An kashe Falasdinawa tara a harin da Isra'ila ta kai a Jenin

is

Asalin hoton, Reuters

Falasdinawa tara sun rasu ciki har da wata tsohuwa a wani hari da sojin Isra'ila suka kai a gabar yamma da kogin Jordan, kamar yadda hukumomin Falasdinawa suka bayyana.

Ministar lafiya na Falasdinawa ya yi gargadin cewa yanayin ya yi "muni" a yankin Jenin a yayin da wasu da dama suka jikkata sannan kuma motocin daukar marasa lafiya sun kasa kaiwa gare su.

A cewar ministan, a harba hayaki mai sa kwalla a bangaren kananan yara na asibitin yankin.

Dakarun Isra'ila sun fitar da bayanai 'yan kadan, amma kuma kafafen yada labarai na Isra'ila sun ce dakarun sun yi kokarin dakile wani gagarumin hari.

Kungiyar Hamas ta Falasdinawa da kuma kungiyar Islamic Jihad sun ce suna fafatawa da dakarun Isra'ila a muhimman wuraren da Isra'ila ta kaddamar da samame.

Ana zaman dar-dar a Gabar Yamma da Kogin Jordan a yayin da dakarun Isra'ila suka ci gaba da kai harin abin da suka bayyana a matsayin na dakile ayyukan 'yan ta'adda.

Kawo yanzu a wannan shekarar, dakarun Isra'ila sun kashe Falasdinawa 29 a Gabar Yamma da Kogin Jordan ciki har da 'yan tada kayar baya da kuma fararen hula.

A bara, an hallaka fiye da Falasdinawa 150 galibinsu sojojin Isra'ila ne suka kashe su, a yayin da hare-haren da Falasdinawa suka kai a Isra'ila suka janyo mutuwar mutane fiye da 30 ciki har da fararen hula da 'yan sanda da kuma sojoji.