Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kenyatta, Ruto da Odinga: Yadda auren siyasa ya mutu tsakanin shugaban Kenya da mataimakinsa
A cikin jerin wasiƙun da 'yan jaridar Afirka ke aiko mana, ƙwararre kan harkokin sadarwa Joseph Warungu ya yi duba game da mutuwar auren siyasa tsakanin shugaban Kenya da mataimakinsa, har ma da mutum na uku a alaƙar tasu mai sarƙaƙiya.
Kamar ko waɗanne ma'aurata a ranar ɗaurin aurensu, Shugaba Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William Ruto na cike da murmushi a lokacin da suka hau kan dandalin shan rantsuwa.
A ranar 9 ga watan Maris na 2013 ne aka bayyana su a matsayin waɗanda suka lashe zaɓen shugaban ƙasa.
Auren nasu a siyasance ya kasance mai kyau bayan Kotun Laifukan Yaƙi ta Duniya International Criminal Court (ICC) ta yi yunƙurin hukunta su - wanda bai yi nasara ba - kan rikicin bayan zaɓe na 2007.
Ma'aurata na zamani
Soyayya na tsaka da daɗi a wancan lokacin.
Sukan fito kafaɗa da kafaɗa, wani lokaci ma sukan saka kaya iri ɗaya.
Sukan yi addu'a tare a bainar jama'a kuma su yi raha da yawa. Sauran jama'a kan yi dariya tare da su.
Kenyatta na da shekara 51 a lokacin da ya hau mulki, yayin da Ruto ke da shekara 47.
Mutumin da suka kayar a zaɓen, tsohon Firaministan Raila Odinga, yana da shekara 68, wanda aka kalla a matsayin "tsoho" wanda ba na zamani ba - saɓanin Kenyatta da Ruto da ake wa laƙabi da na zamani wato digital a Turance.
Bayan shekara takwas da kuma zaɓen shugaban ƙasa sau biyu, auren ya mutu kuma mu 'ya'yansu, 'yan ƙasar Kenya, mun rasa abin yi.
Musabahar da ta sauya tsarin siyasa
Alamar mutuwar auren ta farko ta faru a Maris na 2018 lokacin da shugaban ƙasa ya gabatar da tsohon abokin adawarsa, Mista Odinga, a matsayin mutum na uku a auren nasu.
Da ma can Odinga ya sha shirya zanga-zangar cewa an yi maguɗi a zaɓen tare da abokan siyasarsa a jam'iyyar haɗaka ta National Super Alliance (Nasa) tare da mutum uku.
Kenyatta ya miƙa wa Odinga goron gayyata ne bayan ya yi tunanin cewa zanga-zangar ka iya gurgunta yunƙurinsa na aiwatar da alƙwuran da ya yi a lokacin kamfe.
Mutanen biyu sun gaisa a bainar jama'a domin bayyana ƙawancensu a hukumance.
Sannu a hankali Mista Ruto ya fara janye jiki daga abokinsa na tsawon shekara biyar.
A kwanan nan, rigimar da ke tsakanin ma'auratan na fitowa fili. Ba sa son haɗuwa sannan alamun da ke fuskarsu na nuni da lalacewar alaƙa ko kuma mutuwar aurensu.
Ruto ya ƙi fita daga gidan aure
Yayin bikin 1 ga watan Yuni na Ranar 'Yancin Kai, Kenyatta ya bayyana cewa ya gabatar da ayyukan raya ƙasa a zamanin da yake ƙawance da Odinga fiye da yadda ya yi da Ruto.
Sai dai Mista Ruto ya ƙi yarda ya sauka daga mulki - ko kuma ya ƙi fita daga gidan aurensu. Ya shafe lokaci mai tsawo a ɗakin saukar baƙi yana ƙorafi ga duk wanda ya saurare shi cewa an yi watsi da shi duk da irin taimakon da ya bai wa Kenyatta wajen gina fadarsa.
A lokacin da mutanen biyu suka haɗa gwiwa, sun ƙulla yarjejeniya ta tsawon shekara 20, wadda Ruto zai goyi bayan Kenyatta wajen kammala wa'adin mulki na shekara biyar sau biyu.
Bayan haka, Kenyatta zai goyi bayan mataimakinsa ya zama shugaban ƙasa a 2022, inda shi ma zai yi wa'adi biyu.
Sai dai a Janairun 2021, shugaban ya kawo ƙarshen yarjejeniyar ƙarara.
"Shugabancin ƙasa ba na ƙabila biyu ba ne kaɗai," a cewar shugaban yayin wani taro, yana mai cewa da alama lokaci ya yi wata ƙabila daga cikin 42 na Kenya ta hau mulki.
Shugaban ya ce ƙabilu biyu ne suka mamaye kujerar a tsakaninsu - Kikuyu da Kalenjin.
Kenyatta ɗan ƙabilar Kikuyu ne, Ruto ɗan Kalenjin ne, yayin da Odinga ya fito daga Luo waɗanda da ma sun daɗe suna kuka kan ware su daga shugabanci.
Kenya ta talauce
Mista Ruto bai yarda cewa ƙabilar Kalenjin ba za ta sake yin mulki ba, ko kuma a ce ba zai iya sake haɗa gwiwa da wani daga Kikuyu ba.
Ya sha zuwa yankin tsakiyar ƙasar domin ƙoƙarin samun goyon bayan wani ɗan Kikuyu.
Mu kuma 'yan ƙasa mun rasa yadda za mu yi.
Shin za mu ci gaba da zama da ubanmu ne wanda zai yi ritaya daga shugabancin ƙasa a shekara mai zuwa?
Shin za mu karɓi sabon abokin zamansa Mista Odinga ne wanda ya yi alƙawarin zaman lafiya da daidaitacciyar al'umma, sannan kuma yake yawan yin waƙa a kan dandalin kamfe?
Ko kuwa za mu bi Ruto ne - tsohon abokin zamansa wanda ke da tsaurin ido wanda ya yi wa talakawa alƙawarin kyautata rayuwarsu?
Farashi ko sadaukarwar da 'yan ƙasa suka yi mai tsada ce sosai. Ƙasar ta talauce.