Ko za a iya dakatar da Shari'ar Musulunci a Arewacin Najeriya?

Lokacin karatu: Minti 3

Ƴan Najeriya musamman na arewacin ƙasar sun fusata dangane da bayanan da ke nuna yadda wani gungun ƴan Najeriya ya bayyana a gaban Majalisar Dokokin Amurka inda ya nuna wa majalisar cewa Shari'ar Musulunci da ake yi a arewacin Najeriya ce ke taimakawa wajen azabtar da Kiristoci a ƙasar.

Tuni dai Majalisar Ƙoli ta addinin Musulunci da sauran ƙungiyoyin Musulmi na arewacin Najeriya suka yi kakkausan martani dangane da batun.

Wannan ne ya sa BBC ta yi nazari kan Shari'ar ta Musulunci a tsarin kundin Mulkin Najeriya da kuma ko akwai yiwuwar cire ta daga kundin.

Shari'ar Musulunci a tsarin mulkin Najeriya

Barista Bulama Bukarti wanda lauya ne mai zaman kansa a Burtaniya ya shaida wa BBC cewa cire Shari'ar Musulunci daga tsari mulkin Najeriya ba abu ne mai sauƙi ba.

"Maganar Shari'a da kuma ƙarfin da aka bai wa majalisun dokokin jihohi na cikin kundin tsarin mulki, wanda sauya shi na da wuya domin shugaban ƙasa shi kaɗai ba zai iya yi ba."

"Haka ma ƴan majalisar tarayya su kaɗai ba za su iya yi ba. Dole ne sai an haɗa da ƴan majalisar jihohi. Kuma ka ga majalisun jihohin da ke ɗabbaƙa shari'ar Musulunci da al'ummominsu ba za su yarda a cire shari'a da Hizba ba daga tsarin mulki ba," in Bukarti.

"Barista Bukarti ya ƙara da cewa hanyar cire shari'ar Musulunci da Hizba daga tsarin mulki guda ɗaya ce kawai, wato yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima wanda kuma zai yi matuƙar wuyar gaske."

"Sashe na 9 na kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya tanadi yadda za a yi wa tsarin mulki gyaran fuska kuma ya ce dole ne sai an samu kashi biyu bisa uku na dukkannin ƴan majalisar dattawa da wakilai sun goyi bayan ƙudirin yin kwaskwarimar. Sannan kuma daga nan za a tafi majalisun jihohi inda sai an samu kaso biyu bisa uku, wato jihohi 24 na jihohi 36 na ƙasar."

Yaushe Shari'ar Musulunci ta fara aiki a Najeriya?

Bukarti ya ce shari'ar Muslunci ta samu shiga kundin tsarin mulkin Najeriya tun 1979 duk da cewa ambatonta ya fi shahara a 1999 bayan gyaran fuska da aka yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar.

Ya ce bayan yi wa tsarin mulin Najeriya a 1999 wanda ya bai wa jihohi damar yin dokoki kan laifi, sai aka samu raji daga wurin al'ummu na neman a yi hukunce-hukunce kan laifuka.

"Abin da ya faru har aka yi rajin dawo da shari'ar Musulunci a 1979 shi ne kundin tsarin shekarar ya tanadi shari'ar Musulunci ne a kan mu'amala kamar aure, gado da iyali da dai sauran su wanda ya janyo aka kafa kotunan shari'ar Musulunci.

To amma a 1999 sai aka samu masu rajin da ke son a samu shari'o'in kan laifuka. Kuma wannan ne ya sa ƴan majalisa suka yi dokokin laifuka bisa doron addinin Musulunci kuma har aka kakkafa kotunan addinin Musulunci. Ke nan da ma akwai shari'ar amma yanzu faɗaɗa ta kawai aka yi," in ji Bukarti.

Rikicin Obasanjo da Hizba

Masanin ya ce idan aka yi duba dangane da abin da ya faru tsakanin Obasanjo da rundunar Hizba, a ƙoƙarinsa na ganin an rushe rundunar, daga nan za a fahimci ƙarfin majalisar dokoki.

"Lokacin da Obasanjo ya je kotu yana son a ruguje Hizba, ka ga bai yi nasara ba, inda kotu ta kori ƙarar tana mai cewa ba huruminta ba ne shiga al'amarin. Saboda ai dokokin majalisar jiha ne suka kafa Hisba saboda tsarin mulki ya ba su ƙarfin iko na samar wa kansu dokokin hukunta laifuka."

Jihohin arewacin Najeriya dai da ke bin tafarkin Shari'ar Musulunci sun fito da rundunar Hisba domin tabbatar da biyayya ga dokokin addini, musamman abin da ya shafi ɗa'a da tarbiyya.

Sai dai kuma rundunonin sun fuskanci ƙalubalen suka daga ƙungiyoyi masu rajin kare haƙƙin ɗan'adam inda suke kwatanta ayyukan Hisba da na ƙungiyoyin ƴan sa-kai ko ƙato da gora.

Jihohin Arewa 12 da ke yin tsarin Shari'a

Aƙalla jihohin Najeriya 12 ne daga cikin 36 ke dabbaƙa dokokin Shari'ar Musulunci.

Ga jerin jihohin 12:

  • Zamfara State
  • Kano State
  • Sokoto State
  • Katsina State
  • Bauchi State
  • Borno State
  • Jigawa State
  • Kebbi State
  • Yobe State
  • Kaduna State
  • Niger State
  • Gombe State