Da alama Ronaldo ya shiga damuwa a Saudiyya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Adwaidh Rajan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport journalist
- Lokacin karatu: Minti 3
An fara tababa kan makomar Cristiano Ronaldo a ƙungiyarsa ta Al-Nassr bayan rashin ganinsa a wasan da ƙungiyar ta buga ranar Litinin da ƙungiyar Al-Riyadh a babbar gasar ƙasar ta Saudi Pro League.
Jaridar Bola ta ƙasar Portugal ta ce Ronaldo, mai shekara 40 a duniya ya ƙi buga wasan ne bayan nuna ɓacin ransa kan yadda ake tafiyar da lamurran ƙungiyar.
Al-Nassr da Al-Hilal su ne ƙungiyoyi biyu mafiya nasara a Saudiyya, wadanda kuma Asusun Zuba Jari na Gwamnatin Saudiyya (PIF) ke gudanarwa, wanda kuma ke da hannu a tafiyar da ƙungiyae Newscastle da ke Ingila.
Ronaldo ya tafi Al-Nassr ne a shekarar 2022 bayan barin Manchester United a tsakiyar kakar wasa, inda ya zama ɗan wasa da ya fi karɓar albashi a tarihin ƙwallon ƙafa, inda ake biyan shi kudi fam miliyan 177 a shekara, to sai dai har yanzu kofi ɗaya kawai ya lashe na Zakarun Yankin Larabawa.
Ɗan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or har sau biyar ya sake sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyu da Al-Nassr a watan Yunin 2025.
Gabanin sanya hannu kan sabon kwantaragin an yi ta rade-radin cewa dan wasan zai tafi a Al-Hilal, abokiyar adawar Al-Nassr.
An shaida wa BBC cewa ƙoƙarin da Al-Hilal ta riƙa yi na ɗaukan Karim Benzema na daga cikin abubuwan da suke ƙara cusa wa Ronaldo bakin ciki a Al-Nassr.
Benzema, wanda tsohon ɗan wasan gaban na Faransa kuma tsohon abokin wasan Ronaldo a Real Madrid ne ya koma Al-Hilal da Al-Ittihad a ranar Litinin bayan kawo ƙarshen kwantaraginsa.
Benzema mai shekara 38 a duniya ya riƙa atisaye shi kaɗai bayan samun saɓani da shugabannin ƙungiyar Al-Ittihad kan batun tsawaita kwantaraginsa.
"Ya cika son gasa kuma ba ya son ya ga wasu ƙungiyoyin na ƙara ƙarfi," kamar yadda wani da ya san abubuwan da ke gudana a ƙungiyar Al-Nassr ya shaida wa BBC, game da Ronaldo.
Wannan al'amari zai kara iza wutar raɗe-raɗi game da halin da Ronaldo ke ciki a Saudiyya - mene ne abin da ke faruwa da Ronaldo a Al-Nassr?
Ya zaman Ronaldo ya kasance a Saudiyya?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ronaldo ya yi ƙoƙarin tun bayan komawarsa ƙungiyar Al-Nassr, inda ya zura ƙwallo 14 a kakar wasa ta 2022-23 a babbar gasar Saudiyya ta Saudi Pro League, bayan zuwa ƙungiyar a tsakiyar kaka.
Ronaldo ya kasance wanda ya fi kowane ɗan wasa zura ƙwallo a kakar wasanni biyu da suka gabata, inda ya zura ƙwallo 35, sai kuma 25.
Bayan karrama shi da lambar yabo ta ɗan wasa mafi hazaƙa a Gabas ta Tsakiya a bikin bayar da lambar yabo ta ƴan wasan ƙwallon ƙafa na duniya a cikin watan Disamba, Ronaldo ya ce: "Kun san burina.
"Abin da nake so shi ne na ci kofuna kuma ina so na zura ƙwallo (1,000), duk kun san haka. Zan iya yin hakan in dai ban ci karo da raunuka ba."
Ya zura ƙwallonsa ta 17 a wannan kakar a karawar da suka yi da Al-Kholood a ranar Juma'a, wanda hakan ya sa ya zura jimillar ƙwallaye 961 a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa – inda yake sa ran zura ƙarin 39 domin kai wa 1,000.
To sai dai Ronaldo ya gaza lashe kofuna.
Al-Nassr ta kammala a matsayi na biyu a kakar wasanni biyu na farko bayan isar sa, sai kuma ta ƙare a ta uku a kakar da ta gabata da maki 13 a bayan Al-Ittahad.
Haka nan Al-Nassr ta sha kashi a hannun Al-Hilal a wasan ƙarshe na Kofin Sarki – a gasar 2023-2024, a bugun fenariti.










