Ƙasar Kenya: Bishiyar ɓaure mai shekara 100 da ta fi ƙarfin shugaban ƙasa

Daga cikin jerin wasiƙun da muke wallafawa na 'yan jarida daga Nahiyar Afirka, masanin harkar sadarwa Joseph Warungu ya duba mana yadda bishiyoyi ke da tasiri fiye da 'yan siyasa a ƙasar Kenya.

Ba kodayaushe gwamnatoci ke sauraron koken al'umma ba.

Da a ce suna ji, da babban birnin Uganda, Kampala, bai kaure da rikici ba a kwanan nan sakamakon daƙile yunƙurin 'yan ƙasar da gwamnati ta yi ba saboda suna neman sauyi yayin da ake yunƙurin gudanaar da zaɓe.

A Kenya, mutane na roƙon gwamnati da 'yan siyasa su taimaka wurin kawo ƙarshen annobar cutar korona ta hanyar daina shirya taron yaƙin neman zaɓe game da neman ƙuri'ar mutane kan gyaran kundin tsarin mulki.

Idan zaɓen raba-gardamar ya gudana kuma mutane suka amince da shi, za a samar da babban sauyi a kundin tsarin mulki, wanda zai sake fasalin gwamnati sannan a ƙirƙiri sabbin ofisoshin siyasa, ciki har da yawan 'yan majalisa - dukkaninsu da kuɗin talakawa za a biya su.

Sai dai 'yan siyasar jam'iyya mai mulki da 'yan adawa ba su saurari al'umma ba, inda suka ci gaba da tarukansu da tarin jama'a, ciki har da waɗanda ba su damu da saka takunkumi ba.

Fargabar da ake da ita ta ƙaruwar kamuwa da kuma mace-macen da ake a yanzu sama da farkon sanda cutar korona ta ɓarke, su ne suka sa ake wannan kiraye-kirayen.

Saboda haka, abin ya zo wa mutane da mamaki lokacin da wata bishiya ta yi magana kuma gwamnati ta saurara.

Sai dai fa ba bishiyar gama-gari ba ce.

Shirgegiyar bishiyar mai shekara 100 wadda ta mamaye wani yanki na Waiyaki Way da ke yammacin birnin Nairobi, an yanke shawarar tumɓuke ta ne domin gina wani titi mai hannu biyu.

Titin mai tsawon kilomita 27 zai haɗa babban filin jirgin sama na Jomo Kenyatta da yankin Westlands na Nairobi sannan ya haɗe da Waiyaki Way, babbar hanyar da ta haɗa Kenya da Uganda.

'Ƙashin bayan al'ada'

Babu wanda ya san dalilin da ya sa shugaban ƙasar ya sauya ra'ayi tare da bayar da umarnin a ƙyale bishiyar.

Ya siffanta bishiyar da "al'ada da kuma mahalli a Kenya".

Tabbas, bishiyar na da muhimmanci a al'adance da addinance ga al'ummar Bantu.

Wasu al'ummar da ke yankin Luhya na yammacin Kenya, kamar Maragoli, suna ganin girman "mukumu" ko kuma bishiyar ɓaure. A al'adance, dattawa na amfani da inuwarta a matsayin kotun shari'a. Kazalika, ana girmama bishiyoyin ɓaure a yankin Maragoliland.

Alamun miƙa mulki

A wurin al'ummar Kikuyu na Kenya, waɗanda suka fi kowa yawan al'umma a ƙasar, an mayar da bishiyar wadda aka fi sani da "mugumo" wata kushewa, wurin ibada da yin ayyukan sadaukarwa.

Al'ummar Kikuyu ba sa bari a sare ɓaure saboda sun yi imanin cewa sare shi zai iya haifar da wani bala'i.

Duk sanda wata bishiriyar ɓaure ta faɗi ƙasa, al'ummar Kikuyu na kallon hakan a matsayin wata alama ta sauyin iko daga wani ƙarni na gargajiya zuwa na gaba. Kowane ƙarni kan rayu kusan shekara 30.

Shugaba Uhuru Kenyatta, wanda shi ma Kikuyu ne, babu mamaki wani abin da ba a so ne zai same shi a harkar siyasarsa, amma ba ni da tabbas ko shi ma yana riƙo da wannan al'adar ta matacciyar bishiyar ɓaure.

Yayin da masana mahalli ke kiran a daina sare bishiyoyi, su kuwa masu riƙo da ala'adar Kikuyu na jiran ganin an kyautata al'adarsu.

Ba wannan ne karon farko ba da aka tilasta wa gwamnati dakatar da ita daga taɓa mahalli.

A shekarun 1980 - sanda jam'iyyar African National Union ke mulki - ta tsara gina wani katafaren gini a matsayin hedikwatarta a wurin shaƙatawa na Uhuru Park da ke birnin Nairobi.

An tsara cewa ginin Times Media Complex zai zama mafi tsayi a yankin Gabashin Afirka baki ɗaya, inda za a samar da hawa 60 da babban kantin sayar da kayayyaki da wurin ajiye ɗaruruwan motoci.

Masu fafutikar kare mahalli ƙarƙashin jagorancin Farfesa Wangari Maathai sun ƙaddamar da wani kamfe domin ceton wurin shaƙatawar.

A ƙarshe dai, Daniel arap Moi wanda shi ne shugaban ƙasa, ya saurare su kuma ya ƙyale wurin.

Lamarin ya bai wa 'yan China mamaki

Yanzu bishiyar ɓaure ta Waiyaki Way za ta ci gaba da shaƙar bishiyar 'yanci tun da an fasa sare ta.

Lokacin da na ziyarci wurin a makon nan, ma'aikatan har sun zana yadda za su haƙa ramuka a wurin.

Wani direban tasi ya faɗa mani cewa: "Bayan shugaban ƙasa ya bayar da umarnin, wani ɗan kwangilar China ya zo ya kalli hanyar ƙasa da ya kamata ta ratsa ta cikin bishiyar sannan ya wuce yana girgiza kai."

'Yan China za su yi mamakin irin tasirin da wannan bishiya ke da shi.