KAI TSAYE, Labarin wasanni daga 22 zuwa 27 ga watan Fabrairu 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Lahadi 22 zuwa 27 ga Fabrairu 2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Arsenal ta ci Tottenham 8-2 gida da waje a bana a Premier, Premier League

    Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal ta je ta doke Tottenham 4-1 a Premier League da suka fafata ranar Lahadi.

    Eze ne ya ci wa Gunners ƙwallo biyu da kuma Gyokeres da shima ya zura biyu a raga, yayin da Kolo Muani ya farke wa Tottenham ɗaya daga ciki.

    Wasa na 199 da suka yi na hamayya a dukkan karawa, inda Gunners ta ci 86 da canjaras 52, Tottenham ta yi nasara 61.

    A wasan farko a bana da suka buga a Emirates, an doke Tottenham 4-1.

    Gunner ta ci gaba da zama a matakin farko a kan teburi da maki biyar tsakani da Manchester City, amma wasa 28 ta yi, ita kuwa City tana da 27.

  2. Barcelona ta karɓe teburin La Liga daga hannun Real Madrid, La Liga

    Barcelona

    Asalin hoton, Getty Images

    Barcelona ta koma matakin farko a kan teburin La Liga, bayan doke Levente 3-0 a wasan mako na 25 da suka buga ranar Lahadi.

    Ƙungiyar Camp Nou ta ci ƙwallayen ta hannun Marc Bernal da De Jong da kuma Fermín López.

    Da wannan sakamakon Barcelona tana ta ɗaya a kan teburi da maki 60, sai Real Madrid ta biyu da tazarar maki ɗaya tsakani.

    Real Madrid ta ci karo da komabaya, sakamakon da ta yi rashin nasara 2-1 a gidan Osasuna ranar Asabar.

    Ranar Laraba, Real Madrid za ta karɓi bakuncin Benfica a wasa na biyu a neman cike gurbin zuwa zagaye na biyu a Champions League.

    Wasan farko da suka buga a Portugal, Real ce ta yi nasara a wasan da Vinicius Junior ya yi zargin an yi masa kalaman wariya - Uefa tana bincike kan lamarin.

  3. Kano Pillars ta doke El-Kanemi 3-0

    Pillars

    Asalin hoton, npfl

    Kano Pillars ta doke El-Kanemi Warriors da ci 3-0 a wasan mako na 27 a Premier League ta Najeriya da suka kara ranar Lahadi.

    Ƙungiyar da ake kira sai masu gida ta fara cin ƙwallo ta hannun Rabiu Ali a minti na 11 da take leda daga baya Lius Dadong ya kara na biyu daf da zuwa hutu.

    Bayan da suka sha ruwa suka koma zagaye na biyu ne, Chiedozie Okorie ya kara ci wa Pillars na uku a wasan da suka yi a filin da ake kira Sani Abacha da ke Kofar Mata a Kano, Najeriya.

    Da wannan sakamakon Pillars ta yi saman teburi zuwa mataki na 16 da maki 32, ita kuwa El-Kanemi mai maki 38 tana nan a mataki na tara.

    Sauran wasannin da aka buga ranar Lahadi:

    • Wikki Tourists 2-1 Remo Stars
    • Katsina United 0-0 Enugu Rangers
    • Abia Warriors 1-0 Kwara United
    • Ikorodu City 1-1 Bayelsa United
    • Kano Pillars 3-0 El Kanemi Warriors
    • Kun Khalifat 2-0 Niger Tornadoes
    • Nasarawa United 1-0 Bendel Insurance
    • Plateau United 4-1 Shooting Stars
    • Rivers United 1-1 Enyimba

    Wasan ranar Asabar:

    • Warri Wolves 0-0 Barau FC
  4. Ina jin daɗin taka leda a Al-Nassr ba inda zan koma - Ronaldo, Gasar tamaula ta Saudiyya

    Ronaldo

    Asalin hoton, Reuters

    Cristiano Ronaldo ya ce yana jin daɗin taka leda a Al-Nassr duk da jita-jitar da ake yi kan makomarsa a ƙungiyar ta Saudiyya.

    Ɗan wasan mai shekaru 41 ɗan kasar Portugal an ruwaito cewa bai gamsu da yadda Asusun Zuba Jari na Saudiyya (PIF) ke tafiyar da ƙungiyar ba, kuma bai yi wasa uku a baya-bayan nan ba.

    Sai dai ya koma taka leda a makon jiya, kuma ya zura kwallo biyu a 4-0 da suka yi a kan Al-Hazem ranar Asabar — hakan ya sa suka koma na ɗaya a kan teburin babbar gasar tamaula ta Saudiyya.

    “Ina cikin farin ciki sosai,” in ji ɗan wasan Portugal a wata hira da kafar yada labarai ta Saudiyya Thmanyah. “Kamar yadda na sha fada sau da dama, ni na Saudiyya ne.

    “Kasa ce da ta karɓe ni hannu bibiyu, tare da iyalina da abokaina. Ina farin ciki a nan, kuma ina son ci gaba da zama a kasar nan.

    “Abu mafi muhimmanci shi ne mu ci gaba da kokari domin lashe kofin lig. Muna kan gaba yanzu, muna samun nasarori, muna kuma matsa lamba — sai mu yi hakuri kan ganin yadda za ta kaya a karshen kakar.”

    Ronaldo ya koma Gabas ta Tsakiya da wasa a watan Disambar 2022 bayan kwantiraginsa da Manchester United ya kare ta hanyar yarjejeniya, inda ya zama mafi tsadar da karɓar albashi mai tsoka a tarihin kwallon kafa da albashin fam miliyan 177.

    Sai dai tun zuwansa, ƙungiyar mai kofin Saudiyya 10, ta samu nasarar lashe Arab Club Champions Cup na 2023 kawai.

    Nasarar ranar Asabar ta sa sun saman Al-Hilal da maki ɗaya tsakani a teburi, sannan sun kai matakin kwata-final na gasar AFC Asian Cup.

  5. Inter Miami ta fara gasar bana da kafar hagu a MLS, Gasar ƙwallon kafa ta Amurka, MLS

    Lionel Messi

    Asalin hoton, Reuters

    Lionel Messi da Inter Miami sun fara kare kambunsu na MLS ta kafar hagu, bayan sha kashi 3-0 a hannun Los Angeles FC.

    Tsohon ɗan wasan Tottenham, Son Heung-min, ya bai wa David Martinez kwallo da aka ci ta farko a minti na 38, kafin Denis Bouanga ya kara ta biyu a minti na 78.

    Duk da cewa Miami ta fi rike kwallon, amma ta kasa farke ƙwallayen da aka ɗura mata - daf da za a tashi daga karawar Nathan Ordaz ya zura kwallo ta uku.

    Los Angeles ta yi kokari wajen rage hatsarin Messi a wasan, duk da cewa tauraron Argentina ya buga wasan yana fama da dan karamin rauni.

    Haka kuma Los Angeles ta ci gaba da rike tarihinta na rashin shan kashi a wasan bude kakar tamaula ta Amurka, inda ta yi fafatawa tara ba tare da shan kashi ba.

  6. Bayern Munich

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Bayern Munich ta sanar cewa Alphonso Davies ya ji ciwo a wasan da suka doke Eintracht Frankfurt da ci 3-2 ranar Asabar a filin wasa na Allianz Arena.

    Davies, wanda kwanan nan ya dawo taka leda, bayan jinya mai tsawo saboda raunin gwiwa, an sauya shi da Hiroki Ito a minti na 50 bayan ɗan wasan Canada ya fadi a kasa tare da bukatar kulawar likitoci.

    Har yanzu ba a tabbatar da tsawon lokacin da zai yi jinya ba, amma koci Vincent Kompany ya ce yana fatan zai dawo wasa cikin mako biyu zuwa hudu.

    Bayern, wadda ke kan gaba a teburin Bundesliga da maki 60 daga wasa 23, za ta kara da Borussia Dortmund mai matsayi na biyu a ranar Asabar mai zuwa.

  7. , Daga Jaridu

    Nico

    Asalin hoton, Getty Images

    Tottenham da Newcastle suna sha'awar dawo da dan wasan gaban Al-Hilal mai shekaru 26 Darwin Nunez tsohon dan wasan Liverpool zuwa gasar Premier. (Teamtalk)

    Tottenham da Aston Villa suna cikin kungiyoyin da ke sa ido kan dan wasan tsakiya na Lyon mai shekaru 25 Pavel Sulc. (Mail)

    Dan wasan baya na Ingila Joe Gomez yana shirin barin Liverpool a wannan bazararinda AC Milan da Bayern Munich ke neman wasan mai shekaru 28. (Cought Offside)

    Roma da Juventus sun shiga takarar sayen dan wasan baya na Argentina mai shekaru 28 na Bournemouth Marcos Senesi a karshen kakar wasa. (Corriere Dello Sport)

  8. Yanzu ake buga Premier League - Guardiola, Premier League

    Guardiola

    Asalin hoton, Getty Images

    Pep Guardiola ya ce yanzu ne aka fara buga Premier League ya kuma ce yana sa ran za a ga karin abubuwan da za suke ɗaukar hankali a kokarin lashe kofin bana, ya jaddada cewa Manchester City ba za ta mika wuya ba wajen ci gaba da kalubalantar Arsenal ba.

    Ƙungiyar da Guardiola ke jan ragama ta ci gaba da matsawa Arsenal lamba wajen maye gurbinta a kan teburin kakar bana.

    Ranar Asabar City ta doke Newcastle 2-1 a Etihad a wasan mako na 27, kenan saura maki biyu tsakani da Arsenal mai jan ragama, wadda za ta fafata da Tottenham a wasan mako na 28 ranar Lahadi.

  9. Sheffield Wednesday ta faɗi daga Championship, Champions League

    Wed

    Asalin hoton, Shutterstock

    Sheffield Wednesday, wadda aka cire mata maki 18 saboda karya dokar kashe kuɗi daidai samu, ta zama ta farko a tarihin English Football League da ta fadi daga gasar kasar tun a watan Fabrairu, bayan shan kashi 2-1 a hannun Sheffield United ranar Lahadi wanda ya tabbatar da saukarsu daga Championship.

    Tun watan Satumba ba ta ci wasa ba, kuma tana cikin jerin fafatawa 11 a jere ba tare da nasara ba a dukkanin gasa. Wednesday wadda tae ta karsen teburi ta 22, ana bin ta maki bakwai, kuma tana da tazarar maki 41 tsakani da West Bromwich Albion mai matsayi na 21,

    Da yake wasa 13 suka rage a kammala kakar bana, Wednesday ba za ta iya ci gaba da taka leda a baɗi ba, kenan za ta koma buga League One a baɗi.

    Ƙungiyar mai shekaru 158 a tarihi, yanzu ana neman mai sayenta.

  10. , Daga Jaridu

    De Bruyne

    Asalin hoton, Getty Images

    Real Madrid ce ke kan gaba wajen neman dan wasan baya na Jamus na Borussia Dortmund Nico Schlotterbeck, amma Barcelona ma tana sha'awar dan wasan mai shekaru 26. (AS Sport)

    Newcastle na sha'awar siyan dan wasan baya na Sifaniya Hugo Bueno mai shekaru 23 daga Wolves a wannan bazarar. (Football Insider)

    Liverpool na shirin mika tayin £83m ga dan wasan gefe na Ingila Anthony Gordon mai shekaru 24 na Newcastle idan dan wasan gaba na Masar Mohamed Salah, mai shekaru 33, ya bar kungiyar a wannan bazarar. (Fichajes)

    Everton na shirin gabatar da tayin £30m ga dan wasan gaba na Chelsea mai shekaru 23 Liam Delap a wannan bazarar. (Teamtalk)

  11. , Yadda teburin Premier League kafin a kammala wasannin mako na 27

    EPL Table

    Asalin hoton, BBC Sport

  12. , Wasannin da za a buga ranar Lahadi

    EPL

    Asalin hoton, BBC Sport

  13. , Sakamakon wasannin mako na 27a Premier League

    EPL Week 27

    Asalin hoton, BBC Sport

  14. An buga wasa biyar a Premier League ranar Asabar, Premier League

    Trophy

    Asalin hoton, Getty Images

    Ranar Asabar aka fara wasannin mako na 27 a gasar Premier League da aka yi karawa shida.

  15. Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni

    Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.

    Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.