Makarantar Neja ta fitar da jerin sunayen ɗalibanta da aka sace

Cocin Katolika da ke Kotagora ta fitar da sunayen ɗalibai da malaman da 'yanbindiga ke ci gaba da yin garkuwa da su bayan sace su daga makarantar St. Mary a garin Papiri na jihar Neja.

Cocin ta ce sabon jerin sunayen da aka tattara ranar 24 ga watan Nuwamba ya nuna cewa waɗanda ke hannun masu garkuwar su 265 ne.

Jerin ya ƙunshi malamai biyar, da ma'aikata bakwai, da ɗaliban sakandare 14, da ɗaliban firamare 239.

An sace ɗaliban ne a ranar Juma'a, 21 ga watan Nuwamba, lokacin da 'yanbindigar suka auka wa makarantar da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.

Daga baya ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya Christian Association of Nigeria (CAN) ta yi iƙirarin cewa 50 daga cikinnsu sun kuɓuta kuma har sun koma wajen iyayensu. Sai dai gwamnatin jihar na nuna shakku game da iƙirarin tana mai cewa ba ta iya tabbatar da sahihancin labarin ba.

Ana kyautata zaton yaran da suka gudu lokacin harin ne suka koma gida, ba waɗanda aka tafi da su daji ba.

Bayan sanarwar kuɓutar ɗaliban ne kuma CAN ta sauya zuwa 265 daga fiye da 300 da ta ce tun farko. Sai dai ba za mu iya wallafa sunayen ɗaliban ba saboda tsaron lafiyarsu.

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Neja ta tura dakarunta zuwa Papiri, kamar yadda Kwamashinan 'Yansanda Adamu Abdullahi Elleman ya shaida wa BBC.

CP Adamu ya ce "tun daga ranar farko da lamarin ya faru muka tura jami'anmu da sauran dakaru na musamman".

Ya ƙara da cewa makarantar ba ta sanar da su ba game da ɗalibai 50 da aka ce sun kuɓuta daga hannun masu garkuwar.

'Yadda ɗana mai shekara shida ya tsira'

Wani uba ya bayyana yadda ɗansa mai shekara shida ya tsere daga cikin ɗaruruwan ɗaliban da aka yi garkuwa da su a makarantar ta Neja.

Da yake shaida wa BBC labarin ɗan nasa, mutumin da muka sakaya sunansa ya ce: " Lokacin da na gan shi na yi farin ciki sosai."

"Na kira sunansa, ya juyo ya kalle ni, kuma na rungume shi."

Lucas ya ce ɗan nasa ya faɗa masa cewa suna tsaka da barci lokacin da suka fara jiyo harbin bindiga.

Maharan sun karya tagogin ɗakunan kuma suka tilasta musu buɗe ƙofofi. A lokacin ne kuma wasu ɗdaliban suka fara haura shinge na waya.

Duk da cewa Lucas ya hadu da ɗansa ɗaya, akwai sauran biyu da ba a gan su ba har yanzu.

Ba mu da tabbas kan adadin ɗaliban St. Mary da aka sace - Gwamna Bago

Gwamnan jihar Neja Umar Bago ya ce duk da cewa ba ya so a mayar da hankali kan ɗora wa wani laifin sace ɗaliban makarantar St. Mary's ta Papiri, ya dasa alamar tambaya kan haƙiƙanin adadin ɗaliban da aka sace.

Lamarin ya fara jawo muhawara mai zafi ne bayan da gwamnatin jihar ta ce ta bayar da umarnin a rufe makarantun yankin da abin ya faru baki ɗaya, sakamakon samun rahoton barazanar tsaro, amma makarantar ta yi gaban kanta wajen sake buɗe karatu ba tare da neman izinin gwamnati ba.

A cikin wata hira da BBC, shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN reshen jihar, Bishop Bulus Dauwa Yohanna ya musanta iƙirarin gwamnan cewa an buƙaci su kulle makarantar.

''Ba wanda ya ce mana mu rufe makaranta saboda barazanar tsaro, ba inda aka taɓa faɗa mana haka'', in ji shi.

Talla

Amma a zantawarmu da gwamnan jihar, Umar Bago ya nanata cewa lallai gwamnati ta bayar da umarnin rufe makarantar saboda matsalar tsaro, sannan ya ƙara da cewa "ko bayan samun labarin hare-hare a jihar Kebbi da Kwara mun sake bayar umarnin a rufe makarantun da ke yankin Neja ta Arewa," in ji shi.

'Gwamnati ba ta yi mana ƙoƙari'

Shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Neja, Bishop Bulus Dauwa Yohanna ya zargi hukumomin ƙasar da rashin kataɓus a ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban.

A tattaunawarsa da BBC, Bishop Yohanna, wanda shi ne mamallakin makarantar, ya ce zuwa yanzu hukumomi ba su ɗauki wani 'matakin a zo a gani' ba kan batun ceto yaran da aka sace.

Bishop Yohanna ya shaida wa BBC cewa matakin da hukumomi suka ɗauka zuwa yanzu shi ne karɓar sunayen yaran da ƴanbindigar suka yi awon gaba da su.

''Zuwa yanzu ban san wani ƙoƙari da hukumomi ke yi fiye da karɓar sunayensu'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa kawo yanzu ba shi da masaniyar tura jami'an tsaro domin ceto ɗaliban.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Neja da gwamnatin tarayya su haɗa ƙarfi wurin guda domin ceto ɗaliban makarantar.

Me ya janyo musayar yawu tsakain CAN da gwamnatin Neja?

An fara samun saɓanin ra'ayi tsakanin gwamnati da ƙungiyar CAN, tun bayan da ƙungiyar ta ce ɗalibai 50 daga cikin waɗanda aka sacen sun kuɓuta.

Bayan da CAN ta fitar da sanarwar da a ciki ta ce tuni aka mayar da ɗaliban wajen iyayensu, ƴansanda suka ce suna da shakku game da labarin kuɓutar ɗaliban.

Ƴansandan sun ce sun buƙaci ƙungiyar ta ba su hujjar kuɓutar ɗaliban, amma ba su samu ba, don haka rundunar ta ce "ba mu da tabbacin alƙaluman yaran da suka tsere da ma inda sauran suke a yanzu."

Shi ma gwamnan jihar Umaru Bago ya bayyana cewa babu adadi a hukumance na yawan ɗaliban da aka sace a makarantar.

Amma mamallakin makarantar ya ce adadin haka nan yake.

Shi ma kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya nanata wannan batu cikin wata hira da ya yi da gidan talbijin na Arise ranar Litinin.

Onanuga ya ce har yanzu ba tabbas game da adadin ɗaliban da aka sace a Neja.

"A yanzu da nake maka magana, an bar hukumomi cikin duhu kan adadin mutanen da aka sace. Kun ce an sace ɗalibai, to ku fito da sunayensu, ya kamata mu san abin da muke nema,'' in ji shi.

Sai dai shugaban CAN reshen jihar Neje, Bishop Bulus Dauwa Yohanna ya ce sun tattara adadin ɗaliban ne bayan da suka tantance ɗaliban da suke makarantar da waɗanda ba sa nan bayan faruwar harin.