Ƙasashen Afirka biyar da suka fi ƙarfin soji

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
- Lokacin karatu: Minti 4
Ƙungiyar nan ta ƙasa da ƙasa, ta Global Firepower, mai fitar da jadawalin mizanin ƙarfin sojojin ƙasashen duniya, ta fitar da rahoton da ke cewa a shekara ta 2025 Najeriya ta kasance ta 39 a ƙarfin soji daga cikin ƙasashe 145 na duniya.
Shekaru uku jere ƙarfin sojojin ƙasar na raguwa kamar yadda rahoton ƙungiyar ya nuna.
A duniya, Amurka ce ta farko a jadawalin inda ta shafe shekaru 18 jere tana kan matsayin.
Sauran ƙasashen da suke baza ƙarfin sojinsu sun haɗa da Rasha, da China, da Indiya, da kuma Koriya ta Kudu wadda ta kasance ƙasa ta biyar a duniya da take da ƙarfin soji.
Mun yi nazarin jadawalin da ƙungiyar ta fitar ga kuma jerin ƙasashe biyar da suka fi ƙarfin soji a nahiyar Afirka.
Masar

Asalin hoton, Getty Images
Masar ce ƙasa ta farko a nahiyar Afirka kuma ta 19 cikin ƙasashe 145 na duniya da ƙungiyar ta yi nazarin ƙarfin sojinsu a 2024.
Ƙungiyar ta GFP ta bayyana cewa Masar tana bajekolin ƙoƙarin da take na zamanantar da tsarin tsaronta inda take da dubban motocin sulke da sauran makaman yaƙi.
Masar ta riƙe wannan matsayi ne saboda yadda take iya ƙera manyan makamai na fasaha, da yawan ma'aikatanta, da ƙarfin sojin ruwanta, da na jiragen sama na musamman, da kuma kasafin tsaro mai yawa.
Shugaba Abdel Fattah El-Sisi ya bayar da gudummawa wajen samar da gagarumin ci gaba a fannin ƙarfin soji da sabunta makaman ƙasar. Ƙasar ta ƙulla alaƙa mai ƙarfi da ƙasashen duniya wajen haɓaka dakarun ƙasar.
yawan sojojin Masar sun kai dubu ɗari huɗu da arba'in yayin da take da jiragen yaƙi 238.
Masar na kashe kusan dala biliyan shida duk shekara a harkokinta na tsaro, kamar yadda nazarin GFP ya bayyana.
Aljeriya

Asalin hoton, AFP
Aljeriya ce ta biyu bayan Masar wajen ƙarfin soji a nahiyar Afirka inda kuma a jerin ƙasashen duniya ta kasance ta 25.
Kamar kowace ƙasa, Aljeriya tana da sojoji na ƙasa na ruwa da kuma na sama ƙari da dakarun tsaron sararin samaniya wadda ta maye gurbin sojin National Liberation Army, wani ɓangare na ƙungiyar National Liberation Front da ta yi yaƙi da mulkin mallakar Faransa lokacin yaƙin nemar wa Aljeriya ƴancin gashin kai tsakanin shekarar 1954 zuwa 1962.
Ƙungiyar ta GFP ta ƙiyasta cewa kasafin da ƙasar ke ware wa ɓangaren tsaronta duk shekara ya kai dala biliyan 25.
Tana kuma da jiragen yaƙi 102 da sojoji dubu ɗari uku da ashirin da biyar.
Najeriya

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Najeriya ce ta uku a Afirka, kuma ta 31 a duniya cikin ƙasashe 145 inda ta samu maki 0.5771.
Najeriya tana bayar da gudummawa sosai wajen samar da tsaro a yammacin Afirka saboda kasafin kuɗin da take ware wa tsaro da kuma ayyukan sabunta makaman yaƙi.
A cikin gida kuma, dakarun ƙasar na bayar da gudummawa wajen murƙushe ayyukan ta'addanci musamman a yankin arewa maso gabas sannan kuma ta kasance ɗaya daga cikin na gaba-gaba a Afirka da ke ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya a duk lokacin da aka samu ɓarkewar hatsaniya a wata ƙasa ta nahiyar.
A kasafin kuɗin da gwamnatin ƙasar ta ware wa ɓangaren tsaron ya kai naira tiriliyan 4.91, fiye da adadin da aka ware wa ɓangaren a kasafin da ya gabata.
A jadawalin GFP, Najeriya tana ware sama da dala biliyan uku a jumulla wajen tafiyar da al'amuran tsaron ƙasar duk shekara.
Tana kuma da jirage yaƙi 14 sannan yawan sojojinta sun kai 230,000.
Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images
Afirka ta Kudu ce ƙasar da ke biyewa Najeriya inda ta zo ta huɗu a Afirka kuma ta 40 a duniya.
Afirka ta Kudu ta yi fice wajen amfani da makamai na zamani da ƙwararrun sojoji saboda albarkatun ƙasar da take da su.
Ƙasa ce da ta fifita tsaronta sannan kuma tana shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya a ƙasashen da aka samu tarzoma.
GFP ta bayyana cewa ƙasar tana ware dala biliyan 2,266,800,000 a matsayin kuɗin ta take kashewa a ɓangaren tsaronta.
Sannan kuma tana da yawan sojojin da suka kai 71, 235 haɗi da jiragen yaƙi biyu.
Habasha

Asalin hoton, AFP
Habasha ta kasance ta biyar a Afirka kuma ta 52 a duniya a ƙarfin soji
Ƙungiyar ta GFP ta bayyana cewa Habasha ta ware sama da dala biliyan biyu don tafiyar da harkokin tsaron ƙasar.
A cewar jadawalin, ƙasar tana da yawan jiragen yaƙi da suka kai 25 sannan yawan sojojinta sun kai dubu ɗari da sittin da biyu.










