Manyan malaman da suka yi tasiri a arewacin Najeriya har bayan rasuwarsu

Lokacin karatu: Minti 6

Mabiya da almajiran Sheikh Dahiru Bauchi na ci gaba da bayyana irin gudunmawar da fitaccen malamin ya bai wa Addinin Musulunci a tsawon rayuwarsa.

A makon da ya gabata ne shehin malamin ya rasu yana da kimanin shekara 100 a duniya bayan fama da jinya.

Shehin malamin ya kasance cikin fitattun malaman da suka yi matuƙar tasiri a tarihin ƙasar.

Bayan Sheikh Dahiru Bauchi akwai wasu malaman da suka yi matuƙar tasiri a Najeriya, ko dai sanadiyyar hidima ga addini ko al'umma ko kuma duka biyun.

BBC ta duba wasu daga cikin irin waɗannan malamai waɗanda suke da matuƙar tasiri a lokacin rayuwarsu da kuma bayan sun shuɗe.

Abubakar Gumi

An haifi Abubakar Mahmud Gumi ne ranar Juma'a 7 ga watan Nuwamban shekarar 1924.

Shahararren malamin addinin Musulunci ne kuma masanin shari'a, wanda ya kai har matsayin Alkalin Alkalai (Grand kadi) na arewacin Najeriya.

Ya kasance kan gaba a ƙoƙarin bai wa mata dama su koyi ilimin addini.

Ya yi rubuce-rubuce masu yawa na littattafan addini ciki har da tafsirin al-qur'ani mai girma.

Kimanin shekara 33 bayan rasuwarsa, miliyoyin Musulmai a Najeriya na ci gaba da bin koyarwarsa, sannan ƙungiyoyin da ya jagoranci kafawa ne a gaba-gaba wajen yaɗawa da kuma tafiyar da al'amuran Musulunci a ƙasar.

Baya ga Shehu Usman Danfodiyo, wanda ya yi jihadin sake ɗabbaƙa addinin Musulunci a ƙasar Hausa a farkon shekarun 1800, ana ganin cewa babu wani malami da koyarsa ta Musulunci ta yi tasiri a Najeriya kamar Abubakar Gumi.

Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya rasu ne a ranar 11 ga watan Satumba shekara ta 1992, a birnin Landan na ƙasar Birtaniya.

Isma'ila Idris Jos

Sheikh Ismail Idris Zakariyya ya kasance ɗaya daga cikin fitattun malaman addinin musulunci mafiya tasiri a Najeriya.

An haife shi a shekarar 1937 a garin Gwaskwaram na jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya.

Koyarwarsa ta fi mayar da hankali ne kan muhimmancin tsayuwa kan sunnar Manzon Allah (S.A.W) tare da kawar da abubuwan da yake ganin an cakuɗa addini da su.

A shekarar 1978, Sheikh Zakariyya ya kafa ƙungiyar Izala da taimakon Sheikh Abubakar Gumi, da nufin kawo sauyi a yadda ake gudanar da ayyukan ibada da addini a Najeriya.

Cikin ƙanƙanin lokaci ƙungiyar ta samu karɓuwa, inda ta zama ɗaya daga cikin ƙungiyoyin addini mafiya tasiri a fagen addini a ƙasar.

Sheikh Zakariyya na da almajirai masu yawa da suka riƙa yaɗa koyarsa har bayan rasuwarsa.

Ya rasu ne ranar 25 ga watan Janairun 2000 a garin Jos na jihar Filato.

Nasiru Kabara

An haifi Sheikh Nasiru Muhammad Kabara a shekarar 1912 a ƙauyen Gurungawa da ke wajen birnin Kano.

Sheikh Nasir Kabara - wanda shi ne jagoran ɗariƙar Qadariyya - ya karɓi ɗarikar ne a wurin wani fitaccen malamin ɗarikar mai suna Sheikh Sa'ad da ke unguwar Alfindiƙi a birnin a Kano.

Bayan da shehun Malamin ya samu izini sai ya fara assasa zawiyya ta hanyar mayar da soron gidansa wurin zikiri, inda ya samu mutum huɗu da suke gudanar da ayyukan ɗarikar tare.

Allah ya huwace wa Sheikh Nasiru Kabara basirar rubutu inda mafi yawancin rubuce-rubucensa yake yin su domin warware wata mas'ala da aka bijiro masa da ita.

Masana da masu nazarin littafan marigayi Nasiru Kabara sun ce har yanzu babu ƙididdigar yawan littafan da ya rubuta kasancewar rubutunsa na hannu ne.

Yana ɗaya daga cikin malaman da tasirinsu ya ci gaba da wanzuwa har bayan rasuwarsu a wajen almajirai da mabiyansu.

Sheikh Nasiru Kabara ya rasu ranar Juma'a 4 ga watan Oktoban 1996, a gidansa da ke birnin Kano yana da shekara 84 a duniya.

Aliyu Harazimi

An haifi Sheikh Aliyu Harazimi a shekarar 1919 a unguwar Hausawa da ke birnin Kano.

Sheikh Aliyu Harazimi na ɗaga cikin fitattun jagororin ɗariƙar Tijjaniya mafiya kusanci da Sheikh Ibrahim Inyass.

Marigayi Sheikh Harazimi ya kasance ɗaya daga cikin fitattun malaman ɗarikar Tijjaniyya a Afirka ta Yamma, wanda tasirinsa ya bazu har zuwa wajen Najeriya.

Fitaccen Shehin malamin ya rasu yana da shekara 93 bayan gajeriyar jinya a gidansa da ke unguwar Hausawan Mandawari a ƙaramar Hukumar Gwale da ke Jihar Kano.

Isa Waziri

An haifi Sheikh Isa Waziri a shekarar 1925 a garin Kano da ke arewacin Najeriya

Ya yi karatunsa na Allo a ciki da wajen ƙasar kano, sannan ya halarci makarantar koyon Aikin Shari'ah ta Kano, daga bisani ya tafi Jami'ar Al-Azhar da ke Masar, inda ya ƙarasa karatunsa.

Ya kuma samu ilimin shari'ah da koyar da Ilmin Addinin Musulunci.

Ado Bayero ya naɗa shi limamin Masallacin Murtala da ke kano, kuma a nan ya ci gaba da tafsirin Alqur'ani mai girma, kafin daga baya Ado Bayero ya naɗa shi matsayin babban limamin Kano.

Bayan rasuwar ɗan'uwansa ne kuma sarkin Kanon na wancan lokaci ya naɗa shi matsayin wazirin Kano.

Shekh Isah Waziri ya ba da gudunmawa da dama a ciki da wajen Kano a harkokin addini, kuma ya yi ƙoƙari wajen ganin an yi aiki da Shari'ar Musulunci a ƙasar Kano.

Ja'afar Mahmud Adam

Fitaccen masanin Al-qur'ani da tafsiri ne da yake da tasirin gaske a zukatan mabiyansa.

An haife shi ne a ranar 12 ga watan Fabrairun shekarar 1961 a Daura jihar Katsina.

Daga baya ya koma Kano don yin karatun allo yana da kimanin shekara huɗu a duniya.

Ya yi fice a tafsirin Al-qur'ani, inda a mafi yawan lokuta yake gudanar da tafsirin nasa a birnin Maiduguri na jihar Borno a kowane watan azumi.

A lokacin da yake tafsiri a Maiduguri, fitaccen malamin ya sha gwagwarmaya da masu aƙidar Boko Haram, inda suka sha yin muƙabala da shugaban ƙungiyar na farko, Muhammad Yusuf.

Wasu ƴan bindiga ne suka harbe malamin yayin da yake Sallar Asuba a ranar 13 ga watan Afrilun shekarar 2007 a Kano.

Duk da cewa har yanzu jama'a na ci gaba da bayyana mutuwarsa a matsayin wani babban rashi, amma kuma har yanzu babu wani da aka kama laifin kisan malamin.

Auwal Albany Zariya

An haifi Muhammad Auwal Adam da aka fi sani da Albani Zariya a ranar 27 ga watan Satumban 1960.

Babban masanin ilimin Hadisi ne da shari'a da ke da ƙwarewa a ilimin fasahar sadarwar intanet.

Ya kasance jagoran aƙidar Salafiyya a Najeriya, mai neman ɗaɓɓaka koyarwar Sahabban Manzon Allah (S.A.W).

Ana yi masa kallon fitaccen malamin Salafiyya a Najeriya, da ya sha gwagwarmayar tabbatar da koyarwar a yankin arewacin Najeriya.

Malamin na da tasiri matuƙar musamman wajen ɗimbin mabiyansa.

Malamin ya gamu da ajalinsa bayan da wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka kashe shi a ranar 1 ga watan Fabarairun 2014.

Kamar yadda shaidu suka bayyana 'yan bindigar sun harbe malamin da iyalin nasa ne lokacin da suke cikin mota suna kan hanyar su ta komawa gida daga makaranta a cikin garin Zaria jihar Kaduna.

Dahiru Bauchi

Shiekh Dahiru Usman Bauchi babban malamin ɗarikar Tijjaniyya ne da ake ji da shi a nahiyar Afirka, sannan malami ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga koyar da Al-qur'ani.

Shehun malamin na ɗaya daga cikin malamai a Najeriya da suka sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa addinin Musulunci hidima.

Ya yi fice wajen sanin Al-qur'ani mai girma da tafsirinsa, kamar yadda masana Al'qur'ani a Najeriya ke bayyanawa.

Malamin na da tarin ƴaƴa masu yawa, inda ɗaya daga cikinsu ya ce kusan 70 daga ciki sun haddace Al-qur'ani.

Cikin wata hira da ya yi da BBC a 2019, Sheikh Dahiru Bauchi ya ce baya ga kasancewa almajirin Sheikh Ibrahim Inyass, akwai dangantakar auratayya a tsakaninsu inda ya auri ƴaƴan Sheikh Inyass har guda biyu.

Shehin malamin na da miliyoyin mabiya a nahiyar Afirka, da ke bin koyarwarsa sau da ƙafa.

Sheikh Dahiru Bauchi ya sha gwagwarmayar kare aƙidarsa daga malaman da ke ganin akwai kura-kurai a Tijjaniya.

Da asubahin ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamban 2025 ne malamin ya rasu a garin Bauchi da ke arewacin Najeriya.