Mene ne matsayin azumin mai ƙarya?

- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist (Multimedia)
- Aiko rahoto daga, Abuja
Ƙarya, a cewar malaman addini, wani baƙin hali ne maras kyau, da kan sa Musulmi ya yi asarar ɗumbin lada a duk lokacin da ya kantara ƙarya.
Yin ƙarya a cikin watan azumi ko ba a watan ba, babban saɓo ne, a cewar Sheikh Halliru Maraya
Fitaccen malamin addinin Musulunci da ke jihar Kaduna, ya ce matuƙar mutum ya mutu yana ƙarya, bai tuba ba, zai haɗu da azabar Allah.
"Yana da kyau mutum ya nisanci ƙarya saboda bai san gwargwadon ladan azumin da zai yi asara ba idan ya tafka ta, a cikin watan Ramadan," in ji malamin.
Kuma Allah (SWT) zai yi masa hukunci da azaba mai yawa.
Azumi dai ibada ce da Allah ya farlanta a kan bayinsa, inda akan buƙaci kamewa daga ci da sha da kusantar iyali, sannan da kiyaye gaɓoɓin jiki daga aikata duk wani abin ƙi.
Akwai ladubban da ake son mai azumi ya siffanta da su.
Daga ciki, akwai nisanta kai daga sharara ƙarya da gulmace-gulmace da annamimanci.
"Ya zama wajibi ga mai azumi ya kiyaye harshensa ga yin ƙarya, ya tabbatar ya guje wa furta duk wani sharri ko saɓanin alheri, a cikin watan azumi balle har ta kai ga yin ƙarya," in ji Halliru Maraya.
Ko ƙarya tana lalata azumi?
Malamin addinin Musuluncin ya ce yin ƙarya ga mai azumi, ba wai yana nufin azuminsa ya karye ba ne.
Sai dai ya ce illar da ƙarya ke yi ga azumi shi ne zabge lada domin "da tana lalata azumi, za a ce idan mutum ya yi ƙarya da azumi a bakinsa, to azuminsa ya ɓaci, bayan sallah sai ya sake ko ya yi ramuwa."
Ko kuma da za a ce idan mutum ya yi ƙarya da gangan, sai a ce bayan rama azumin ma, sai kuma ya yi kaffara, in ji malamin.
Ya ce yana da kyau mutum ya guji yin ƙarya saboda yin ta, na rage ladan azumi.
Hanyoyin kauce wa yin ƙarya da azumi...
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Malamin ya ce akwai hanyoyi da dama da mai azumi zai bi don guje wa furta abin da zai zama ƙarya har ta kai azuminsa ya samu rauni.
Mai azumi zai iya cimma hakan, ta hanyar zama mai yawan ibada a magance - yawan istighfari da hailalah da yawan salatin Annabi (SAW).
Sannan kuma ya zama mai yawan karatun Al-Qur'ani, kuma ya ƙaurace wa mutane waɗanda ba larura ce ta sa sai ya haɗu da su ba kamar a kasuwa ko wajen aiki.
A guji zama a dandali ana hirarrakin babu gaira babu dalili, don kuwa hakan ne ke jawo har mutum ya yi ƙarya, a cewar Sheikh Maraya.
Sheikh Halliru Maraya ya ƙara da cewa ga waɗanda suke amfani da wayoyinsu, su kuma su guji amfani da ita, idan ba hakan ya zama dole ba - mutum ya raja'a wajen karatun Qur'ani.
"Da dare kuma nafiloli domin rabautar wannan wata mai albarka, musamman cikin goman ƙarshe tun da a cikinsu ne ake dacewa da ganin daren Laylatul Qadr wanda ya fi wata dubu," in ji malamin.
"Idan mutum ya dace da wannan dare, za a rubuta masa fiye da wata dubu, fiye da wata dubu sallar nafila da yake da daddare,"
"Idan mutum ya dace da Laylatul Qadr ta hanyar ƙaurace wa mutane da dagewa wajen ibada, ba mai zai samu damar yin ƙarya ba." a cewar Sheikh Halliru Maraya.











