Matakan da ake bi wajen naɗa shugaban INEC a Najeriya

..

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban hukumar zaɓe ta Najeriya daga 2015 zuwa 2025, Farfesa Mahmud Yakubu ya sauka daga muƙaminsa a ranar Talatar nan, inda ya miƙa ragamar jagorancin hukumar ga May Agbamuche wadda ita kwmaishinar da ta fi daɗewa a hukumar.

Farfesa Mahmdu ya fara aiki ne a matsayin shugaban INEC a ranar 9 ga watan Nuwamban 2015, bayan da tsohon shugaban ƙasar marigayi Muhammadu Buhari ya naɗa shi domin yin wa'adin shekara biyar, inda kuma bayan ƙarewar wa'adin nasa, marigayi Buhari ya sake tsawaita masa wa'adin.

Shugaban INEC ɗin wanda ya bar gado ya sanar da batun kammalar wa'adinsa da kansa a watan Afrilu lokacin wani taron shugabannin hukumomin zaɓe na ƙasashen ƙungiyar ECOWAS da aka yi a Banjul, babban birnin ƙasar Gambia.

Farfesa Mahmud Yakubu shi ne shugaban hukumar INEC mafi daɗewa a kan kujera tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokraɗiyya a 1999, inda ya gudanar da zaɓukan 2019 da 2023.

Abin da tsarin mulki ya ce kan shugaban INEC

..

Asalin hoton, Getty Images

Kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi shimfiɗa dangane da yadda ya kamata a zaɓi shugaban hukumar zaɓe ta ƙasar.

Sashe na 154 na kundin ya fayyace hanyoyin zaɓen shugaban, inda kuma ƙaramin sashe na 3 ya yi cikakken bayani kan muƙamin.

"Domin amfani da damarsa ta naɗa wani a matsayin shugaba ko kuma mamba a Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ko Majalisar Alƙalai ta Ƙasa da Hukumar da ke sa kula da da'ar alƙalai ta ƙasa ko kuma hukumar ƙidaya ta ƙasa, ya kamata Shugaban ƙasa ya tuntuɓi Majalisar Ƙasa....kuma hakan zai tabbata ne bayan sahhalewar Majalisar Dattawa."

Majalisar Ƙasa

Majalisar Ƙasa wani ɓangare ne na gwamnati da ke taka rawar bayar da shawara ga ɓangaren zartarwa wato Fadar Shugaban Ƙasa.

Majalisar ƙasar ta ƙunshi shugaban ƙasa wanda shi ne ke jagorantar majalisar da mataimakin shugaban wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar da kuma tsoffin shugabannin ƙasar da shugaban Majalisar Dattawa da shugaban Majalisar Wakilai da ministan Shari'a da kuma dukkannin gwamnonin jihohin kasar.

Wane ne ya cancanci shugabancin hukumar?

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana yawan zargin hukumar zaɓen Najeriya da gazawa wajen tabbatar da isar kayan zaɓe rumfunan zaɓe a kan lokaci.

Malam Kabiru Sufi masanin kimiyya siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a Kano wato CAS, ya ce da ma dokar mulkin soja ta 17 ta 1998 ita ce ta kafa hukumar zaɓen kuma ta faɗi mutanen da ya kamata a naɗa su shugabance ta.

"Dokar ba ta faɗi cewa lallai sai mai matakin ilimi kaza ba ko na farfesa ko makamancin wannan ba. Hasali dai kawai ta faɗi shekaru cewa shi shugaban ka da ya gaza shekara 50 da haihuwa sannan sauran mambobi kuma ka da su gaza shekaru 40 da haihuwa.

Sai dai kuma dokar ta yi maganar nagarta dangane da waɗanda za a naɗa ɗin. Wasu na ganin bisa al'ada ana naɗa farfesoshi sai ake ganin kamar haka doka ta ce amma kuma ba haka ba ne. Hasali idan aka duba wanda ya yi shugabancin hukumar da ta yi zaɓen 1999, Chief Ephraim Apata ba malamin jami'a ba ne amma tsohon alƙalin babbar kotun ƙoli ta ƙasa ne." In ji Malam Kabiru Sufi.

Me ya kamata a duba wajen naɗa shugaban?

..

Asalin hoton, Getty Images

Malam Kabiru Sufi ya ce babban abin dubawa wajen naɗa shugaban hukumar zaɓen shi ne wane ne idan aka naɗa shi al'ummar ƙasa za su samu tabbacin hukumar za ta yi adalci a lokacin aiwatar da ayyukanta?

"Tsarin ya bai wa shugaban ƙasa dama mai yawa wajen naɗin tunda shi ne shugaban Majalisar Ƙasa sannan kuma yana da iko kan Majlaisar Dattawa da za ta tantance shugaban hukumar. To kenan shugaban ƙasa ka iya naɗa mutumin da yake ganin zai tausasa masa."

Wannan ne ya sa wasu ke ganin kamar da wuya shugaban ƙasa ya yi naɗin da al'umma za su gamsu. Kuma wataƙila wannan ne ya sa wasu ke ganin idan dai har hukumar zaɓen mai zaman kanta ne to lallai bai kamata ma ace da hannun shugaban ƙasa a naɗin shugaban hukumar ba."

Mutum 4 da ka iya gadar Mahmud Yakubu

..

Asalin hoton, Getty Images

Kafafen watsa labarai na Najeriya na ta faman kama wasu sunayen mutum hudu da ake gani daga ciki ne za a samu mutumin da zai gaji kujerar Farfesa Mahmud Yakubu ta shugabancin hukumar zaɓe ta INEC. Sunayen su ne:

  • Justice Abdullahi Mohammed Liman: Ɗaya daga cikin alƙalan Kotun Ƙoli ta Najeriya.
  • Lai Olurode: Tsohon kwamishinan zaɓe na ƙasa kuma tsohon farfesa a jami'ar Legas.
  • Kenneth Ukeagu: Tsohon darekta a hukumar zaɓe ta INEC.
  • Sam Olumekun: Babban Kwamishina na labarai da ilmantar da masu zaɓe a INEC.

Shugabannin INEC daga 1999 - 2025

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Farfesa Attahiru Jega na daya daga cikin mutanen da suka shugabanci hukumar INEC a Najeriya.
  • Ephraim Akpata: 1998-1999
  • Abel Guobadia: 2000-2005
  • Maurice Iwu: 2005-2010
  • Attahiru Jega: 2010 - 2015
  • Mahmood Yakubu: 2015 - 2025