Me ya sa ake samun ƙaruwar rikici tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa?

Asalin hoton, Getty Images
An samu ruruwar rikici tsakanin Isra'ila da Palasɗinu tun farkon wannan shekarar inda mutane da dama suka mutu a duka ɓangarorin musmman Falasdinawa. Ga ƙarin bayani game da abin da ke wakana.
Me ke faruwa?
Ana gwabza rikicin na yanzu ne a Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma Gabashin Ƙudus - yankunan da Isra'ila ta mamaye tun yaƙin Gabas ta Tsakiya a 1967.
Rikicin ya soma ta'azzara a Maris ɗin 2022. Cikin ƴan kwanaki, Isra'ila ta fuskanci munanan hare-hare daga Falasɗinu inda sojojin Isra'ila suka ƙaddamar da samame a yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan lamarin da ya haifar da samame cikin dare a yankunan da aka mamaye.
Ya yaƙin ya munana?
An samu mutane da dama da suka mutu ko suka jikkata sakamakon samamen na Isra'ila da hare-haren Falasɗinu cikin shekarar da ta gabata.
Amma abin da ke nuna irin tashin hankalin da aka yi shi ne yawan mutanen da suka rasa rayukansu da hare-haren da aka kai har aka kashe mutane musamman Falasdinawa.
A bara, kimanin Falasɗinawa 146 - ƴan tawaye da farar hula da mahara - sojojin Isra'ila suka kashe a Gabar Yamma da kuma gabashin Ƙudus - fiye da kowane lokaci tun ƙididdigar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta soma a 2005.
A gefe guda kuma, an kashe ƴan Isra'ila 29 da wasu baƙi biyu - dukkansu amma huɗu a cikinsu farar hula - a farmakin da Falasɗinawa suka kai ko Larabawan Isra'ila.
Wannan ce shekara mafi muni ga ƴan Isra'ila tun 2015.
Tun a wata na biyu na bana, adadin mutanen da suka mutu - Falasɗinawa 60 da mutum 14 a ɓangaren Isra'ila - ya ɗara mace-macen da aka samu a irin wannan lokacin a 2022 sanadin wasu munanan hare-hare da aka kai cikin shekaru.
A wani samame da sojojin Isra'ila suka yi a Nablus a Fabarairu, Falasɗinawa 11 aka kashe a tashin hankalin inda gomman mutane suka ji rauni sakamakon harbin bindiga, a cewar ma'aikatar lafiya ta Falasɗinu.
A wani samamen da musayar wuta a Jenin a watan da ya gabata, Falasɗinawa 10 ne aka kashe.
Ƴan Isra'ila sun fuskanci munanan hare-hare: farar hula bakwai aka harbe a wajen Gabashin Ƙudus a watan Janairu.
Yayin da a wani harin kuma cikin watan Fabarairu, aka kashe mutane uku a wata tashar mota da ke wajen birnin.
Me ke janyo artabun?
Duka ɓangarorin na zargin juna amma akwai wasu dalilai da suka daɗe da haifar da rikicin.
Maharan Falasɗinu da masu mara musu baya sun ce suna yaƙar Isra'ila da kuma mamayen da ta yi musu inda kuma suke mayar da martani kan Isra'ila.
Wasu daga cikin hare-haren wasu ƴan-ba-ruwana ne da ba sa ƙarƙashin wata ƙungiya suka kai su.
Isra'ila ta zargi hukumar Falasɗinu da ke Gabar Yamma da kitsa hare-haren.
Sauran hare-haren ƴan tawayen Falasɗinu ne ciki har da sabuwar ƙungiyar Lions' Den da tasirinta ya ƙaru a tsakanin Falasɗinawa ke kaiwa
Isra'ila ta ce samamen da take yi a Gaɓar Yamma tana kaiwa ne kan ƙungiyoyin ƴan tawaye inda ake kamensu domin hana su kai hare-hare.
Ana kai samamen ne a yankunan da ke sansanin ƴan gudun hijra da wasu birane inda suke fuskantar turjiya daga ƴan bindiga da a mafi yawan lokuta ke kai wa ga zubar da jini.
Akwai alamun za a tsagaita rikicin?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ba a nan kusa ba. Isra'ila ta ce ta ci gaba da samamenta domin murƙushe ƙungiyoyin ƴan tawaye tare da daƙile hare-hare yayin da Falasɗinawa ke cewa hare-haren martani ne ga matakan Isra'ila da kuma sojoji masu ƙarfi.
Sannan kuma babu wani shirin zaman lafiya na siyasa da zai iya kaiwa ga maslaha ta din-din-din - Falasɗinawa na neman a ba su ƙasa ta kansu, ita kuwa Isra'ila na neman zama babbar jami'ar tsaro a tsakaninsu.
Ana ganain ci gaba da faɗaɗa matsugunan Yahudawa a yankunan da Falasdinawa ke son kafa ƙasarsu a nan gaba shi ne tushen daɗaɗɗen rikicinsu da Isra'ila.
Ana ganin samar da matsugunan sun saɓa da doka a ƙarƙashin dokar ƙasa da ƙasa duk da cewa Isra'ila ta musanta haka.
Akwai ɗan fatan samun nasara a tattaunawar da Amurka ke jagoranta wadda Isra'ila da Falasɗinawa suka yi gaba da gaba a taro irinsa na farko tsawon shekaru.
An yi wannan ganawa mai tarihi a Jordan ranar Lahadi a wani yunƙuri na kawar da tashin hankali da nufin cimma matsaya don ganin ɓangarorin biyu sun sake haɗuwa a watan Maris.










