Yadda kawance tsakanin matan Isra'ila da na kasashen Larabawa ke burge jama'a

Fleur Hassan-Nahoum

Asalin hoton, Fleur Hassan-Nahoum

Bayanan hoto, Fleur Hassan-Nahoum ta bayyana yadda haduwarsu ta farko a wani taro da ta shirya ya kasance mafarin kawance a matsayin ‘yan uwan juna

Fleur Hassan-Nahoum, mataimakiyar magajin birnin Kudus a Isra'ila, ta bayyana taron farko da suka gudanar na kungiyar da take cikin wadanda suka kafa a matsayin "somin-tabi na 'yan uwantaka."

Sun kafa kungiyar ce ta matan yankin Gulf da Isra’ila.

A shekara ta 2020 aka soma irin wannan taro, bayan cimma yarjejeniyar tarihi tsakanin Isra’ila da Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain.

Wannan yarjejeniya ta sanya sun kasance kasashen yankin Gulf na farko da ke daidaita alakarsu da Isra’ila da kawo karshen kauracewa kasar na tsawon shekaru.

Yarjejeniya ce da aka sanya hannu a watan Satumban 2020 a fadar White House, sannan wata guda bayan haka aka gudanar da taron tattaunawa na mata karkashin jagoranci Ms Hassan-Nahoum a birnin Dubai.

mata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yarjejeniyar da ake kira ta Abraham an sanya hannu a kanta shekaru biyu da suka gabata

Yarjejeniyar da ake kira ta Abraham an sanya hannu a kanta shekaru biyu da suka gabata a wani taro da aka gudanar a fadar gwamnatin Amurka ta White House.

Wannan kusan wani mataki ne da aka dauka domin bai wa mata Isra’ila da sauran hamshakan mata ‘yan kasuwa a yankin Gulf damar hadu su tattauna kan cigabarsu ta fuskar kasuwanci da kawance.

Ms Hassan-Nahoum, wadda kuma ke jagorantar wani kamfanin harkokin yada labarai kuma kwararriyar lauya, ta ce ana da yakinin cewa mata jagorori ne nagari da kuma ke taimakawa wajen habbaka sana’o’i da masana’antu.

Ta ce tana da yakini cewa dama komai zai tafi daidai tun kafin ganawarsu.

“Duk da cewa ina da dan shaku, yana da muhimmanci a ce mun taka rawa wajen tabbatuwar zaman lafiya da cigaban nahiyarmu.

“Sabanin abin da wasu ke tunani, mu ba makiyan juna ba ne. Idan akwai wani abu na tsokaci ma shi ne kamanceceniya da matan Isra’ila da Gulf ke da shi.

Dukkaninmu mun fito daga dakin taro cike da annashuwa.

 Yanzu wannan kungiya na da daruruwan mambobi daga bangarori daban-daban na kwarewa a rayuwa, ciki har da matan da suka fito daga yankunan da ba sa cikin yarjejeniyar Abraham, irin su Saudiyya da Masar.

Har yanzu babu kyakkyawar alakar diflomasiyya tsakanin Saudiyya da Isra’ila, yayin da Masar ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninta da Isra’ila a 1979, sai dai ita ba ta cikin kasashen Gulf.

Gulf-Israel Women's Forum

Asalin hoton, Gulf-Israel Women's Forum

Bayanan hoto, Kungiyar na taro akai-akai a shekara, wani lokaci ana haduwa ko kuma a yi taron ta intanet.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Matan na haduwa a kalla sau takwas a shekara, ko a zahiri ko ta bidiyo.

Mai sharhi kan harkokin siyasa a Bahrain, kuma tsohuwar shugabar kungiyar lauyoyi ta Bahrain, Ahdeye Ahmed Al.-Sayed, na cikin matan da ke wannan kungiya.

Ta ce yayin da kungiyar ke kokari wajen sake gina sabbin alaka, har yanzu akwai jan aiki wajen daidaita alakar gaskiya tsakanin Isra’ila da yankin Gulf.

“Ko da alakar ta shafi siyasa da tsaro da soji da batun tattalin ariki da zuba jari da batun abinci, abin da muke bukata baki daya shi ne sabuwar alaka da za ta taimaka wajen inganta mana harkoki domin fuskantar manyan kalubale,” a cewarta.

"Wannan ita ce ma’anar alakar Isra’ila da Bahrain.”

Ta kuma bayyana cewa lokacin da ta soma nuna goyon baya kan yarjejeniyar Abraham, ta "fuskanci kiyayya da tsana, barazana da tsangwama a shafukan sada zumunta.”

“Wannan ya nuna cewa mata a ko da yaushe na da muhimmanci, kuma duk mai kalubalantarsu zai yi kokarin karya lagonsu ta kowanne hanya.

Amma a nawa labarin hakan ya karfafa mun gwiwa.”

Ahdeya Amed Al-Sayed daga hannu tare da Fleur Hassan-Nahoum ta ce ta sha suka saboda ra’ayinta

Asalin hoton, Fleur Hassan-Nahoum

Bayanan hoto, Ahdeya Amed Al-Sayed daga hannu tare da Fleur Hassan-Nahoum ta ce ta sha suka saboda ra’ayinta

Ga Hadaddiyar Daular Larabawa, a cewar wata kwararriya a Amurka, Leah Tedrow, abu guda da wannan kungiya ke taimakawa da shi, shi ne mata Isra’ila ‘yan kasuwa na koyon sabbin dabarun harkokin kasuwanci da kula kyawawan sabbin alaka da kasashen Gulf.

“Samun sabbin hanyoyi kasuwanci a matsayinki na wanda harkokin na cikin gida ne na da muhimmanci sosai, domin tabbatar da cewa baki fada cikin matsalar da babu mamaki fita tayi wahala,” a cewar Ms Tedrow, shugabar wani kamfanin harkokin sadarwa da ke Dubai, Evoke.

Ms Tedrow ta ce idan ke sabuwa ce a harkokin kasuwanci a Hadaddiyar Daular Larabawa dole ki dauki lokaci wajen gina yarda a zukatan mutane, kuma ba karamin aiki ba ne.

“Duk wanda ke tunanin yana iya zuwa Dubai kawai ya cimma yarjejeniya kai-tsaye ya cire wannan zaton.

Leah Tedrow

Asalin hoton, Leah Tedrow

Bayanan hoto, Leah Tedrow

Ms Tedrow kusan ita ce ta gaba-gaba wajen tattaunawa ta fuskar siyasa tsakanin Isra’ila da UAE da shugabannin ‘yan kasuwa kafin yarjejeniyar Abraham.

Ta bayyana yadda ta saurari tattaunawar farko ta waya kan wannan matsayi da ake kai yanzu.

Yayin da wannan kungiya na matan Isra’ila da Guld ke kara karfi, wani bincike ya yi hasashen cewa kasuwaci tsakanin Isra’ila da UAE za ta kai dala biliyan biyu da rabi a wannan shekara, sannan zai karu zuwa dala biliyan biyar kafin 2027.

Kasahen biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci mara shinge a watan Maris.

Isra’ila da Bahrain na cigaba da tattaunawa domin cimma irin wannan yarjejeniya a tsakaninsu. Sai dai yayin da wadannan kasashe na yankin Gulf da Isra’ila ke inganta alakarsu, wata ‘yar kasuwa a Falasdinu, Maha AbuShusheh ta ce an bar su a baya.

Maha AbuShusheh ta ce ita da sauran matan Falasdinu ‘yan kasuwa a bar su a baya.

Asalin hoton, Maha AbuShusheh

Bayanan hoto, Maha AbuShusheh ta ce ita da sauran matan Falasdinu ‘yan kasuwa a bar su a baya.

“Sai nake ganin kamar a sa mu a gefe da sauran harkokin kasuwancin mata Falasdinu, kasashen Larabawa kamar suna ware mu indai aka zo batun kasuwanci,” a cewar shugabar kamfanin gine-gine da ke Ramallah.

“Akwai matukar wahala iya kasuwanci da su saboda ba mu da tsarin kasuwanci budaddiya da sauran kasashen duniya, tattalin arzikinmu na shan wahala saboda dalilai da dama, irin su rashin tabbas da rashin iya kula da iyakokinsu da albarkatu.

“Babu shaka mu ‘yan uwa ne kuma kawaye da sauran kasahen Larabawa…Amma kasuwanci tsakaninmu abu ne mai wahala, da yarjejeniya ko babu yarjejeniya.

Rayuwarmu babu sauki tabbas kuma ba zan iya bayyana abu guda na alheri da muke samu ba.