Isra'ila ta tsaya da gine-gine a yankunan Falasɗinawa da ta mamaye

Asalin hoton, Getty Images
Isra'ila ta sanar cewa za ta dakatar da fadada gine-ginen da take yi a yankunan da ta mamaye na Falasdinawa da ke rayuwa a Gabar Yamma da Kogin Jordan "na wasu watanni masu zuwa".
Da alama wannan wata riba ce da ake samu sanadin tattaunawar da Amurka ke yi da jami'an gwamnatin Isra'ila da na Falasdinu.
An dauki wannan mataki ne bayan da ake sukar jami'an Falasdinu saboda amincewar da suka yi a janye wani kudurin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar kan matsugunan da Isra'ilar ke ginawa.
A madadin haka, sai kwamitin tsaron ya fitar da wata sanarwa da ke bayyana "damuwarmu da jimaminmu" kan abubuwan da suke aukuwa.
A makon jiya, Isra'ila ta sanar da amincewar gwamnatinta ta tsarawa da gina sababbin gidaje kusan 10,000 a yankunan da ta mamaye.
Ba a sa ran za a sauya wadannan matakan ba.
Tun farko Amurka ta gargadi Isra'ila, wadda ita ce ta fi samun alaƙar ƙut-da-ƙut da ita a yankin Gabas ta Tsakiya, cewa ta guji gina sababbin gidaje.
A ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa, yin gine-ginen ya kasance laifi ne, duk da yake Isra'ila ta musanta haka.
Ƙungiyar nan ta Palestine Liberation Organisation (PLO), wadda ke wakiltar Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya ba ta ce uffan ba a hukumance kan wannan matakin.
Ita ma gwamnatin Falasdinu da Shugaba Mahmoud Abbas ke jagoranta ta wadda ke da iko kan wasu yankuna na yammacin kogin na Jordan ba ta ce komai ba.
A yankunan da Isra'ila ke da iko, Falasdinawa na yin gine-gine ba tare da sun nemi izini ba, suna cewa samun izinin abu ne da ba ya samuwa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ita kuwa Isra'ila na kallon wadannan gine-ginen da Falasdinawa ke yi a matsayin wadanda suka taka dokokinta kuma a baya-bayan nan ta rika rusa su, lamarin da ya ƙara tayar da hankali a yankin.
Ƙasashen duniya na bayyana damuwarsu kan matakin na Isra'ila - kuma suna hasashen za a iya samun ɓarkewar rikici tsakaninta da Falasdinawa a watannin da ke tafe.
A misali, Musulmi za su fara azumin watan Ramadan nan da wasu makonni, wanda zai zo a daidai lokacin da Yahudawa za su yi wani bikinsu na Passover a cikin watan Afrilu, domin za su yi bukukuwan ne a wuraren ibadunsu da ke da kusanci da juna a gabashin Birnin Ƙudus.
Ƙungiyar Hamas mai iko da yankin nan na Gaza, ta soki matakin na Majalisar Dinkin Dunya, tana cewa ya ci karo da abin da yancin al'ummar Falasdinu ke buƙata.
Shugaban wata jam'iyyar Falasdinawa ta Palestinian National Initiative, Mustafa Barghouti ya shaida wa BBC cewa halin da ake ciki ya yi daidai da abin da Amurka ke so.
Wasu Falasdinawa a shafukan intanet - ciki har da wani mai amfani da Twitter mai suna Yessar, wanda kuma ke bayyana kansa a matsayin likita - ya zargi jagororin Falasdinu da hada kai da Isra'ila wajen cutar da Falasdinawa.
Falasdinawa sun daɗe suna neman kafa ƙasarsu mai cikakken iko a yankunan Yamma da Kogin Jordan da Gaza, inda gabashin Birnin Ƙudus zai kasance babban birnin kasar - wadanda sune yankunan da Isra'ila ta ƙwace yayin yaƙin nan da ƙasashen Larabawa suka gwabza da Isra'ila a 1967.
Tun 1967, Isra'ila ta gina matsugnai 140 na Yahudawa a yankin yamma da kogin Jordan, tana iƙirarin addinin Yahudu ya ba ta iko kan yankunan.
Ta shafe shekaru tana rusa muhallan Falasdinawa baya ga bijire wa dukkan ƙudurorin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙaddamar da ke sukan matakin nata.










