Man United ta ɗauki sabon ɗan wasan tsakiya, Real za ta haƙura da Konate

Asalin hoton, Getty Images
Mahukuntan Real Madrid sun fara nuna shakku kan zawarcin ɗan wasan bayan Liverpool da Faransa Ibrahima Konate, mai shekara 26, wanda kwantiraginsa zai ƙare a Anfield a bazara mai zuwa. (Fichajes)
Har yanzu ɗan wasan gaban Manchester United Joshua Zirkzee yana jan hankalin Juventus da AC Milan, yayin da ita ma Como ke sha'awar ɗaukar ɗan wasan na Netherlands, mai shekara 24, a matsayin aro a watan Janairu. (ESPN)
Liverpool ta fara karkata akalarta kan ɗan wasan Crystal Palace da Faransa Maxence Lacroix, mai shekara 25, a madadin abokin wasansa, ɗan wasan baya na Ingila Marc Guehi, mai shekara 25. (Football Insider)
Manchester United ta sanya ɗan wasan tsakiya na Brentford da Ukraine Yehor Yarmolyuk mai shekara 21 a cikin jerin ƴanwasan da ta ke zawarci. (Caughtoffside)
Manchester United ta kammala cinikin ɗan wasan tsakiyar Colombia Cristian Orozco mai shekara 17 daga kulob ɗin Fortaleza na Bogota. (Fabrizio Romano)
Tottenham da Manchester United sun shiga gaban Fulham a fafatukar neman ɗauko ɗan wasan Middlesbrough ɗan ƙasar Ingila Hayden Hackney, mai shekara 23. (Teamtalk)
Newcastle na zawarcin ɗan wasan tsakiyar Athletic Club dan ƙasar Sifaniya Oihan Sancet, mai shekara 25. (Mundo Deportivo)







