Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaben Kenya: Yadda gaisuwa ta kawo sauyi a yankin da aka haifi Odinga
Lokacin da muka kai ziyara mahaifar dan takarar shugaban kasar Kenya Raila Odinga, ta bayyana karara cewa matakin da ya dauka na hada kai da babban mai adawa da shi, kuma shugaba mai barin gado Uhuru Kenyatta ya janyo rabuwar kawuna.
An gyara hanyar shiga karamin garin mai cike da hada-hada mai suna Bondo, mai nisan kilomita 60 daga birnin Kisumu da ke bakin ruwa, an kuma gyara hanyar da ke zuwa har gaban gidan mahaifinsa marigayi Mzee Jaramogi, kamar yadda bisa al’ada ake kiransa kasancewarsa mataimakin shugaban Kenya na farko lokacin shirin karbar ‘yancin kasar.
Mzee Jaramogi ya yi aiki a gwamnatin Shugaba Jomo Kenyatta, mahaifi ga Shugaba Uhuru, har zuwa lokacin da suka bata daga nan mataimakin shugaban kasa ya kafa jam’iyyar adawa, an kuma tsare Mzee a gidan kaso a shekarar 1969 na tsawon watanni 18.
Tun daga nan iyalan biyu suka zama abokan gaba, amma a shekarar 2018 aka kawo karshenta, ta hanyar wata ‘musabaha’ da aka yi tsakanin Mista Odinga da Mista Kenyatta.
"Jim kadan bayan wannan gaisuwar tsakanin mutanen biyu aka gyara mana hanya. Har muna fatan gyaran ya kai sauran kauyuka, idan Mista Odinga ya zama shugaban kasa," in ji wani bakanike mai suna Isaac Omondi, inda yake bayani kan hanyar Bondo da a baya take cike da ramuka da fatan ganin an sake inganta ta.
An tsaurara matakan tsaro a gidan su Mista Odinga, mai shekara 77, inda ake ganin sojoji dauke da manyan bindigogi a tsaye kikam, kamar yadda aka san gidajen ‘yan takarar shugaban kasa gabanin zabe.
Idan ka dan leka, za ka iya gano ganin mai alfarma, da aka kewaye da manyan karafuna. A can wani bangare na gidanka na iya ganin wata Coci da aka yi wa adon da ke nuna mabiya darikar Roman Katolika ne.
Kamar yadda mazauna yankin suka ce Mzee Jaramogi yana bin darikar Roman Katolika ne lokacin da yake raye, danshi kuma ya ba da sadakar cocin inda makwabta ke zuwa domin yin bauta.
Sai dai an mayar da gidan maifin Odinga gidan adana kayan tarihi, inda mutane ke kai ziyara, aka kuma adana tarihin iyalan Odinga da kabilarsu ta Luo da ma kasar Kenya baki daya.
Cikin kayan tarihin akwai wasu daga cikin na Mzee Jaramogi, kamar fitattun hulunan da aka san shi da su, da sandarsa ta girma, da wata kyakkyawar kwalbar barasa da ta kasance ‘yar gaban goshinsa, har da kayan da ya sanya lokacin zaman kaso, da garmaho guda biyu.
Daga can bangaren dama ta gefen kofar shiga gidan tarihin, gidan farko da Mr Odinga ya mallaka da aka gina da itacen bishiyar timba.
"Cikin sauri Mista Odinga ya gina gidan, gabanin tafiyarsa kasar Jamus a karshen shekarun 1960 domin karo ilimi.
Mahaifinsa ne ya sanya masa sharadin sai ya gina muhalli da yin aure kafin ya dawo daga Jamus," in ji Mercellus Otieno wanda ke kula da gidan kayan tarihin.
Akwai kuma hotunan shugabannin Kenya hudu a bangon gidan tarihin. An bar wani sarari da za a sanya shugaban Kenya na biyar idan lokaci ya yi.
Yawancin al'umar Bondo na fatan zaben da za a yi ranar 9 ga watan Agusta zai kasance hoton Odinga zai shiga gurbin shugaba na biyar da aka adana a gidansu na gado, kuma gidan tarihi, ba sa fatan mataimakin shugaban kasa William Ruto ya yi nasara a zaben da ke tafe.
Wannan shi ne fatan Shugaba Uhuru Kenyatta, wanda bayan yin nasara kan Mista Odinga a zabuka biyu, a yanzu kuma yake mara masa baya da fatan ya gaje shi.
Masu sukar Mista Odinga sun ce adawarsa na tafiyar hawainiya, musamman suka kan batun cin hanci da rashawa a cikin gwamnati tun bayan gaisawar da suka yi da Shugaba Uhuru.
Yayin da shi kuma Mista Ruto ya fassara shirin na mutanen biyu da manufar karbe iko kamar yadda magabatansu suka yi lokacin su ne masu karfin fada a ji.
Amma ga magoya bayan "Baba" kamar yadda magoya bayan Mista Odinga, suka lakaba masa, sun ce ya cancanci jan ragamar Kenya, sakamakon yadda ya jagoranci gangamin da ya kawo karshen tsarin jam’iyya daya.
Amma kuma daga bisani wasu ne kadai ke shan romon nasarar da su ka jagoranci samarwa.
"Baba ya yi tsayin daka da fafutukar kafa dimokuradiyya a kasarmu, albarkacinsa ya sanya ake duba ayyukan da gwamnatoci ke yi.
Ina matukar alfahari da shi, ina da kyakkyawan fatan shi ne shugaban Kenya a wannan zabe," in ji Mista Omondi.
Batun matsin tattalin arziki, da rashin ayyukan yi da ake fama da su a kasar, na cikin abubuwan da Mista Odinga zai fuskanta idan ya zama shugaban kasa - kuma yana fatan kafa sabbin masana’antu da tayar da tsofaffi, da samar da ayyukan yi.
Ya kuma yi alkawarin samar da gidaje miliyan biyu ga ‘yan kasa matalauta, ta hanyar saukaka musu biyan kudin haya kan shilling 6,000 kwatankwacin dala 50 (Naira 35,500), karkashin wani sabon shirin da zai fito da shi idan aka zabe shi shugaban kasa.
Sai dai a lokacin da Mista Omondi, ke gyaran wata tsohuwar mota, ya ce yawancin mazauna Bondo ba sa son zama cima-zaune.
"Ba ma bukatar a ba mu kudi kyauta. Muna son aiki tukuru domin samun kudi.
"Abin da kawai muke bukata shi ne a ba mu tabbacin za a tallafa mana, a sama wa mutane aikin yi," in ji bakaniken mai shekara 46."
A shekarar da ta gabata an gyara hanyar birnin Kimusu da ke da tashar ruwa, an kuma yi sabbin hanyoyi har da tashar jirgin kasa, wannan ci gaba da aka samu ya yi wa direbobin manyan motoci da dakon kaya kamar John Atwoto dadi.
"Tashar ruwan ce ta sanya bukatar manyan motoci ta karu. Wannan hanya ta kara wa garuruwan Kakamega da Kitale saukin zuwa, hakan ya taimaka kwarai wajen safarar mutane," in ji shi.
Gaisuwar da mutanen biyu suka yi, da suka fito daga kabilar Luo da Kikuyu, wadda Mista Kenyatta ya fito, ta kawo karshen gabatar da ‘yan kabilun biyu ke yi da juna.
Wani mai gidan sayar da abinci a Kikuyu, ya ce zabuka biyu da suka gabata an fuskanci tashin hankali, amma a wannan karon ba ya fargabar komai, don haka ba zai bar Kisumu ba.
Sannan Mista Odinga ya karawa tafiyar siyasarsa armashi, wajen dauko mace mataimakiya idan ya yi nasara a zaben, wadda kuma ta fito daga kabilar Kikuyu wato Martha Karuwa.
Martha Karua ta taba rike mukamin ministar shari’a a lokacin mulkin Shugaba Mwai Kibaki.
"Ba na tunanin za a yi tashin hankali. Abin alfahari ne gare mu kabilar Kikuyu da aka zabi Karua, ka ga idan ya yi nasara mu ma za a dama da mu a cikin gwamnati," in ji Mr Mwangi.
Amma yawancin kabilar Kalenji da Mista Ruto ya fito sun fara tserewa daga Kisumu zuwa gida Eldoret.
Silas Lelei, matashin mahauci dan shekara 25, ya ce tuni matarshi da yara suka koma gida, shi ma nan da ranar daya ga watan Agusta zai tattara kayanshi ya bi su, ba zai dawo ba sai an kammala zabe an sanar da sakamako hankula kuma sun kwanta.
"Ba zan iya ci gaba da zama a nan ba, a tsorace nake. Ranar 1 ga watan Agusta zan rufe kasuwancin nan na koma gida," in ji shi lokacin da yake yankawa wani kwastoma nama.
Idan har Mista Odinga, ya yi nasarar zama shugaban kasa, zai kasance abin alfaha ga kabilar Luo, dan su na farko da ya taba zama shugaban kasar Kenya.
Inda Lucas Obwar, mai gyaran taya a Kisumu, ya ce wannan zai sanya su samu ayyukan yi a kuma dama da su a cikin gwamnati.
"Duk lokacin da muka nemi aiki a hukumomin gwamnati ba ma samu, saboda ba a taba yin shugaban kasa daga yankinmu ba, don haka aka mayar da mu saniyar-ware," in ji Mista Obwa.
Kamun Kifi na daga cikin kasuwancin da ke bunkasa arzikin Kisumu, mazauna yankin na fatan idan Odinga ya zama shugaban kasa zai kara bunkasa wannan fannin.
"Idan aka bunkasa harkar kamun kifi, za a samar da ayyukan yi da kudaden shiga," in ji Nelson Adul.
A kwai barkwancin da ake yi a Kenya wai kifi ya fi tsada a birnin Kisumu, fiye da ko ina a kasar, kuma wasu tarin mata da ke sayar da soyayyen kifi a gabar teku na sayar da shi da matukar tsada.
Masunta a tekun Dunga, kamar Denis Morio ya dora alhakin tsadar kifin ga masu hannu da shuni.
Ya kara da cewa ida aka fito da tsarin samar da injinan da manyan sundunan kankare kifi za su taimaka wajen rage tsadar da safarar shi zuwa wasu kasashen.
Birnin Kisumu ya yi fice wajen samar da auduga, har masana’anta guda ake da ita ta Kicomi da ke harkar, da kuma kamfanin yin sikari mai suna Miwani.
Sai dai kamfanonin sun durkushe sakamakon rashin shugabanci na gari, dubun dubatar mutane sun rasa ayyukansu.
Unguwar Obunga ta matalauta, da ke kewayen inda kamfanin auduga na Kicoma ya ke ba ta da kyawun gani, gidajen da ke yankin an yi su ne da kwano, wasu kuma na kasa ne. Wannan shi ne matsugunin ma’aikatan kamfanonin.
Isaiah Onyango, mai shekara 58, ya tuna lokacin da masana’antar audugar ke da lokutan aiki uku.
"Kasuwancin bada hayar gidaje na kara bunkasa. Matasa na samun ayyukan yi da zarar sun kammala karatu," in ji shi, a lokacin da yake mana bayanin fatan da yake da shi idan Mista Odinga ya zama shugaban kasa.
Da kyakkyawan zaton darajar Kisumu za ta karu, bayan abinda ya kira gwamman shekarun da akai watsi da al’ummar yankin.
Evelyne Musambi za ta kai ziyara mahaifar William Ruto, rahoton zai zo muku ranar Juma’a. Kar ku bari a ba ku labari.