Labarin wasanni daga 01 zuwa 06 ga watan Fabrairu 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Lahadi 01 zuwa 06 ga Fabrairu 2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Hukumar ƙwallon Saudiyya ta gargaɗi Ronaldo

    Cristiano Ronaldo

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Cristiano Ronaldo

    Hukumar kula da gasar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa ta Saudiyya, wato Saudi Pro League ta gargaɗi Cristiano Ronaldo kan cewa “babu wanda ya fi ƙarfin ƙungiyarsa – duk muhimmancinsa, balle ya ce shi zai yanke wa ƙungiyar hukunci”.

    Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tababa kan makomar fitaccen ɗan wasan a ƙungiyar Al-Nasr.

    Ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Portugal bai buga wasan da Al-Nassr ta yi ba a gasar ta Saudi Pro League da ƙungiyar Al-Riyad a ranar Litinin.

    Jaridar A Bola ta Portugal ta ruwaito cewa Ronaldo ya ƙi buga wasan ne sanadiyyar rashin gamsuwa da yadda hukumar zuba jari ta Saudiyya ke tafiyar da lamurran ƙungiyar.

    An shaida wa BBC cewa komawar ɗan wasa Karim Benzema zuwa ƙungiyar Al-Hilal daga Al-Ittihad a farkon makon nan na daga cikin abubuwan da suka tunzura Ronaldo a ƙungiyar Al-Nassr.

    Benzema ya zura ƙwallo uku a wasa na farko da ya buga wa Al-Hilal ranar Alhamis lokacin da suka kara da ƙungiyar Al-Okhdood.

    Ƙungiyar Al-Nassr da Al-Hilal duk suna ƙarƙashin kulawar hukuma ɗaya ce, kuma su ne ƙungiyoyin da suka fi samun nasara a gasar, inda suka lashe kofuna 19.

  2. An dakatar da Rodrygo wasa biyu a Champions League, Champions League

    Rodrygo

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai (UEFA) ta sanar cewa ta dakatar da ɗan ƙwallon Real Madrid, Rodrygo wasa biyu, saboda zagin jami’in wasa a karawar da Benfica ta doke su 4-2 a Champions League a makon da ya gabata.

    Ɗan wasan tawagar Brazil ya samu katin gargaɗi na biyu daf da tashi da ta kai an yi masa jan kati, sakamakon da yake zagin ƴan wasan Benfica da zargin suna ɓata lokaci.

    Bayan shi an kuma bai wa Raul Asencio jan kati a karawar.

    Rashin nasarar da Real Madrid ta yi a hannun Benfica ya sa ta kasa kai wa zagayen ƴan 16 kai tsaye, sai ta yi wasannin cike gurbi.

    Real Madrid za ta fuskanci Benfica gida da waje a zagayen cike gurbi, domin neman matakin shiga ƴan 16 da za su ci gaba da gasar Champions League, amma Rodrygo ba zai karawar ba.

  3. Guardiola na son a bar Guehi ya buga wasan karshe a Carabao Cup, Carabao Cup

    Guehi

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Manchester City, Pep Guardiola yana son Hukumar Kwallon Ƙafa ta Ingila (EFL) ta ba wa ɗan baya Marc Guehi damar buga wasan ƙarshe a gasar Carabao Cup da Arsenal a watan gobe.

    City ta sayi Guehi daga Crystal Palace a lokacin da aka yi cinikayyar ƴan ƙwallo a watan Janairu da aka kammala ranar Litinin.

    Ta kuma sayi ɗan wasan ne bayan da ta je ta ci Newcastle United 2-0 a wasan farko a League Cup a St James Park.

    Bisa dokokin gasar, hakan ya sa Guehi bai cancanci buga wasan karshe da Arsenal ba a watan gobe a Wembley.

  4. Za a fara gasar Olympics ranar Juma'a a birnin Milan, Olympics

    Hukumar Gasar Olympics ta Duniya (IOC) na fatan cewa bikin buɗe Gasar Olympics ta Hunturu ta Milano Cortina da za a yi a ranar Juma’a ba za ta ci ko da tsaiko ko ba ko ihu ko ƙyamar Amurkawa ba.

    Kuma zai zama wani biki na nuna girmamawa ga ƴan wasa daga sassa daban-daban na duniya.

    Ana sa ran mataimakin shugaban kasar Amurka, JD Vance, da sakataren harkokin waje, Marco Rubio, za su halarci bikin da za a gudanar a filin wasa na San Siro a Italiya.

  5. Chamberlain na daf da komawa Celtic ta Scotland, Celtic

    Chmaberlain

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon ɗan wasan Arsenal da Liverpool, Alex Oxlade-Chamberlain, na dab da komawa buga babbar gasar tamaula ta Scotland a Celtic.

    Mai shekaru 32 ya kasance bai da wata ƙungiya tun bayan da ya bar Besiktas ta Turkiyya ta Besiktas a watan Agusta - tun daga lokacin ya koma atisaye a Arsenal, wadda ya yiwa wasa kusan 200 a kaka shidan da ya yi a Emirtaes.

    Kocin Celtic, Martin O’Neil ya tabbatar da sha’awarsa ɗaukar Oxlade-Chamberlain a wannan makon, kuma ya ce yana ganin zai ba su gagarumar gudunmuwa a ƙungiyar.

  6. Premier ce kan gaba a cefanen ƴan ƙwallo daga waje a watan Janairu, Kasuwar saye da sayar da ƴan ƙwallo

    Conor

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Ingila ne suka jagoranci kashe kuɗi a duniya wajen sayen ƴan wasa daga ƙasashen waje a kasuwar sayen ƴan ƙwallo a hunturu a shekarar 2026, a cewar wani sabon rahoto daga FIFA.

    Ƙungiyoyin sun kashe fam miliyan 268 wajen ɗaukar ƴan wasa daga ƙasashen waje, daga cikin jimillar kuɗin da aka yi cinikayya ya kai fam biliyan 1.44.

    Wannan shi ne karo na biyu mafi girman adadin kuɗin da aka taɓa kashewa a kasuwar hunturu, bayan a watan Janairun bara da ya kai fam biliyan 1.75.

    Sayen Conor Gallagher da Tottenham ta yi daga Atletico Madrid kan fam miliyan 34.7 shi ne mafi tsadar ciniki daga wata kasar zuwa Premier League a cikin watan Janairu.

    Haka kuma, sayen Taty Castellanos da West Ham ta yi daga Lazio da kuma wanda Bournemouth ta ɗauki Rayan daga Vasco da Gama, suna daga cikin manyan cefanen da aka yi.

    A cewar rahoton, ƙungiyoyin Italiya da Brazil da Jamus da na Faransa ne suke bin bayan Premier League wajen yawan kashe kuɗi.

  7. , Daga Jaridu

    Ronaldo

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan wasan gaban Portugal Cristiano Ronaldo, wanda zai cika shekaru 41 a ranar Alhamis, zai kauracewa wasa na biyu da Al-Nassr, duk da cewa ya saka hotonsa yana atisaye, kuma yana iya neman barin kungiyar Saudi Pro League a watan Yuni. (ESPN)

    Idan Ronaldo ya bar Al-Nassr, watakila komawarsa zai koma kungiyarsa ta farko Sporting Lisbon. (Fichajes)

    Elliot Anderson na Nottingham Forest ne kan gaba a jerin 'yan wasan tsakiya da Manchester United ke son dauka. Ragowar wadanda kungiyar ke nema sun hada da abokin wasansa na Three Lions Adam Wharton, mai shekaru 21, na Crystal Palace, da kuma ɗan wasan Kamaru da Brighton Carlos Baleba, mai shekaru 22, (The Athletic)

    Atletico Madrid na shirye ta sayi ɗan wasan baya na Tottenham Cristian Romero, mai shekaru 27, bayan wani sabon rubutu da ɗan wasan na Argentina ya yi a shafukan sada zumunta yana sukar ƙungiyarsa. (Sun)

  8. , Gasar Olympics

    A Gasar Olympics ta hunturu, ƴan Birtaniya Bruce Mouat da Jen Dodds sun samu nasara ta biyu a jere a wasan curling na Mixed Doubles. Ƴan Team GB sun yi gagarumin kokari inda suka samu maki huɗu a ƙarshen kusa da na ƙarshe, wanda ya ba su nasarar 10–5 a kan Estonia a Cortina.

  9. Wasu hukuncin raflin Premier ya shafi rashin ƙwazonmu - Guardiola, Manchester City

    Pep Guardiola

    Asalin hoton, Getty Images

    Pep Guardiola ya yi watsi da ra’ayoyin da ke cewa akwai wata makarkashiya daga alkalan Premier League da ake yi wa Manchester City, amma ya jaddada cewa wasu hukunci na baya-bayan nan sun shafi koma bayan ƙungiyar.

    Kocin ya misalta wasu hukunce-hukuncen da yake ganin sun yi wa ƙungiyarsa illa, tun da aka shiga sabuwar shekarar nan.

    Ɗan wasan Rodri ma ya bayyana takaicinsa, bayan da suka ci Tottenham 2-0 daga baya aka zare kwallayen, sannan suka tashi 2-2 a gasar Premier League.

    Hakan ya sa wasa daya City ta ci daga shida a Premier League tun da aka shiga sabuwar shekara - kuma Arsenal, wadda take kan ragama teburin babbar gasar tamaual ta Ingila ta ba ta tazarar maki shida tsakani.

  10. , Daga jaridu

    Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban jami'in gudanarwa na Newcastle United David Hopkinson ya ce "ba shi da masaniya" ko wakilin Sandro Tonali ya yi wa Arsenal tayin dan wasan mai shekara 25, bayan jita-jitar da ake ta yadawa dangane da yiwuwar komawar dan wasan tsakiyar na Italiya kungiyar a ranar ƙarshe ta kasuwar musayar yan wasan kwallon kafa. (Talksport)

    Chelsea, da Manchester City da Liverpool suna sha'awar sayen mai tsaron raga na Sunderland na Netherlands Robin Roefs, inda kungiyar ke sa ran tayin sama da fam miliyan 50 ga dan wasan mai shekaru 23. ((Football insider)

    A shirye dan wasan baya na Faransa Dayot Upamecano, mai shekaru 27 yake, ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya a Bayern Munich wadda za ta ba shi damar ci gaba da zama a zakarun na Bundesliga har zuwa watan Yunin 2030. (Fabrizio Romano)

    Wolves sun amince da tayin Palmeiras na fam miliyan 21.6 don siyan ɗan wasan gefe na Colombia Jhon Arias, kuma ɗan wasan mai shekaru 28 ya riga ya tattauna yarjejeniyar sirri da ƙungiyar ta Brazil. (UOL)

  11. Betis za ta kara da Bilbao a Copa del Rey ranar Alhamis, Copa del Rey

    Lamine Yamal

    Asalin hoton, Getty Images

    Za a kammala zagayen kwata fainals a Copa Del Rey na Sifaniya tsakanin Real Betis da Atletico Madrid.

    Har yanzu Barcelona na fatan kare kofin da ta lashe a bara, bayan da ta dole Albacete 2-1 ranar Talata,

    Albacete mai buga karamar gasar tamaula ta biyu a Sifaniya ce ta fitar da Real Madrid a bana da yin nasarar 3-2 a zagayen ƴan 16 karkashin sabon koci Arbeloa.

    Haka kuma a can Italiya a daren nan za a kara a daf da na kusa da na karshe tsakanin Atalanta da Juventus a Italian Cup da kuma zagayen ƴan 16 a Coupe de France tsakanin Strasbourg da Monaco.

  12. City da Arsenal za su buga wasan karshe a Carabao Cup, Carabao Cup

    Carabao Cup

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester City za ta buga wasan karshe a Carabao Cup da Arsenal a Wembly ranar 22 ga watan Maris.

    City ta kawo wanna matakin bayan cin Newcastle United, mai rike da kofin 3-1 ranar Laraba a Etihad, kenan 5-0 gida da waje.

    Tun a ranar Talata Gunners ta kai karawar karshe, sakamakon nasara 1-0 a kan Chelsea a Emirates – da cin kwallo 4-2 gida da waje.

    Guardiola na fatan lashe kofi na 20 a kaka 10 a Etihad karo na biyar da ƙungiyar ta kai final karkashin kociyan ɗan kasar Sifaniya da ɗaukar Carabao Cup huɗu daga takwas da take da shi jimilla.

    Arsenal na fatan lahe League cup na uku a tarihi, wadda rabonta da shi tun 1993 shekara 33 tsakani.

    Liverpool ce kan gaba a yawa lashe Carabao Cup mai 10 jimilla

  13. Newell na kokarin ɗaukar Messi ƙungiyar da ya fara taka leda, Newell Old Boys

    Messi

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Argentina, Newell Old Boys na aiki tukuru, domin sake ɗaukar Lionel Messi, inda ya fara taka leda tun yana ɗan dagaji.

    Wani jami’in ya tabbatar da cewa suna ƙoƙarin shawo kan Messi ya koma ƙungiyar da ya fara tun ƙuruciyarsa, domin buga rabin kakar farko ta 2027.

    To sai dai Messi, wanda ya lashe Ballon d'Or takwas, ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da Inter Miami mai buga babbar gasar tamaula ta Amurka a watan Oktoba, wadda za ta ƙare a ƙarshen 2028.

    Messi, mai shekaru 38, ya buga wa Newell tamaula daga 1995 zuwa 2000 daga nan ya koma makarantar koyon tamaula ta Barcelona - da aka sa mata sunan La Messia, wadda ke renon matasa ƴan baiwa.

    Inter Miami za ta fara kakar MLS ta 2026 a ranar 21 ga Fabrairu da fuskantar da Los Angeles FC.

  14. Australia da Koriya ta Kudu da Kuwait na son haɗakar baƙuncin Asian Cup, Asian Cup

    Asian Cup

    Asalin hoton, Getty Images

    Australia da Koriya ta Kudu da Kuwait sun sanar a hukumance suna sha’awar haɗakar karɓar bakuncin Gasar Cin Kofin Asiya ta 2035,

    Ana sa ran fitar da kasar da za ta karɓi bakuncin manyan gasar tamaula ta nahiyar Asia da ake gudanarwa duk bayan shekara huɗu a taron da za a gudanar nan gaba.

    Hukumar ƙwallon kafar Asia ta ce Japan ma ta nuna sha’awar karɓar bakuncin gasar 2035 ita kaɗai.

    Tuni kasashen da ya haɗa da Indiya da Indonesia da kuma haɗaka tsakanin Kyrgyzstan da Uzbekistan da kuma Tajikistan—su ma suka miƙa bukatunsu shirya wasannin 2031..

    Ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa, wadda ta gudanar da wasannin 2019 na zawarcin na 2031 amma kuma ta janye daga ƴan takara a watan Nuwambar bara.

    Saudi Arabiya ce za ta karɓi bakuncin Gasar Cin Kofin Asiya ta 2027.

  15. Forest za ta auna koshin lafiyar Sels da Odoi, Nottingham Forest

    Sean Dyche

    Asalin hoton, Getty Images

    Nottingham Forest za ta ci gaba da auna koshin lafiyar Matz Sels da Callum Hudson-Odoi gabanin muhimmin wasan Premier League da za ta fafata da Leeds United a ranar Juma’a.

    Sels ya fita daga wasan da suka yi canjaras da Crystal Palace a ranar Lahadi sakamakon raunin ƙugu, yayin da Hudson-Odoi ya samu matsalar kafaɗa a dai wasan.

    Kocin ƙungiyar, Sean Dyche, ya ce: “Matz har yanzu yana jin zafin ciwo. Muna jira daga likitoci kafin mu yanke hukunci''

    Sabbin ƴan wasa, Stefan Ortega da Luca Netz watakila na iya shiga cikin jerin ƴan ƙwallon da za su buga wasan a karshen mako.

  16. Abokan hamayyarmu sun fi mu kashe kuɗin cefane - Guardiola, Manchester City

    Pep Guardiola

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya yi barkwanci yana mai cewa yana ɗan jin haushin ƙungiyarsa, saboda abokan hamayyarsu sun fi su kashe makudan kuɗi wajen cefane.

    City ce ta fi kashe kuɗi a kasuwar saye da sayar da ƴan kwallo da ta ci ta watse a watan Janairu, inda ta sayi Antoine Semenyo daga Bournemouth da Marc Guehi daga Crystal Palace kan kusan fam miliyan 84 gabaki ɗayansu.

    Sai dai Guardiola ya ce abokan hamayyarsa a gasar Premier League sun fi zuba jari mafi yawa…

    Idan har za a yi kididdigar cefane, City ta kashe sama da fam miliyan 396 a kaka biyar baya.

    Manchester United ce kan gaba da ta kashe fam miliyan 675 sai Arsenal mai fam miliyan 663 da Chelsea mai fam miliyan 651

    Tottenham kuwa ta kashe fam miliyan 574 da Newcastle United mai fam miliyan 424 da kuma Liverpool da ta kashe fam miliyan 420 in ji wani bincike

  17. , Daga Jaridu

    Mateta

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool na hamayya da Manchester United da Real Madrid kan ɗanwasan tsakiya na Crystal Palace da Ingila Adam Wharton, mai shekara 21. (Mirror)

    Manchester United za ta shiga zawarcin ɗanwasan gaba Jean-Philippe Mateta, mai shekara 28 a bazara bayan ɗanwasan na Faransa da Crystal Palace ya gaza komawa AC Milan. (Mirror)

    AC Milan da Chelsea da Newcastle na rubibin ɗanwasan gaba na Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 26 wanda suke son ɗaukowa a bazara daga Juventus. (Football Italia)

    Manchester United na son ƙarfafa tsakiyarta kuma tana son ɗanwasan Newcastle da Italiya Sandro Tonali, mai shekara 25, is of interest. (Metro)

  18. Romero na takaici da ƴan wasan Tottenham da yawa ke jinya, Tottenham

    Romero

    Asalin hoton, Getty Images

    Kyaftin ɗin Tottenham, Cristian Romero ya ce abin takaici ne da fitattun ƴan wasansu 11 ne ke tsaye a karawar da suka tashi 2-2 da Manchester City a Premier League ranar Lahadi.

    Shi kansa Romero sai canja shi aka yi a karawar da Pape Matar Sarr - daman Mohammed Kudus na jinya sai cikin Afirilu zai koma wasa, tuni Lucas Bergvall da Rodrigo Bentancur suka daɗe ba sa buga wasannin.

    Shima Richarlison da Pedro Porro har yanzu ba su murmure ba, yayin da James Maddison ke jinya tun daga watan Agusta.

    A watan Janairu Tottenham ta ɗauki Conor Gallagher daga Atletico Madrid da wani matashi mai shekara 19 ɗan Brazil, Souza daga Santos, amma ta sayar da Brennan Johnson ga Crystal Palace.

    Tottenham wadda take ta 14 a kasan teburin Premier League da maki 29 a wasa 24 za ta ziyarci Manchester United ranar Asabar a Old Trafford a babbar gasar tamaula ta Ingila.

  19. An sanar da filayen da za a buga wasannin Olympics a 2028, Olympics 2028

    Olympics

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu shirya wasannin Olympic da za a yi a 2028 a birnin Los Angeles sun sanar da filaye shida da za a gudanar da gasar - za kuma su faɗaɗa ta har Kudancin birnin Californiya.

    Za a buga wasannin cikin rukuni a birnin New York da Columbus da Nashville da St. Louis da San Jose da kuma San Diego.

    Wasannin karshe na maza da na mata da raba kyautukan lambobin yabo kuwa za a yi ne a Rose Bowl a Pasadena.

  20. Arsenal na sa ran lashe Carabao Cup domin dawo da martabarta, Carabao Cup

    Arteta

    Asalin hoton, Getty Images

    Jurrien Timber na ganin cewa lashe kofin Carabao Cup na iya zama wata hanya ta buɗe ƙofofin samun manyan nasarori ga Arsenal a wannan kakar ta bana.

    Ƙungiyar da Mikel Arteta ke jagoranta tana dab da kawo ƙarshen shekara shida ba tare da kofi ba, bayan da ta doke Chelsea a filin Emirates 1-0, kenan ta kai wasan karshe da cin 4-2 gida da waje.

    Arsenal ta kare a mataki na biyu sau uku a teburin Premier League, sai dai a bana tana kan teburi da tazarar maki shida tsakani da Manchester City ta biyu - kuma ita ce ta ja ragamar teburin Champions League da lashe dukkan karawa takwas gida da waje.

    Haka kuma, Arsenal za ta karɓi baƙuncin Wigan Athletic mai buga League One a zagaye na huɗu na FA Cup.