Abu biyar da za a riƙa tuna tsohon shugaban INEC Mahmood Yakubu da su

Farfesa Mahmood Yakubu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Farfesa Mahmood Yakubu ya fara jagorancin INEC a watan Nuwamban 2015
    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 6

Bayan shekara 10 yana jagorantar hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta, a ranar Talata ne Farfesa Mahmood Yakubu ya ajiye aiki a hukumance bayan kammala wa'adi biyu na jagorancin hukumar.

Nan take kuma Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci May Agbamuche-Mbu ya maye gurbinsa a matsayin shugaban riƙo na hukumar ta Independent National Electoral Commission (INEC).

A ranar 21 ga watan Oktoban 2015 Tsohon Shugaban Ƙasar Marigayi Muhammadu Buhari ya naɗa Yakubu a matsayin shugaban INEC.

Shi ne ya jagoranci gudanar da manyan zaɓukan ƙasa biyu; na 2019 da 2023, da kuma zaɓukan cike gurbi masu yawa.

Baya ga nasarori, Farfesa Yakubu ya gamu da cikas iri-iri, waɗanda ke jawo shigar da ɗaruruwan ƙararraki a gaban kotu duk lokacin da aka kammala babban zaɓe.

Wannan maƙala ta duba irin abubuwan da za a fi tuna tsohon shugaban da shi, musamman sauye-sauyen da ya kawo wa INEC a lokacinsa.

Na'urar BVAS da shafin IReV

Na'urar Bvas

Asalin hoton, Inec

Wani babban sauyi da Farfesa Yakubu ya kawo wa hukumar zaɓe ta INEC shi ne yadda aka dinga amfani da na'urar Bimodal Voter Accreditation System (Bvas) wajen tantance masu kaɗa ƙuri'a a rumfunan zaɓe.

Kafin zuwansa, magabacinsa Farfesa Attahiru Jega ne ya fara ƙirƙiro na'urar Card Reader da ke tantance katunan masu kaɗa ƙuri'a.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A watan Nuwamban 2021 kuma, Farfesa Yakubu ya ƙaddamar da na'urar Bvas yayin zaɓen gwamna a jihar Anambra da ke kudancin ƙasar.

Na'urar Bvas ta zarta Card Reader a fasaha. Jam'ian INEC ka iya tantance mai kaɗa ƙuri'a ta hanyar ɗaukar hotonsa, ko kuma zanen yatsunsa.

Sai dai ta sha jawo tsaiko a wasu rumfunan zaɓe kamar yadda Card Reader ma ta dinga yi a baya.

Sai a babban zaɓe na watan Fabrairun 2023 aka fara amfani da ita a ƙasa baki ɗaya, wadda masana da dama suka ce ta taimaka wajen rage maguɗin zaɓe.

Kafin nan kuma, INEC ta ƙaddamar da shafin duba sakamakon zaɓe mai suna INEC Result Viewing (IReV) a 2020, inda aka fara amfani da shi a zaɓen cike gurbi na ɗanmajalisa a jihar Nasarawa.

A shekarar ne kuma aka yi amfani da shi a zaɓukan gwamna na jihohin Edo, da Ondo, da kuma Anambara a 2021, kafin ya zama ƙashin bayan babban zaɓe na 2023.

Shafin kan bai wa 'yan Najeriya damar ganin sakamakon ƙuri'un da suka kaɗa kai-tsaye yayin da INEC ke wallafa su bayan tattaro su daga mazaɓun ƙasar.

Ƙara yawan rumfunan zaɓe

Wata rumfar zaɓe

Asalin hoton, Inec

Adadi mai yawa na rumfunan zaɓe sun ƙaru a lokocin mulkin Yakubu, abin da ya sa rumfunan zaɓe suka ƙara matsawa kusa da al'umma, musamman a yankunan karkara.

Ya zuwa 2019, akwai rumfunan zaɓe 119,973 a faɗin Najeriya, waɗanda aka ƙirƙira kuma aka dinga amfani da su tun daga shekarar 1996.

A watan Yunin 2021 INEC ƙarƙashin jagorancin Mahmood Yakubu ta sanar da ƙarin rumfunan zaɓe 56,872, ta hanyar sauya wasu wuraren kaɗa ƙuri'a (voting points) zuwa rumfunan zaɓe (polling units).

Kazalika, hukumar zaɓen ta soke wasu rumfunan zaɓe 749 da ta ce ba su dace ba waɗanda aka kakkafa a wuraren ibada, da maƙabartu, da gidaje, da gine-ginen wasu mutane.

Sakamakon haka, jimillar adadin rumfunan zaɓe ta tashi daga 119,973 zuwa 176,846.

Bai wa nakasassu damar kaɗa ƙuri'a

Masu larura ta musamman a kan layin kaɗa ƙuri'a

Asalin hoton, Inec

Yayin jagorancinsa ne kuma INEC ta ƙaddamar da wasu matakai na tabbatar da cewa masu larura ta musamman sun samu damar kaɗa ƙuri'unsu.

Kamar yadda sabuwar Dokar Zaɓe ta 2022 ta tanada, INEC ta bai wa masu larurar gani ko nakasa damar wani mutum ya raka su tare da taimaka musu wajen kaɗa ƙuri'arsu.

Ta haka ne hukumar ta samar da allon karatu ga makafi, da fom ɗin EC40H na musamman da ake yi wa masu larura rajista, sannan kuma ta ƙirƙiri sashe na musamman domin masu laurar nakasa a ofisoshinta na jihohi da kuma Abuja babban birnin ƙasar.

A zaɓukan gwamna na jihohin Kogi da Bayelsa da Imo na watan Nuwamban 2023, INEC ta ware wa masu larura ta musamman rumfunan zaɓe 2,238 domin kaɗa ƙuri'unsu.

Sabuwar dokar zaɓe

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Asalin hoton, State House

Wani muhimmin abin tarihi da ba za a manta da shi lokacin jagorancin Farfesa Mahmood Yakubu ba shi ne fara aiki da sabuwar Dokar Zaɓe ta 2022, wadda marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya saka wa hannu ranar 24 ga watan Fabrairun 2022.

Ɗaya daga cikin sababbin abubuwan da dokar ta kawo shi ne kafa Asusun INEC, wanda ya tanadi cewa dole ne a bai wa hukumar kuɗaɗen gudanar da manyan zaɓuka aƙalla shekara ɗayakafin ranar zaɓe.

Sannan ta goyi bayan amfani da fasaha wajen gudanar da zaɓukan, da kuma sanar da sakamakon zaɓen kai-tsaye a shafin intanet mai suna Inec Result Viewing (IReV).

Haka nan, tanadin dokar da ya ce dole ne jam'iyyun siyasa su gudanar da zaɓukan fitar da gwani aƙalla kwana 180 kafin ranar zaɓe (maimakon kwana 60 a baya), ya taimaka wajen sasanta rigingimu da wuri kafin lokacin zaɓen.

Yin rajistar katin zaɓe akai-akai

Tarin katin zaɓe

Asalin hoton, Inec

Kafin Yakubu ya zama shugaban INEC, akan yi wa 'yan Najeriya rajistar katin zaɓe ne kawai idan babban zaɓe ya ƙarato.

A ƙarƙshin mulkinsa, 'yan Najeriya da suka kai shekarun kaɗa ƙuri'a kan yi rajista a duk tsawon shekara.

A watan Yunin 2021 ne hukumar ta ƙaddamar da shafin intanet na yin rajistar, inda za su iya sauyawa ko gyara sunayensu kafin daga baya a ɗauki hoton yatsunsu a ofishin hukumar.

Hakan ya taimaka wajen rage cunkoso a wuraren yin rajistar da hukumar kan ware a kowace mazaɓa da ke faɗin ƙasar.

Kalubalen da ya fuskanta

Duk da irin nasarorin da ya samu, masana na ganin akwai tarin ƙalubale da Farfesa Mahmood Yakubu ya fuskanta kuma bai yi maganinsu ba har ya bar aikin.

"Babban ƙalubalen da ya fuskanta shi ne lokacin da aka yi wa 'yan Najeriya alƙawarin yin amfani da shafin IReV a zaɓen 2023 amma kuma ba a yi ba," in ji Dr Ibrahim Baba Shatambaya malami a sashen nazarin kimiyyar siyasa na Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto.

"Wannan lamari ya sa wasu na kallon jagorancin Mahmood Yakubu a matsayin wanda ya karkata ga wasu 'yansiyasa ko wata jam'iyya a lokacin," Dr Shatambaya.

Wani ƙalubalen da masanin ya bayyana shi ne yawaitar yin zaɓukan cikamako da ake kira re-run a Turance, inda ranakun zaɓe suka shiga rana ta biyu a jihohi da dama, ko kuma a wata rana daban saboda masu kaɗa ƙuri'a ba su samu damar yin hakan ba.

Ga kuma matsalar zargin cin hanci da rashawa, kamar yadda malamin jami'ar ya bayyana.

"Akwai manyan jami'an INEC da aka zarga da karɓar cin hanci da kuma rashawa," a cewar Dr Ibrahim. "Misali, shi ne na jihar Sokoto da kuma jihar Adamawa."