Wane ne Sheikh Ɗahiru Bauchi, jagoran ɗarikar Tijjaniyya da ya rasu?

    • Marubuci, Usman Minjibir
    • Aiko rahoto daga, Abuja, Najeriya
  • Lokacin karatu: Minti 6

Da Subahin ranar Alhamis ta 27 ga watan Nuwamban 2025 ɗin nan Allah ya yi wa fitaccen jagoran ɗarikar Tijjani a Najeriya, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi rasuwa.

Majiya daga iyalan marigayin ta tabbatar wa da BBC cewa an ajiye gawar Shehun a wani asibiti da ke Bauchi kafin ranar Juma'a lokacin da za a yi masa jana'iza.

An dai sha baza labaran rasuwar Shehin malamin kafin yanzu, inda kuma iyalansa ke ƙaryatawa.

Shiekh Dahiru Usman Bauchi babban malamin darikar Tijjaniyya ne da ake ji da shi a nahiyar Afirka, sannan malami ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga koyar da al'kur'ani, littafin Musulmi mafi girma.

Shehun malamin na daya daga cikin malamai a Najeriya da suke sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa addinin Musulunci hidima.

Tarihin rayuwar Sheikh Ɗahiru Bauchi

A wata tattaunawa da BBC ta yi da Sheikh Dahiru Bauchi a 2019 da kuma 2024 ya shaida cewa an haife shi ne a ranar 28 ga watan Yunin 1927, dai-dai da 2 ga watan Muharram 1346, wato Shehin malamin ya rasu yana da shekaru 98 kalandar Turawa amma a ta Musulunci ya rasu yana shekara 100 da ƴan watanni kenan.

An haife shi a wani gari da ake kira Nafada da ke jihar Gombe, wanda garin mahaifiyarsa ce, "kasancewar a al'adar Fulani ana haihuwar dan fari ne a gidansu mahaifiyarsa," in ji shi.

Ya kara da cewa: "Ni Bafulatani ne ta wurin uwa da uba. Dukkanin kakannina hudu Fulani ne.

"Sunan mahaifiyata Maryam 'yar Hardo Sulaiman. Sunan Mahaifina Alhaji Usman dan Alhaji Adam."

Sheikh Dahiru ya haddace kur'ani a wurin mahaifinsa kafin daga bisani ya tura shi Bauchi domin neman tilawa.

Mahaifinsa almajirin Shehu Ibrahim Nyass ne kuma mukaddami a cikin darikar Tijjaniyya ta hanyar Amadu Futiy kafin Shehi Ibrahim Nyass ya bayyana.

"Mahaifiyata ita ma ta je Kaulaha har sau biyu, kuma Shehu ya kaddamar da ita har ya ba ta carbi, saboda haka ni da mahaifina da mahaifiyata da 'ya'yana da jikokina duk gaba daya mun taru a cikin Shehu Ibrahim,"

Ya yi auren fari a shekarar 1948 lokacin yana da shekara 20 "da wata daya."

Iyalan Shehu

A tattaunawarsa da BBC, ɗaya daga cikin ƴaƴan Shehin malamin, Sheikh Bashir Dahiru Usman Bauchi ya ce a yanzu yawan ƴaƴan da malamin ya haifa sun kai kimanin 90, sannan yana da jikoki da suka zarce 300.

Babban ɗa namiji na malamin shi ne Muhammad Bello, wanda ya rasu tun yana ƙarami, sai kuma mai bi masa, Dakta Hadi Dahiru Bauchi.

Ya bayyana cewa akwai ƴaƴan malamin sama da 70 waɗanda suka haddace Alƙur'ani, kuma jikokinsa sama da 100 ne suka haddace Ƙur'anin.

"Wasu daga cikin yarana sun haddace kur'ani tun suna shekara bakwai da haihuwa kuma tun ma kafin su iya rubutu a allo.'' in ji sheikh Dahiru Bauchi.

"Akwai yarana hudu da suka haddace kur'ani a shekara biyar kamar daya daga cikin 'ya'yana da ke Kaduna. Su da ka suke haddacewa amma dai ba zai hana su rubutu a allo ba idan suka girma.

"Sai dai ban sani ba ko a cikin 'ya'yan nawa akwai wanda ya rubuta kur'ani saboda su kan fita kasashen waje domin neman karatu na sauran fannonin addini da ma boko.

"Yanzu ma akwai daktoci a cikin yaran," a cewar Shehun Malamin da bakinsa.

Matan Sheikh Dahiru Bauchi

BBC ta mika tambayar ga daya daga cikin 'ya'yan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda ya bayar da amsa kamar haka:

"Matan Shehi hudu ne a yanzu haka. Sai dai kuma da dama sun mutu sannan kuma wasu da dama sun fita," in jiDakta Bashir.

Sheikh Bashir ya ce a yanzu haka Dahiru Bauchi na da mata huɗu. Su ne:

  • Hajiya Fatima (Nana)
  • Hajiya Khadija (Inna)
  • Hajiya A'isha
  • Hajiya Maman Hamrat

Karatun Shehu

Sheikh Dahiru ya ce ya haddace kur'ani a hannun mahaifinsa Alhaji Usman dan Alhaji Adam ne domin shi ma mahaddacin alkur'ani ne.

Daga nan ne ya tura shi wurin malamai da dama domin tilawa, "kuma Alhamdulillahi na kan ji mutane na karin gishiri suna kira na gwani," in ji Malam.

Malam ya je Bauchi domin karatu. Malaman da ya yi karatu a hannunsu sun hada da Malam Ahmadu na Sabon gari da Gwani dan Fika da malam Alhaji na Gombe da dai sauran su.

Ya kara da cewa: "Ba gaskiya ba ne cewa na yi karatu wurin Shehi Nasiru Kabara. Malam Abubakar Gumi ne ya yi karatu wurin Shehi Nasiru Kabara.

"Na kuma karbi darikar Tijjaniya a hannun mahaifina."

Gangaran na Alƙur'ani

"Bayan na haddace Alkur'ani inda ake kira na gwani ko gangaran, na rubuta Alkur'ani na farko na bai wa babana kuma malamina kyauta.

"Na kuma rubuta na biyu wasu sun manta. Na fara rubuta na uku amma ban gama ba har yanzu.

"Ina da matsalar agana a idanuna dalilin da ya sa ba ni da nishadi kan duk abin da za a kalla," a cewarsa.

Malamin ya ce matsalar idanun ce ta sa bai yi wasu rubuce-rubuce ba a fannoni.

Dangane kuma da tafsirin Alkur'ani, ya ce ya fara ne a shekarar 1951 ko 1952.

"Ni kuma tafsirina ba na duba takarda saboda haka Annabi yake yi, sannan haka ma manyan bayin Allah suka yi.

"Idan mutane suka tambaye ni me ya sa ba na rike takarda a tafsirina, sai na tambaye su cewa kuna rike kur'ani idan kuna karanta Suratul Ikhlas a sallah.

"Na san kur'ani saboda haka ba sai na rike shi ba idan zan yi tafisiri," in ji Sheikh.

Shehun malamin ya ce abu ɗaya daga cikin biyu da ya fi ƙauna a rayuwarsa shi ne karatun Alƙur'ani da kuma sanya fararen tufafi.

Sirrin karatun Shehu

Shehun Malamin ya ce: "Sirri na Allah ne. Da farko dai muna kiran wani abu da ake kira fafau da muke rubuta wa mutum ya sha domin zuciyarsa ta fafe ya haddace kur'ani.

"Muna da wani sirri da muke rubuta wa yaro a duk Laraba sau uku. Ana rubuta masa ya lashe. Zai haddace kur'ani kuma duk garin da ya zauna sai an yi tafiyar wata uku kafin a samu mahaddaci kamarsa.

"Sai dai ba mu sani ba ko wata ukun na tafiyar kafa ne ko kuma a mota," kamar yadda ya ce.

Ya ce ada can sai sun je garin Barebari sannan su haddace kur'ani amma yanzu ko ina ana iya haddace shi.

Suna da makarantu kusan 300 na almajirai a Najeriya, kuma yaran ba sa wuce shekaru hudu ba tare da sun haddace kur'ani ba sai dai idan suna da nauyin kwakwalwa.

Yawan aikin Hajji

A 2019, Sheikh Dahiru Bauchi ya shaida wa BBC cewa "tun daga shekarar 1970 kawo yau sau daya ne kawai ban je aikin Hajji ba."

Hakan na nufin ya yi aikin hajji sau 48 ya zuwa 2019 ɗin kenan.

Shehi na jin harsuna biyar

"Ni dai Bafulatani ne kuma ko an ji ni ina Fulatanci babu mamaki. Mahaifina yana da tsangaya a kasar Borno inda yake da almajirai Hausawa da Barebari.

"Saboda haka tun a lokacin na iya Hausa da Barbarci kuma tun ina karami na tashi da wadannan.

"Da na girma kuma na iya Larabci kadan da yaren Wolof na su Shehi Nyass da Bolanci.

Wani sanannen abu ne cewa Shehu Ɗahiru Usman Bauchi na gudanar da karatukansa ne a harshen Hausa.

Dangantakar Shehi da Sheikh Ibrahim Inyass

Sheik Dahiru Usman Bauchi ya kuma shaida wa BBC cewa, baya ga kasancewa almajirin Sheik Ibrahim Inyass, akwai karin dangantaka mai karfi a tsakaninsu.

Ya ce: ''Alhamdulillah baya ga zama almajirin Sheik Ibrahim na kuma zama khadiminsa, kana na zama surukinsa, don na auri 'ya'yansa har sau biyu, na auri daya bayan ta rasu ya sake bani auren daya.''

Kana malamin ya ce baya ga haka, yana ƙauna tare da mutunta malamai a ko ina suke, musamman malaman Tijjaniyya.

''Babu abin da ke faranta min rai irin na ga Musulunci ya bunkasa, in ga darikar Tijjaniyya ta bunkasa,'' in ji malamin.