Siyasar ubangida ce babbar illar mulkin farar hula a Najeriya - Bafarawa
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayyana siyasar ubangida da babbar illar mulkin dimokraɗiyya a tsawon shekaru 25 a Najeriya
Attahiru Bafarawa ya shaida wa BBC hakan ne a wata hira da ya yi dangane da cikar mulkin dimokraɗiyya 25 ba tare da katsewa ba.
" Mu da muka zo ba mu da 'kingmaker' wato ubangida, kowane gwamna zaman kansa yake amma bayanmu sai aka mayar da abin ubangida. Wasu gwamnoni ba su da kuɗin takara sai wasu su ba su saboda haka idan suka samu kujerar dole ne su biya. Wannan ya sa siyasa ta lalace saboda ta zama kamar zuba jari."
Wani ƙalubalen da tsohon gwamnan ya ce shi ma ya yi wa dimokraɗiyya dabaibayi, shi ne yadda aka talauta 'yan Najeriya amma idan lokacin zaɓe ya yi sai a fito musu da kuɗi.
"Hakan ya janyo jama'a sun zama mayunwata." In ji Bafarawa.
Dangane da irin cigaban da aka samu a mulkin dimokraɗiyya, Bafarawa ya lissafa abubuwa kamar kwanciyar hankali da Ilimi da noma da zaman lafiya da kuma ƙaruwar arziki.
Matsalar Rashawa da cin hanci
Tsohon gwamnan na jihar Sokoto ya ƙara da cewa gwamnatin tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ita ce ta fi kowacce muni a shekaru 25 na mulkin dimokraɗiyya musamman ta fuskar rashawa da cin hanci
"Ka ga duk wani wanda zai iya kare Buhari ko gwamnatinsa to za mu haɗu a lahira domin Allah shi ne babban alƙali amma bala'in da Buhari ya kawo ƙasar nan dangane da dimokraɗiyya na cin hanci ban taɓa ganin gwamnati wadda ta kawo mana masifa a rayuwata ba irin ta Buhari..." In ji Bafarawa.
To sai dai ya yaba wa gwamnatin shugaba Obasanjo wadda ya ce ta ba su dama irin wadda ba a taɓa bai wa gwamnoni ba a tsawon mulkin dimokraɗiyyar, inda ya ce an sakar musu mara su yi abin da suke so a jihohinsu.
Abubuwan da muka yi a Sokoto
Tsohon gwamnan ya bugu ƙirji cewa "duk wani Basakkwace zai bayar da shaida" cewa an samu cigaban ilimi da lafiya a lokacinsa da sauran fannin cigaba.
"In ka dubi hanyoyi inda aka samu kwalta wajen kilomita dubu kewayen jihar Sokoto lokacin da muka zo ƙananan hukumomi takwas ne kawai ke da wutar lantarki daga cikin 23 da ake da su amma kuma sai na muka tabbatar da kowacce ta samu wutar lantarki.
Haka ma maganar ruwa da tsaro saboda abin da ke janyo matasalar tsaro shi ne talauci kuma mun bar ƙananan hukumomi sun yi amfani da kuɗaɗensu." In ji Bafarawa.












