Yadda ya kamata a kula da mai sikila a lokacin damuna

Ƙwayoyin jini da ke ɗauke da amosani na ƙunshe da wani sanadarin da ake kira haemoglobin wanda ya gurɓata - wannan kan sanya ƙwayoyin jinin su lanƙwashe kamar fasalin wata a kwanakin farko

Asalin hoton, Science Photo Library

Bayanan hoto, Ƙwayoyin jini da ke ɗauke da amosani na ƙunshe da wani sanadarin da ake kira haemoglobin wanda ya gurɓata - wannan kan sanya ƙwayoyin jinin su lanƙwashe kamar fasalin wata a kwanakin farko

Najeriya na daga cikin ƙasashen da suka fi yawan masu fama da cutar sikila a duniya.

Hasali ma, an fi samun cutar ne a ƙasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara.

Sikila dai cuta ce ta gado wadda ke sauya fasalin ƙwayoyin jini, lamarin da kan jefa masu fama da ita cikin mummunan yanayi.

An ware ranar 19 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin ranar yaki da cutar amosanin jini wato sikila a duniya. Rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin fadakar da al'umma kan wannan cutar a matakin kasa da kuma na kasa da kasa.

Shin ta yaya ake kula da masu cutar sikila a lokacin sanyi, sannan waɗanne muhimman abubuwa ne suka kamata ku sani kan cutar?

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

A tattaunawar ta da BBC, Hajiya Badiyya Inuwa, wadda ke da wata gidauniyar taimaka wa masu fama da cutar sikila ta ce yara da ma duk sauran masu fama da cutar na buƙatar kulawa sosai.

Ta kuma ce damuna lokaci ne da kan zo da yanayi na sanyi wanda ke matuƙar illa ga masu fama da cutar.

Ga wasu hanyoyi da ta ce za a iya bi domin kare yara masu sikila daga faɗawa cikin haɗari a lokacin damuna:

  • A rinƙa kai yara masu sikila asibiti domin karɓar magani
  • A rinƙa bai wa yara abinci mai kyau
  • A yi hanzarin kai yaro mai sikila asibiti idan ya nuna alamar damuwa
  • A kare yara masu sikila daga cizon sauro domin gudun kamuwa da maleriya
  • Kada a bar yara masu sikila cikin sanyi domin kauce wa mura
  • A rinƙa saka musu kayan sanyi
  • Kada a bar mai sikila ya yi wasa cikin ruwa
  • Kada a aiki yaro mai sikila cikin sanyi

Ga wasu abubuwan da suka kamata ku sani kan cutar sikila:

1. Najeriya ta fi yawan masu cutar a duniya

Bincike ya nuna cewa duk shekara ana haifar jarirai 300,000 a duniya kuma rabi daga wannan yawan a Najeriya ake haifar su. Daga cikin 150,000 na Najeriya din nan 100,000 ne ke mutuwa duk shekara.

Alkaluma sun nuna cewa mafi yawan masu cutar suna arewacin kasar ne. Masana kiwon lafiya sun yi amanna cewar rashin yin gwajin jini kafin aure yana taka rawa sosai wajen haifar yara masu dauke da cutar sikila a kasar.

2. Shan magunguna har abada

Masu fama da cutar sikila suna fara shan wasu magunguna tun daga lokacin da aka gano suna dauke da cutar har zuwa karshen rayuwarsu, kamar yadda Dr Bashir Isa Waziri, wani likita a asibitin koyarwa na Aminu Kano ya shaida mana.

''Daga cikin magungunan akwai 'Folic Acid' wanda yake kara musu jini, saboda kwayoyin jininsu na yawan karewa. Akwa kuma 'Paludrine' magani ne da ke kare su daga kamuwa da cutar maleriya don tana wahalarsu sosai idan suka kamu.

Sai maganin 'Peniciillin V' shi kuma aikinsa shi ne kare su daga cututtuka masu alaka da numfashi. Sai 'Hydroxyurea' wanda yake taimaka wa kwayoyin jinin siffarsu ta zama mai kyau, yake kuma taimaka musu wajen rage tashin ciwon. Amma yawanci shi sai wanda ciwon ke masa tsanani,'' in ji likitan

3. Yawaita shan ruwa

Yawan shan ruwa abu ne mai matukar muhimmanci ga masu cutar sikila saboda rashin ruwa yana tayar musu da ciwon kwankwaso da na gabobi.

Sannan shan ruwan na sa jini ya dinga gudu yadda ya kamata kuma kwayoyin jini su dinga wucewa cikin jiyoyi, wanda haka ke hana ciwon yawan tashi.

4. Zafin ciwon ya fi na nakuda

Tsananin zafin ciwon kwankwaso da masu cutar kan yi fama da shi lokaci zuwa lokaci yana matukar uzzura musu. Kwararru a harkar lafiya sun ce zafinsa ya fi na nakuda.

Dr Bashir Waziri ya ce: "Suna jin ciwon kashi kamar ana kwankwatsa shi, jini ba ya isa wasu wuraren don haka idan suka taru a waje daya sai su saka ciwo.''

5. Shafar lafiyar jima'i

Likitan ya kuma cewa wannan ciwo bai bar masu shi ta bangaren shafar lafiyar jima'insu ba. Ciwo ne da ke hana su rawar gaban hantsi sosai a wasu lokutan ta wannan fanni.

''Ga maza dai yawanci gbansu ya kan mike mike ya ki sauka, kwayoyin jini masu kamar kauje na makalewa a gabansu sai jinin ya ki fita ya taru a wajen, sai al'aurarsu ta mike ta ki sauka.

''A wasu lokutan har sai an yi 'yar karamar tiyata, wasu kuma da an sanya kankara sai ta taimaka wajen kwantar da gaban,'' in ji Dr Bashir.

6. Kuka da ihu ba babba ba yaro

Tsananin zafin da ciwon ke zuwa da shi kan sa masu yin sa su dinga gurzar kuka tare da gunji da gurnani. A irin wannan yanayi ba babba ba yaro za a ga sun fita hayyancinsu.

Wata mai fama da wannan lalura da ba ta so a fadi sunanta ta ce: ''Ba zan iya kwatanta yadda xiwon yake ba, illa iyaka zan ce na kan ji kamar an kwankwatsa min kashina da guduma. Shi ya sa duk dauriyar mutum dai an ji sautin kukansa.''

Bayanan bidiyo, Tattaunawa akan cutar Sikila tare da Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa

7. Karaya ba tare da jin ciwo ba

Dr Bashir ya ce daga cikin wasu abubuwan mamaki dangane da wannan ciwo shi ne yadda a wasu lokutan sai ƙashin wata gaɓa ta jikin masu ciwon ya karye ɓal. ''Ba komai ke jawo hakan ba sai tsabar zafin ciwon da ke taso musu,'' in ji shi.

Hajiya Badiyya Inuwa
Bayanan hoto, Hajiya Badiyya Inuwa