Man Utd na son Mateta, Goretzka zai iya komawa Arsenal

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool na hamayya da Manchester United da Real Madrid kan ɗanwasan tsakiya na Crystal Palace da Ingila Adam Wharton, mai shekara 21. (Mirror)
Manchester United za ta shiga zawarcin ɗanwasan gaba Jean-Philippe Mateta, mai shekara 28 a bazara bayan ɗanwasan na Faransa da Crystal Palace ya gaza komawa AC Milan. (Mirror)
AC Milan da Chelsea da Newcastle na rubibin ɗanwasan gaba na Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 26 wanda suke son ɗaukowa a bazara daga Juventus. (Football Italia)
Manchester United na son ƙarfafa tsakiyarta kuma tana son ɗanwasan Newcastle da Italiya Sandro Tonali, mai shekara 25, is of interest. (Metro)
Everton za ta yi wa ɗanwasan gaba na Ingila Dwight McNeil tayin sabuwar yarjejeniya bayan ya gaza komawa Crystal Palace kafin rufe kasuwar ƴanwasa. (Football Insider)
Newcastle za ta farfaɗo da buƙatarta kan ɗanwasan tsakiya na Ivory Coast Patrick Zabi, mai shekara 19. (The i - subscription required)
Golan Leeds United da Faransa Illan Meslier, mai shekara 25, ga alama zai koma Turkiya a ƙungiyar Besiktas. (Teamtalk)
Ɗanwasan tsakiya na Jamus Leon Goretzka, mai shekara 30, wanda yarjejeniyarsa ta kawo ƙarshe a Bayern Munich zai iya komawa Arsenal. (Bayern Insider)
West Ham na iya rasa kocinta Nuno Espirito Santo ba tare da biyan diya ba idan har ƙungiyar ta koma buga Championship. (Athletic - subscription required)











