Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kenya : Matar da ta zamewa masu aikata laifi a Kenya ƙadangaren bakin tulu
Harkar binciken tsaro na masu zaman kansu a Kenya, ɗaya ne daga cikin mafi girma a Afirka, saboda yadda jama'a ke karbar ta hannu bibbiyu.
Da matuƙar rashin yardar da aka yi wa ƴan sandan ƙasar, mutane da dama na komawa ga jami'an bincike masu zaman kansu domin samun adalci.
Ƙwararru na ƙiyasin cewa harkar da ke lulluɓe cikin sirri, ta kai darajar miliyoyin dalar Amurka. Sai dai ba tare da ƙa'idajjen horo da tsari ba, wasu na fargabar cewa waɗannan jami'an leƙen asirin ɓoye, na yin gaban kansu.
A Kenya, akwai matuƙar rashin yarda da 'yan sanda abin da ya sa, wasu mutane ke komawa ga jami'an bincike masu zaman kansu don samun adalci.
Jane Mugo, na ɗaya daga cikinsu. Ita mai wani kamfanin jami'an tsaro ne mai zaman kansa da ya fi shahara a Kenya, doguwar mace ce mai jiki da tsayi.
Mutum ce mai jawo ka-ce-na-ce wadda hanyoyin da take amfani da su ke jawo mata arangama da doka ciki har da zarge-zargen zare ido wajen tatsar bayanai.
Sashen Binciken Manyan Laifuka ya sa sunan jami'ar binciken mai zaman kanta, Jane Mugo cikin jerin ɓata gari da ake nema ruwa a jallo.
'Yan sanda sun ce Jane Wawira Mugo da ke yi wa kanta laƙabin jami'ar bincike mai zaman kanta, tsohuwar mai laifi ce da a yanzu ke gudun ɓuya, kuma an ba da sammacin kama ta.
Tuni dai aka yi watsi da tuhume-tuhumen da ake yi wa Jane waɗanda ita ma ta yi iƙirarin cewa wani bi ta da-ƙulli ne kawai.
''Mutanen da ke muguwar magana a kaina, iri uku ne: ko dai ɓata garin da na taɓa bincika ne, ko waɗanda ake zargi sun aikata laifi kuma suke can suna ƙarewa a gidan yari ko kuma 'yan sanda masu cin hanci da ke tunanin cewa Jane Mugo barazana ce a gare su.
Mutanen da ke zuwa wurin ta na neman bayanai a kan abokan zaman aure masu cin amana, ko wasu kayan sata sai kuma daga lokaci zuwa lokaci miyagun laifuka. Jimilla dai, ta yi ƙiyasin jami'anta sun warware batutuwa fiye da 300, inda ta yi sanadin ɗaure ɓata gari 70 a gidan yari.
''Ina son aikina. Ina ƙaunar adalci, a cikinsa ma aka haife ni. A cikin jinina yake. Yaƙi don tabbatar da adalci ba? A cikina yake'' inji Jane.
Jane Mugo ta ɗauki masu bincike 10 aiki ciki har da tsoffin jami'an 'yan sanda da sojoji, ta ce ta ga wasu daga cikinsu ne lokacin da suke atisaye ciki har da gwajin danna mutum a ruwa da kuma shauɗa bulalai don gwada jarumtakarsu.
Charlie, wani tsohon soja kuma na hannun daman Jane, ya ce suna amfani da irin waɗannan dabarun ne lokacin titsiye ɓata gari
''Babu cutarwa wajen yin amfani da ɗan ƙarfi don tatsar bayanan da za su taimaka a kuɓutar da rayuka. Ko da yake, yarjejeniyar Geneva ta hana azabtarwa amma mu namu ba azabtarwa ba ne.
An bai wa jami'an bincike kamar Jane damar ɗaukar makamai masu lasisi kuma ana ƙara shigar da su cikin samamen 'yan sanda.
Jami'anta a kai a kai suna yi wa manyan 'yan siyasa aiki, wani abu da ke ba su wata kariyar siyasa.
Masu suka sun ce hakan ya sa sun zama shafaffu da mai.