Abin da ya sa ba zan koma APC ba — Bafarawa

Asalin hoton, BAFARAWA/BBC
Tsohon gwamnan jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, Attahiru Bafarawa, ya nesanta kansa da ga batun komawa jam'iyyar APC mai mulkin kasar.
Bafarawa ya shaida wa BBC cewa shi dama kowa ya san ya yi ritaya daga siyasa, a don haka batun ya koma APC sam ba shi da wannan niyyar.
Ya ce,"Idan za a iya tunawa na ce na bar siyasa ko ta zabe ko ta nadi, kuma babu wata jam'iyya da zan shiga, amma zan shiga kungiyar taimakawa matasa da sauransu."
Attahiru Bafarawa, ya yi wannan kalamai ne bayan da dubban magoya bayansa suka koma jam'iyyar APC a jiharta Sokoto, sakamakon abin da suka kira gamsuwa da kamun ludayin mulkin gwamnan jihar Ahmad Aliyu.
Bafarawa ya ce," Mutanen ma'ana magoya bayana su ba su yi ritaya daga siyasa ba a don haka ba za su iya zaman banza ba saboda na ce na bar siyasa don haka idan ni na daina su suna damar yin duk abin da suke so."
" Sai da suka same ni suka ce mini na fada musu jam'iyyar da nake so su koma, na ce musu a'a su je su yi shawara su koma duk inda suke so, daga baya suka dawo suka ce sun koma APC na ce musu Allah ya bada sa'a." In ji shi.
Tsohon gwamnan na Sokoto ya ce, " Shekarata 50 ina siyasa don haka dole ina da magoya baya, to amma tun da sun san na bar siyasa dole su nemi abin da ya fiye musu, don hak duk mai cewa da goyon bayana wadannan mutane suka koma APC, to ba haka bane, ni bar siyasa kamar yadda nake fada a koyaushe,
" Ya ce masu ganin kamar wai don magoya bayan sun koma APC, ni ma na koma, to ba haka bane, domin idan mutu ba ya zuwa duk wani taro na jam'iyya babu ruwansa da duk wani abu da ya shafi jam'iyyar to sai ace shi dan jam'iyya ne ai hakan ya nuna cewa babu ruwana da jam'iyyar."
"Kuma ina ganin kashi 70 ko 80 cikin 100 na magoya bayan nawa da suka koma APC, sun koma ne domin bin tafiyar gwamnansu saboda hankalinsu ya kwanta da yadda ya rikesu." In ji shi.
Bafarawa ya ce," Ni shawarar da zan bawa magoyana shi ne sun riga sun koma jam'iyyar APC don haka dole su yi hakuri sannan kuma kada su bude baki su ce suna bukatar a basu wani abu da ya shafi siyasa su yi hakuri da sannu a hankali za a lura da irin rawar da suke takawa a jam'iyyar in ya so anan sai a basu abin da suke so."
Ya ce," Na tabbatar mutanena ba sun koma APC don neman wani abin duniya bane domin da suna yin hakan da tuni sun rabu dani don sunan tafiyarsu ma Bafarawa Akida."
Tsohon gwamnan jihar ta Sokoto ya kasance a baya dan jam'iyyar adawa ta PDP ne inda a farkon 2025, ya sanar da ficewar shi daga jam'iyyar .











