Hotunan da ke bayyana sirrin ɗabi'un duniyar rana
- Marubuci, Pallab Ghosh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Science Correspondent
- Marubuci, Gwndaf Hughes
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Science videographer
- Lokacin karatu: Minti 3
Kumbon da Hukumar nazarin sararin samaniya ta Turai ta tura zuwa duniyar rana, a karon farko ya turo hotuna na farko da aka taɓa gani na ɓarin kudancin duniyar rana.
Ana sa ran hotunan za su ƙara wa masana kimiyya fahimta kan rayuwar duniyar rana a lokutan da take tafarfasa da kuma lokacin da takan natsu.
Wannan na da muhimmanci sosai kasancewar abubuwan da ke faruwa da duniyar rana na iya shafar harkar sadarwa da kuma katse wutar lantarki a duniyar bil'adama.
Hotunan sun nuna wani yanki mai gagarumin tsananin haske a kan rana wanda zafinsa a wasu lokuta kan kai maki miliyan ɗaya a ama'aunin zafi.
A tsakankanin yankin kuma akwai giragizan sinadarai waɗanda zafinsu bai kai tsananin sauran yankin ba, amma duk da haka su ma zafinsu kan kai maki 100,000 a ma'aunin zafi.
Hotunan da kumbon ya turo su ne waɗanda aka ɗauka a wuri mafi kusanci da rana kuma mafiya kyawu, kuma farfesa Carole Mundell ta Hukumar nazarin samaniyar Turai ta ce za su bayyana wa ɗan'adam wani sirri na duniyar rana.
"A yau mun kawo muku hotunan wani sashen duniya da ɗan'adam bai taɓa gani ba," in ji ta.
"Rana ita ce tauraro mafi kusa da mu, wadda ke taimaka wa rayuwarmu, wadda kuma za ta iya yin cikas ga aikin binciken sararin samaniya da hanyoyin samar da lantarki a duniya, saboda haka yana da muhimmanci mu fahimci yadda rana ke rayuwa domin samun ilimin yin hasashe kan abin da za ta iya yi".
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Daga nan duniyarmu, ana hangen rana a matsayin wata ƙwallo mai haskakawa. To amma masana kimiyya na amfani da wasu na'urori wajen ganin ainahin yadda take: a matsayin wani curin ruwan sanadarai mai jujjuyawa tana tunzuri tare da amon tururin sanadarai zuwa sararin samaniya.
Ƙarfin maganadinsu da ke jikin rana ne ke tantance lokutan da rana kan tunzura ta hankaɗo sanadarai zuwa duniyarmu.
Masana kimiyya sun san cewa akwai lokutan da rana kan natsu sa'ilin da ƙarfin maganaɗisun da ke jikinta suka daidaita tsakanin ɓarinta na arewa da kuma ɓarinta na kudu. A wannan lokaci rana ba ta yin tunzuri ko yin amon tururi cikin fushi.
To sai dai akwai lokutan da abubuwan kan cakuda su garwaya, su yamutse inda sukan fusata sa'ilin da suke sauya mazauni tsakanin ɓarin arewaci da kuma kudancin rana, inda suka juya a cikin kimanin shekara 11.
A lokacin da aka samu wannan hargitsewa ne rana ke fitar da abubuwan da ta ƙunsa a fusace, inda wani ɓangare na irin wannan amai da ranar ke yi kan tunkuɗo zuwa wajajen duniyarmu.
Irin wannan tumbuɗi kan iya lalata taurarin zamanin sadarwa da cibiyoyin samar da ƙarfin lantarki, duk da cewa kuma sukan samar da wasu launuka masu kyawun gani a sararin samaniya.
Farfesa Lucie Green ta ce yana zamewa abu mai wahala bil'adama su yi hasashen irin waɗannan abubuwa da ke faruwa a rana ta hanyar amfani da kwamfutocin da ake da su kasancewar babu isasshen bayani kan yadda waɗannan sadadari da ƙarfin maganaɗisu ke yin ƙaura daga arewaci zuwa kudancin rana da kuma akasin hakan.
Sai dai ta ce a yanzu lamarin ya sauya.
"Yanzu mun gano sirrin abin da ya shige mana duhu," kamar yadda ta shaida wa BBC.

Asalin hoton, ESA
Babban maƙasudin binciken shi ne a samar da wata na'urar kwamfuta mai sanya ido kan rana ta yadda za ta iya lura da kuma yin hasashen waɗannan sauye-sauyen yanayi da ake samu a kan duniya rana.
Iya samun tartibin hasashe kan sauyawar yanayin rana zai bai wa masu lura da taurarin ɗan'adam da tashoshin samar da lantarki da kuma masu sha'awar kallon hasken sararin samaniya mai launuka masu ban sha'awa tsara ayyukansu.
"Kumbon zagayen duniyar rana zai taimaka mana wajen gano tushen ilimin sauyawar yanayi a sararin samaniya. Amma akwai sauran aiki ƙalilan da za mu yi domin kaiwa inda za mu iya ganin alamun gane cewa rana za ta yi tumbudin da zai iya kawowa duniyarmu," in ji Farfesa Christopher Owen.

Asalin hoton, ESA
Kumbon nazarin duniyar ranar ya kuma ɗauko hoton sanadarai a wuri daban-daban na duniyar rana da kuma yadda suke wulgawa.
A karon farko, tsarin da aka yi amfani da shi wajen ɗaukar hoton sanadaran an yi amfani da shi wajen auna saurin tafiyar curin sanadaran duniyar. Wannan zai taimaka wajen fayyace yadda ake tukuɗo curin turiri daga cikin rana.












