Mai ra'ayin tsanar Falasɗinawa na gab da zama ministan tsaron Isra'ila

Jam'iyyar Likud ta 'yan gurguzu da Firaministan Isra'ila Mai Jiran-Gado Benjamin Netanyahu ke jagoranta ta ce ta kammala ƙulla yarjejeniya da jam'iyyar Jewish Power mai tsattsauran ra'ayi don kafa gwamnati.

Yarjejeniyar ba ta nufin matakin ƙarshen kenan na kafa gwamnati, amma ta tabbatar wa shugaban Jewish Power, Itamar Ben-Gvir, Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida da kuma kujera majalisar tsaro.

A ƙarƙashin yarjejeniyar, Ben-Gvir zai shugabanci rundunar tsaron iyaka a yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan kuma za a bai wa jam'iyyar tasa ikon jaddada manufar tsugunar da Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna.

Nasarar da masu tsattsaura ra'ayi suka samu a siyasar Isra'ila ta ba da mamaki sosai a zaɓen da aka yi ranar 1 ga watan Nuwamba, amma me muka sani game da babban jagora Ben-Gvir?

Sahabin Kahane

Ben Gvir mai tsattsauran ra'ayi ne, waɗanda siyasarsu ta yi imanin cewa Isra'ila ta Yahudawa zalla kuma suke adawa da kafa ƙasar Falasɗinawa a kusa da su.

A baya ya goyi bayan amfani da tashin hankali ko ƙarfi a kan Falasɗinawa kuma ya yi kira da a kori duk Balaraben da ya ƙi yin biyayya daga ƙasar, a cewar jaridar Times of Israel, abin da ya ƙara masa farin jini.

An haife shi ranar 5 ga watan 1976 a wata unguwa a Birnin Ƙudus kuma iyayensa Yahudawan Iraƙi ne.

Ya fara gwagwarmayar siyasa tun yana ƙarami ƙungiyar Kach mai tsattsauran ra'ayi, wadda Rabbi Meir Kahane ya kafa.

Ben-Gvir na ɗaya daga cikin mataimakan shugaban ƙungiyar, Noam Friedman, a sansanin Kiryat Arba da ke tsakiyar Hebron.

Bayan ƙulla Yarjejeniyar Oslo, an ga Ben-Gvir na ɗaya alamar motar Firaministan Isra'ila na lokacin Yitzhak Rabin, yana cewa: "Za mu iya kaiwa gare shi."

Ƙasa da wata ɗaya, a ranar 4 ga watan Nuwamban 1995, aka harbe Yitzhak Rabin a birnin Tel Aviv yayin wani maci kuma daga baya ya mutu sakamakon raunukan da ya ji.

Jam'iyyar Jewish Power

Ben-Gvir ne ke jagorantar Jam'iyyar Jewish Power, wadda aka kafa da mabiyan Kahane masu yawa a 2012.

Jam'iyyar ba ta samu damar shiga majalisar Isra'ila ba da ake kira Knesset a zaɓukan 2013 da 2015.

Kafin zaɓen 2019, jam'iyyar ta shiga haɗakar Jewish Home wadda ta ƙunshi jam'iyyu masu tsattsauran ra'ayi. Haɗakar ta lashe kujera biyar, Jewish Power ce ta bakwai a yawan 'yan majalisar da ta samu a zaɓen.

A zaɓe na biyu da aka yi a 2019, jam'iyyar ta shiga zaɓen da kanta, inda ta samu kashi 1.88 kacal cikin 100 na ƙuri'un. Hakan ya sa ba ta samu kujera a majalisa ba bayan ta gaza samun kashi 3.25 na ƙuri'un.

A 2021, jam'iyyar ta shiga zaɓe cikin haɗaka da wasu jam'iyyun na masu tsattsauran ra'ayi da Mista Netanyahu ya ɗauki nauyi, inda Ben-Gvir ya shiga majalisa a karon farko.

A zaɓen watan Nuwamba na shekarar nan, Jam'iyyar Religious Zionism - taron haɗakar da Jewish Power ke jagoranta - ta cinye kujera 14 a zaɓen kuma ta zama ta uku mafi girma a majalisa.

Mista Netanyahu ne ya tattaro kan jam'iyyun a yanzu don jaddada nasarar masu tsattsauran ra'ayi da kuma tabbatar da cewa sun shiga majalisa da suna ɗaya.

Kuma hakan ce ta far a zaɓen da ya gabata, inda haɗakar masu tsaurin ta zarce abin da aka yi tsammani.