Cutukan da suka kamata a yi taka-tsantsan da su lokacin azumi

Asalin hoton, Getty Images
Al'ummar Musulmi a faɗin duniya na ci gaba da azumtar watan Ramadan domin ibada ga mahaliccinsu.
Azumi na nufin daina cin abinci da abin sha, da kusantar iyali daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana da nufin neman yardar Ubangiji.
To sai dai kamar yadda likitoci suka yi bayani akwai wasu cutuka da ke tasowa, ko suna iya ƙara muni a lokacin azumi sakamakon daina cin abinci a tsawon wuni.
Haka kuma a gefe guda likitocin sun ce akwai wasu cututtuka da ake samun sauƙi musamman a lokacin azumin.
Cutukan da ka iya tashi lokacin azumi

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Mu'awiya Aliyu ma'aikaci a hukumar lafiya ta jihar Katsina ya ce a lokacin azumi akwai cututtuka da ka iya tashi kamar:
Gyambon ciki
Cuta ce da ke sanya cikin mutum ya yi ta zafi kamar an barbaɗa borkono.
''Hakan na faruwa ne saboda ƙarancin abinci a cikin mutum, kuma mai ɗauke da cutar zai riƙa jin tana tashi a lokacin da bai ci abinci ba'', in ji Dakta Mu'awiya.
Cutar ƙoda
Dakta Mu'awiya ya ce akwai wasu cutakan da ke shafar ƙoda, waɗanda rashin shan ruwa ke haddasa su.
Likitan ya ce masu irin wannan cuta, akan ba su shawara, su riƙa yawan shan ruwa a kai-a kai.
Cutar mafitsara
Ita ma wannan cuta ce da ke bukatar yawan shan ruwa kasancewa ruwan kan taimaka wajen wanke ciwon da ke damun mafitsarar.
Wasu cutuka da ke janyo taruwar duwatsu
A cikin ƙodar mutum ko mafitsara, su ma waɗannan cutuka akan buƙaci mai fama da su ya riƙa yawan shan ruwa wanda zai taimaka wajen narkar da duwatsun.
Likitan ya ce ''irin waɗannan cutuka su ma suna yawan tashi musamman a lokacin azumi''.
Haka kuma Dakta Mu'awiya ya ce akwai cutar Matsarmama wadda ita ma ke buƙatar yawan shan ruwa.
Cutakan da ake samun sauƙinsu a lokacin azumi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Haka kuma, likitan ya zayyana wasu cutuka da ya ce ana samun sauƙin tashinsu musamman a lokacin azumi.
Cutukan zuciya
Likitan ya ce da ma mafi yawan abin da ke haddasa cutukan zuciya su ne yawan kitse da maiƙo a jikin zuciyar.
Cutar kansa
Wasu dalilan cutar, su ne girma na wuce kima da wani ɓangare na jikin mutum ke yi, ''to a wannan yanayin da mai cutar ke azumi, to ka ga babu abincin ma da mutum zai ci balle cutar ta habaka'', in ji likitan.
Cutar amai da gudawa
Likitan ya ce ''Da ma ta hanyar cin wani nau'in abinci da ya gurɓata ko ya cuɗanya da ƙwayar cutar ne ake samun amai da gudawa, to amma idan ana azumi, (ai) ba a ma ci abincin ba, balle a ci ƙwayar cutar''.
Cutar hanta
Hanta ita ce ke tace duk wani abinci domin fitar da abubuwa marasa amfani da mutum ya ci, kamar yadda Dakta Mu'awiya ya bayyana.
Ya kuma ce ''idan mutum na azumi hantarsa za ta samu sauƙin aiki, to a nan hantar kan samu sauƙi sosai a lokacin da babu abincin da hantar za ta tace''.
Cutar ƙiba
Likitan ya ce ƙiba ma cuta ce, inda kitse yake taruwa a cikin tumbin mutum, ko ƙirjinsa ta yadda zai rufe zuciya ko ƙodar mutum.
A cewarsa, azumi yakan taimaka wajen rage ƙibar kasancewar lokacin cin abincin mutum ya zama ƙayyadajje.
Abincin da ya kamata a riƙa ci da azumi

Asalin hoton, Getty Images
Dr Mu'awiya Aliyu ya ce akwai wasu nau'o'in abinci da abin sha waɗanda ya kamata mutane su riƙa ci ko sha musamman a lokutan shan ruwa ko sahur, a cewarsa za su taimaka wajen kwantar da cutukan da ke tashi musamman a lokutan azumi.
Likitan ya ce irin nau’o'in abincin kan taimaka wajen kwantar da cutuka, don kuwa, idan aka yi sahur da su, to mutum zai daɗe bai ji yunwa ba, bayan wayewar gari.
Ya ce duk wani abinci nau’in furotin (Protein) kan taimaka wajen daɗewa a jikin mutum, kasancewar abincin ba ya narkewa da wuri.
Sannan ya shawarci mutane su guji yin amfani da ruwa ko lemukan sanyi musamman a lokacin shan ruwa.
A cewarsa, ba laifi mutum ya fara da kurɓa ruwa, amma ba mai sanyi sosai ba.
‘’Amma idan mutum zai iya, to ya daure ya fara da ruwan ɗumi, wanda zai taimaka wajen narkar da kitsen da ke cikin mutum, amma idan ya fara da ruwan sanyi to zai iya ƙara daskarar da kitse’’, in ji Dakta Mu’awiya.
Likitan ya ce lemukan sanyi, ba sa taimaka wa jiki ko lafiyar mutum, hasali ma a wasu lokutan cutar da jikin mutum suke yi, saboda suna ɗauke da sinadarin sukari.
Ya kuma shawarci masu azumi, su riƙa amfani da abinci mai sinadarin Glucose, saboda zai taimaki mutum wajen maido masa da ƙarfin da ya rasa a lokacin da yake azumi.











