Me ya sa allon nuna hanya ya haifar da rigima a Kenya?

    • Marubuci, Daga Emmanuel Onyango
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Nairobi
  • Lokacin karatu: Minti 3

Rikici ya ɓarke a Nairobi babban birnin Kenya, bayan da aka sauya wa wata hanya suna da sunan shugaban haɗakar ƙungiyar ƙwadago ta Kenya Francis Atwoli.

Tun bayan saka sunan ne waɗanda abin bai yi wa daɗi ba suka cire alamar, kuma bayan mayar da ita suka ƙara cire wa tare da ƙona ta.

A baya sunan hanyar 'Dik Dik', da ke kanyar kasuwar Kileleshwa kafin aka sauya mata suna zuwa 'Francis Atwoli' watan da ya gabata.

Tarihi ya nuna cewa ba a taɓa samun saɓani ba kan rikicin saka wa hanya suna ba a Kenya kamar a wannan karon.

Masu sukar matakin sun ce Mr Atwoli bai cancanci irin wannan karramawa ba, don a tsawon shekaru 20 da ya yi yana jagorantar ƙungiyoyin ƙwadago babu wani abun azo a gani da ya attaka musu.

Bugu da ƙari sun ce ba a bi ƙa'ida wurin sauya sunan hanyar.

To amma ko a wannan makon magoya bayansa sun sake kafa wani allo dauke da sunansa.

Yanzu dai wasu mazauna Nairobi sun kai maganar kotu.

'Sunana ba zai taɓa gushewa ba a Kenya'

Mr Atwoli da kansa ya yi allah wadai da matakin farfasa allon da ke ɗauke da sunansa.

Ya bayyana hakan da aikin mahassada, inda ya ce "sunana ya riga ya shiga duniya, kuma bana buƙatar sai an kafa allo ɗauke da sunana kafin wani yasan wanene 'Francis Atwoli'

''Lura da yadda na kafa tarihi wurin inganta rayuwar ma'aikata a Kenya da ma daukacin al'ummar duniya, sunana ba zai taɓa gushewa ba''. In ji Mr Atwoli.

Ya ƙara da cewa idan da son samun shi ne zai zaɓi hanyar da ta fi dacewa da matsayin shi.

''Kwata kwata abin bai ɓata mini rai ba don ban buƙaci a saka sunana a kan kowace hanya ba. Kuma da ace ni za a bai wa dama da zan zabi hanya mai girma da muhimmanci ne,'' kamar yadda ya faɗa wa gidan talabijin na NTV.

Shi ma gwamnan riƙo na Nairobi Ann Kanunu ya ce ya kasa fahimtar me ya sa wasu ke adawa da ba wata hanya sunan Mr Atwoli, lura da irin namijin ƙoƙarinsa da ƙaunar da ya ke yi wa Kenya.

Amma an lura a baya bayannan dattijon mai shekaru 72 na nuna goyon baya ga shirin Shugaba Uhuru Kenyatta na kawo sauye-sauye ga kundin tsarin mulki wanda ya kira Building Bridges Initiative (BBI).

Shirin BBI ya tsara faɗaɗa ɓangaren zartarwa na gwamnati, amma tuni wasu sun nuna adawa da shirin, kuma a watan da ya gabata kotu ta dakatar da shi duk da bangaren gwamnati ya ɗaukaka ƙara.

Lamarin ya dauki wani sabon salo a shafukan sada zumunta musamman Twitter a Kenya.

Wasu ma sun nuna yadda ya kamata a riƙa saka sunan hanya ta yadda babu wanda zai iya tumɓuke shi.

Sai dai ga alama da wahala dambarwar ta mutu nan kusa, lura da cewa masu fafutuka na shirin gudanar da zanga zanga kan saka sunan Mr Francis Atwoli a kan hanya.

''Ba zamu taɓa bari a riƙa yi mana yadda ake so ba, kuma za mu ci gaba sai inda karfinmu ya ƙare,'' inji Boniface Mwangi, wani mai fafutukar ganin an mayar da sunan tsohuwar hanyar da aka sauya da sunan Francis Atwoli.