Yadda ake yaƙi da camfe-camfe kan cutar sikila

Asalin hoton, OTHERS
Cutar sikila ta fi kama mutane a ƙasashen Afrika fiye da sauran sassan duniya.
Sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye ya tattauna da wani mutum wanda ke taimaka wa mutane masu fama da cutar sikila a wani gari a Kenya inda kusan kashi ɗaya bisa uku na mutanen garin ke fama da cutar wadda ke da alaƙa da gado.
A wani ƙaramin gari na Taveta, da ke kusa da tsaunin Taita a kan iyakar ƙasar Kenya da Tanzania, iyalai sukan taru su zauna kan benci cikin wata rumfa a wani asibitin ƙauyen.
Mutanen da ba su samu wajen zama ba sukan tsaya kan ciyayi.
"Wane ne a nan yake fama da cutar sikila?" in ji Lea Kilenga Bey, matar da aka jima ana sauraron bayani daga gare ta ta tambayi matan da ke zaune a sahun gaba.
"Dukkanmu," muka bayyana da murya guda, abin nufi shi ne ko dai sun taɓa suna ɗauke da cutar ko kuma suna kula da wani mutum da yake fama da ita."
A kasuwar wannan gari mai cike da hada-hadar jama’a a kusa da tsaunin Kilimanjaro, mai yawan alumma 22,000, kusan mutum guda cikin mutane hudu mazauna garin na ɗauke da cutar sikila, ɗaya daga cikin cututtukan gado mafi yawa a kasar.
Ƙwayoyin halittun jini na wasu mutanen da ke fama da cutar sikila, suna kama da sabon jinjirin wata, kuma ba su da karfin ɗaukar isasshiyar iska wadda za ta karaɗe jiki.
Masu fama da cutar sikila suna fuskantar matsanancin ciwo mai tsanani wanda a wasu lokuta sukan shafe mako guda cikin yanayin ciwo mai tsanani.
A cewar hukumar lafiyar ta duniya WHO, kashi biyu bisa uku na mutanen da ke fama da cutar sikila a duniya suna rayuwa ne a ƙasashen Afrika.
Ta kasance cutar gado mafi yaɗuwa a yankin, kuma alƙaluman da ake samu na mutanen da ke warkewa daga cutar ba wani mai karfafa gwiwa ba ne.
Fiye da rabin yaran da ake haihuwa ɗauke da cutar sikila suna mutuwa ne kafin su kai shekaru biyar da haihuwa, yawanci saboda ciwon wasu cututtuka da kan kama su ko kuma ƙarancin jini. Wasu mujallun kiwon lafiya sun bayyana cewa alƙaluman mace-macen ƙanana yara masu fama da cutar sun kai kashi 90 bisa 100.

Asalin hoton, LEA KILENGA BEY
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wata mata a asibitin ta ɗaga hannu domin yin tambaya.
"Sun ce duk wanda ke ɗauke da cutar sikila ba zai rayu sama da shekaru 20 ba. Suna iya rayuwa ne kawai zuwa shekaru 15, mafi ƙololuwa shi ne shekaru 18."
Ms Bey ta ce an gano tana ɗauke da cutar sikila ne tun tana da wata shidda a duniya kuma ta rayu, a yanzu haka tana da shekaru 30 a duniya.
"Wannan tsinuwa ce," wata mata ta faɗi da karfi.
A shekarar 2017, Ms Bey ta kafa wata ƙungiyar yaƙi da cutar sikila a Afrika, ta mayar da hankali wajen inganta rayuwar mutane masu fama da cutar.
Tana yawan ziyartar unguwanni domin wayar da kan jama’a game da yaɗuwar cutar ta hanyar gado, amma ta koma garin Taveta, garinta na asali, domin taimaka wa mutanen garin.
"Da yawa daga cikin al'ummun yankunan suna alaƙanta cutar sikila da tsinuwa, ko maita, kamar yadda," Ms Bey ta bayyana wa BBC Africa Eye.
"Wannan wani al’amari ne da babu wanda ya san shi a tsakanin alumma. Mutane suna ƙirƙirar labaran da ke shafar yankunansu.
Don haka, ya kamata na je na faɗakar da jama’a cewa cutar sikila ba maita ba ce. Ba kuma saboda tsinuwar gado ba ne. Matsala ce da za mu iya magance ta."
Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da mutane masu fama da cutar sikila ke fuskanta a garin Taveta, da sauran garuruwa a fadin ƙasar Kenya, shi ne rashin samun damar samun magunguna.
'Ko dai abinci ko magunguna'
Akwai buƙatar bayar da kulawa ga masu fama da cutar a kullum domin su rayu kamar kowa: amfani da magungunan 'antibiotics' masu kashe ƙwayoyin cuta domin kare kamuwa da wasu cututtuka, da magungunan daidaita ƙwayoyin jini da samar da karin sinadarai masu taimaka wa jiki, kamar maganin folic acid da ke taimakawa wajen magance karancin jini.

Albert Loghwaru ya kasance mai fafutukar wayar da kan jama’a bayan gano ‘yayansa na ɗauke da cutar sikila kuma sun fuskanci tsangwama.
"Galibin mutanen da ba su iya mallakar ƙasa da dala guda ko dala biyu a rana, ba za su iya sadaukar da abincin gidajensu domin su sayi magani mai tsada ba," a cewar Ms Bey.
Sai dai su zaɓi ɗaya - "Ko dai abinci ko magani."
Ta fi kowa sanin matsanancin yanayi da masu fama da cutar sikila ke fuskanta, kamar tsananin ciwon da ake fama da shi sakamakon toshewar hanyoyin jini, wanda hakan na shafar dukkan sassan jiki.
Ms Bey ta naɗi wani bidiyo game da yadda ta sha fama da cutar sikila. Kwanciya a gado, ba tare da samun magani ba, ta bayyana yadda rabin idonta a rufe, da yadda take ɗanɗana kuɗarta sakamakon tsananin zafin ciwon.
Ba ta son sauran mutane su sha wahala.
A garin Taveta, ta bi sahun ayarin mutanen da ke zanga-zanga a wani asibitin ƙauyen domin neman a bayar da kulawa mai kyawu ga majinyata.
"Ana ba mu magungunan da wa’adin aikinsu ya ƙare.”
"Mutane da dama sun mutu saboda ba su da damar samun ingantattun magunguna," a cewar wata matar.
"Na faɗa wa abokiyata ina bai wa ɗana magani, amma idonsa har yanzu ruwan ɗorawa ne. Ta gano wa’adin aikin magungunan ya ƙare.”
Albert Loghwaru, mai shekaru 50, shi ne shugaban ƙungiyar. Ƴaƴansa biyu na fama da cutar sikilar. An yi ta tsangwamar su duk da kasancewar akwai mutane da dama masu fama da cutar a ƙauyen Taveta.
"Mutane a ƙauyen suna cewa abu biyu ne cikin ɗaya. Ko dai cutar muna maita ne shi ya sa muke tsotse jinin yara, ko kuma muna ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV."
Mr Loghwaru ya ɗaura ɗamara a yakin da yake yi domin tabbatar da an bai wa al'ummar yankin damar samun kulawar likitoci ga masu fama da cutar.
"Ya kamata mu samu hanyar tallafa wa irin waɗannan mutane."
A sakamakon wannan gangami, tare da wanda Ms Bey, ke yi, daga ƙarshe an yi nasarar buɗe asibitin kula da masu fama da cutar sikila a ƙauyukan Taita Taveta da ke ƙasar.
Amma wannan ba shi ne ƙarshen gwagwarmayar Ms Bey ba. “Wasa farin girki.”











