Ronaldo zai bar Al-Nassr, Chelsea da City da Liverpool na rububin Robin Roefs

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Cristiano Ronaldo
Lokacin karatu: Minti 2

Dan wasan gaban Portugal Cristiano Ronaldo, wanda zai cika shekaru 41 a ranar Alhamis, zai kauracewa wasa na biyu da Al-Nassr, duk da cewa ya saka hotonsa yana atisaye, kuma yana iya neman barin kungiyar Saudi Pro League a watan Yuni. (ESPN)

Idan Ronaldo ya bar Al-Nassr, watakila komawarsa zai koma kungiyarsa ta farko Sporting Lisbon. (Fichajes)

Elliot Anderson na Nottingham Forest ne kan gaba a jerin 'yan wasan tsakiya da Manchester United ke son dauka. Ragowar wadanda kungiyar ke nema sun hada da abokin wasansa na Three Lions Adam Wharton, mai shekaru 21, na Crystal Palace, da kuma ɗan wasan Kamaru da Brighton Carlos Baleba, mai shekaru 22, (The Athletic)

Atletico Madrid na shirye ta sayi ɗan wasan baya na Tottenham Cristian Romero, mai shekaru 27, bayan wani sabon rubutu da ɗan wasan na Argentina ya yi a shafukan sada zumunta yana sukar ƙungiyarsa. (Sun)

Babban jami'in gudanarwa na Newcastle United David Hopkinson ya ce "ba shi da masaniya" ko wakilin Sandro Tonali ya yi wa Arsenal tayin dan wasan mai shekara 25, bayan jita-jitar da ake ta yadawa dangane da yiwuwar komawar dan wasan tsakiyar na Italiya kungiyar a ranar ƙarshe ta kasuwar musayar yan wasan kwallon kafa. (Talksport)

Chelsea, da Manchester City da Liverpool suna sha'awar sayen mai tsaron raga na Sunderland na Netherlands Robin Roefs, inda kungiyar ke sa ran tayin sama da fam miliyan 50 ga dan wasan mai shekaru 23. ((Football insider)

A shirye dan wasan baya na Faransa Dayot Upamecano, mai shekaru 27 yake, ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya a Bayern Munich wadda za ta ba shi damar ci gaba da zama a zakarun na Bundesliga har zuwa watan Yunin 2030. (Fabrizio Romano)

Wolves sun amince da tayin Palmeiras na fam miliyan 21.6 don siyan ɗan wasan gefe na Colombia Jhon Arias, kuma ɗan wasan mai shekaru 28 ya riga ya tattauna yarjejeniyar sirri da ƙungiyar ta Brazil. (UOL)

Bayanai na cewa har West Ham ta amince da yarjejeniyar fam miliyan 27 don siyan ɗan wasan gaba na Crystal Palace Eddie Nketiah, mai shekaru 26, a lokacin musayar 'yan wasa, kafin raunin da ɗan wasan ya samu ya kawo ƙarshen tattaunar. (Athletic)