United za ta ɗauki Son, Barca na harin Diaz na Liverpool

Son Min

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United na duba yiwuwar daukar Son Heung-min, Kevin de Bruyne na daf da komawa buga MLS, Real Madrid za ta yi rige-rigen sayen Castello Lukeba da wasu kungiyoyin Premier.

Manchester United na duba yadda za ta dauki dan wasan Tottenham mai shekara 32 dan kasar Koriya ta Kudu, Son Heung-min. (Fichajes)

Sabuwar kungiyar da ke buga gasar Amurka MLS, San Diego ta kusan kulla yarjejeniyar daukar mai shekara 33 dan kasar Belgium, Kevin de Bruyne da zarar kwantiraginsa ya kare da Manchester City a karshen kakar nan. (TBR Football)

Real Madrid za ta shiga rige-rigen sayen dan wasan RB Leipzig mai shekara 22 dan kasar Faransa, Castello Lukeba, wanda Liverpool da Chelsea da kuma Manchester United ke son dauka. (Mirror)

Nottingham Forest da Newcastle United da Everton na bibiyar dan kwallon Marseille mai shekara 23 dan kasar Brazil, Luis Henrique. (TBR Football)

Juventus na sha’awar sayen dan wasan Feyenoord mai shekara 27 dan kasar Slovakia, David Hancko, wanda ke fatan komawa birnin Turin da taka leda duk da Liverpool na shirin yi masa farashi. (Tuttosport - in Italian)

Barcelona ta sa dan kwallon Liverpool mai shekara 28 dan kasar Colombia, Luis Diaz a jerin wanda za ta fara dauka a karshen kakar nan. (Diario AS - in Spanish)

Chelsea za ta sayi dan wasa, Loic Bade daga Sevilla a karshen kakar nan. A shirye take ta biya Yuro miliyan 30m (£24.9m) ga mai shekara 24. (Fichajes)