2026, sakamakon kashe shugaban kungiyar miyagun kwayoyi Nemesio Oseguera, “El Mencho” da jami'an tsaro suka yi.

    Oseguera, mai shekaru 60, shugaban kungiyar Jalisco New Generation Cartel (CJNG), ya mutu a hannun jami’an tsaro bayan rauni a wani arangama a bakin tekun Pacific a jihar Jalisco.

    Liga ta Mexico ta sanar a shafukan sada zumunta cewa an ɗage wasa biyu na manyan ƙungiyoyi da aka shirya ranar Lahadi — Queretaro da Juarez FC a fannin maza da na Chivas da America a wasan mata — har sai komai ya koma daidai.

    Haka kuma, an soke wasu wasa biyu na rukuni na biyu da aka shirya ranar Lahadi, in ji rahotannin kafafen watsa labarai na gida.

    Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Mexico tana shirin karawa da Iceland ranar Laraba a wani wasan sada zumunta a filin Corregidora da ke Queretaro.

  15. An dakatar da Prestianni wasa ɗaya na jeka gyara hali, Champions League

    An dakatar da ɗan ƙwallon Benfica, Gianluca Prestianni wasa ɗaya na jeka gyara hali, bayan zargin kalaman wari da Vinicius Jr na Real Madrid ya kai rahoto a yayin haduwar su a gasar Champions League a makon jiya a Portugal.

    Vinicius ya shaida wa alkalin wasa Francois Letexier cewa ɗan wasan tawagar Argentina ya yi masa kalaman wariya a wasan cike gurbin shiga zagaye na biyu a Champions League da Real Madrid ta ci 1-0 ranar Laraba.

    UEFA ta sanar da wannan dakatarwa ta wucin gadi a ranar Litinin, bayan naɗa jami’in da suka gudanar da bincike kan lamarin.

    Hukumar kwallon kafa ta Turai ta ce za a iya daukar karin matakan ladabtarwa da zarar ta kammala binciken.

    Real Madrid da Benfica za su kara haduwa a wasa na biyu a birnin Madrid ranar Laraba.

  16. Sterling ya buga wasan farko a Feyenoord na farko tun 2025, Feyenoord

    Raheem Sterling ya buga wa Feyenoord wasan farko, inda ya canji dan ƙwalo karon farko da ya taka leda a babbar gasa tun bayan watan Mayun 2025.

    Ɗan wasan mai shekaru 31, wanda ya koma ƙungiyar ta Netherlands a makon jiya bayan soke sauran kwantiransa a Chelsea, ya shiga karawar a lokacin da Feyenoord ke cin Telstar 2-1 — kuma haka suka tashi.

    Wasan karshe da ya buga a Arsenal da ya buga mata wasannin aro a Premier League a bara.

  17. ''Ɗan wasa zai tsaya a wajen fili minti ɗaya idan an duba lafiyarsa'', Fifa

    Ɗuk ɗan wasan da aka duba lafiyarsa a cikin fili zai fita waje na minti ɗaya daga baya ya koma wasan, karkashin shawarwari daga FIFA.

    Wannan na daga cikin matakan da ake son ɗauka, domin rage tsaikon wasa da ɓata lokaci, kuma ana sa ran za a amince da wannan dotar a taron shekara-shekara na International Football Association Board (IFAB) a ranar Asabar.

    A halin yanzu dokokin kwallon kafa ba su fayyace tsawon lokacin da ɗan wasa da aka kaiwa agajin gaggawa zai zauna a waje ba.

    Kowace gasa ta kasa tana da ikon kafa tata ka’idojin, inda Premier League ta fara amfani da dakatar da ɗan wasa na dakika 30 tun daga kakar 2023-24.

    FIFA ta gudanar da gwaje-gwaje wannan dokar a gasar Arab Cup da aka yi a watan Disamba, inda aka bukaci ɗan wasa ya zauna a waje na minti biyu kafin ya dawo fili.

  18. Arsenal ta ci Tottenham 8-2 gida da waje a bana a Premier, Premier League

    Arsenal ta je ta doke Tottenham 4-1 a Premier League da suka fafata ranar Lahadi.

    Eze ne ya ci wa Gunners ƙwallo biyu da kuma Gyokeres da shima ya zura biyu a raga, yayin da Kolo Muani ya farke wa Tottenham ɗaya daga ciki.

    Wasa na 199 da suka yi na hamayya a dukkan karawa, inda Gunners ta ci 86 da canjaras 52, Tottenham ta yi nasara 61.

    A wasan farko a bana da suka buga a Emirates, an doke Tottenham 4-1.

    Gunner ta ci gaba da zama a matakin farko a kan teburi da maki biyar tsakani da Manchester City, amma wasa 28 ta yi, ita kuwa City tana da 27.

  19. Barcelona ta karɓe teburin La Liga daga hannun Real Madrid, La Liga

    Barcelona ta koma matakin farko a kan teburin La Liga, bayan doke Levente 3-0 a wasan mako na 25 da suka buga ranar Lahadi.

    Ƙungiyar Camp Nou ta ci ƙwallayen ta hannun Marc Bernal da De Jong da kuma Fermín López.

    Da wannan sakamakon Barcelona tana ta ɗaya a kan teburi da maki 60, sai Real Madrid ta biyu da tazarar maki ɗaya tsakani.

    Real Madrid ta ci karo da komabaya, sakamakon da ta yi rashin nasara 2-1 a gidan Osasuna ranar Asabar.

    Ranar Laraba, Real Madrid za ta karɓi bakuncin Benfica a wasa na biyu a neman cike gurbin zuwa zagaye na biyu a Champions League.

    Wasan farko da suka buga a Portugal, Real ce ta yi nasara a wasan da Vinicius Junior ya yi zargin an yi masa kalaman wariya - Uefa tana bincike kan lamarin.

  20. Kano Pillars ta doke El-Kanemi 3-0

    Kano Pillars ta doke El-Kanemi Warriors da ci 3-0 a wasan mako na 27 a Premier League ta Najeriya da suka kara ranar Lahadi.

    Ƙungiyar da ake kira sai masu gida ta fara cin ƙwallo ta hannun Rabiu Ali a minti na 11 da take leda daga baya Lius Dadong ya kara na biyu daf da zuwa hutu.

    Bayan da suka sha ruwa suka koma zagaye na biyu ne, Chiedozie Okorie ya kara ci wa Pillars na uku a wasan da suka yi a filin da ake kira Sani Abacha da ke Kofar Mata a Kano, Najeriya.

    Da wannan sakamakon Pillars ta yi saman teburi zuwa mataki na 16 da maki 32, ita kuwa El-Kanemi mai maki 38 tana nan a mataki na tara.

    Sauran wasannin da aka buga ranar Lahadi:

    • Wikki Tourists 2-1 Remo Stars
    • Katsina United 0-0 Enugu Rangers
    • Abia Warriors 1-0 Kwara United
    • Ikorodu City 1-1 Bayelsa United
    • Kano Pillars 3-0 El Kanemi Warriors
    • Kun Khalifat 2-0 Niger Tornadoes
    • Nasarawa United 1-0 Bendel Insurance
    • Plateau United 4-1 Shooting Stars
    • Rivers United 1-1 Enyimba

    Wasan ranar Asabar:

    • Warri Wolves 0-0 Barau FC