Katafaren jirgin ruwan yaƙin China da ke gogayya da na Amurka

Asalin hoton, CCTV
- Marubuci, Benny Lu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Chinese
- Lokacin karatu: Minti 5
Katafaren jirgin ruwan yaƙi na China na uku, wanda ƙasar ta ƙaddamar a watan Nuwamban 2025 ya fi guda biyu na baya da ta ƙaddamar girma da amfani, in ji masana, lamarin da ya ƙara kusantar da Beijing ga muradunta na yin kafaɗa da kafaɗa da Amurka wajen zama kan gaba a ɓangaren sufurin jiragen yaƙi a teku.
Jirgin mai suna Fujian mai nauyin tan 80,000, an sanya masa sunan wani yanki ne da ke kusa da Taiwan, kuma zai iya ɗaukar jiragen yaƙi guda 70 da sauran kayan yaƙi da za su iya gano barazanar tsaro daga nesa da samar da kariya da kuma mayar da martanin hare-hare.
Haka kuma bayan ƙara ɗaga darajar rundunar sojin ruwan China, ƙaddamar da jirgin ma kaɗai wani sako ne mai girman gaske.
Jirgin na ɗauke da shimfiɗaɗɗen ƙarfe da farantan harba jiragen yaƙi, ta yadda zai iya tayar da jiragen yaki masu girma, ya dauki mai mai yawa da kuma makamai. Amurka ce kaɗai ke da jirgin ruwa irin wannan.
"Wannan matakin ya ƙara ɗaga darajar China a fagen mallakar makaman yaƙi na zamani, domin wannan sabon jirgin ya ɗara guda biyu da take da su a baya wato Liaoning da Shandong," in ji Dr William C Chung na cibiyar bincike da nazarin harkokin tsaro ta Taiwan a zantawarsa da BBC.

Asalin hoton, Getty Images
Kafar yaɗa labaran China ta kambama ƙaddamar da jirgin ruwan yaƙin na Fujian, inda ta bayyana shi da "babbar nasara" wajen inganta aikin sojan ruwa a ƙasar. Yanzu China za ta iya yin "kafaɗa da kafaɗa" da Amurka a "ɓangaren jiragen ruwan yaƙi, in ji Dr Chung.
Ya kalato yadda mujallar New York Times ta bayyana jirgin da canji daga "bayar da kariya" zuwa "jirgin ruwan ƙaddamar da hare-hare." Sannan Shugaban China Jinping Xi ya bayyana a wata sanarwa cewa, "tekunan duniya suna da yawan da Amurka da China za su iya shiga su duka ba tare da matsala ba."
China tana ta ƙoƙarin faɗaɗa ɓangaren sojin ruwanta a ƙarƙashin mulkin Xi, sannan yanzu ƙasar ta fara tara jiragen ruwa, lamarin da ke ƙara matsa lamba kan Amurka da ƙawayenta.
Shugaban ƙasa ne da kansa ya ɗauki matakin tabbatar da an saka ƙugiyar harba jiragen, kamar yadda kafar yaɗa labaran ƙasar ta ruwaito, sannan da kansa ya jagoranci bikin ƙaddamar da jirgin a kudancin tsibirin Hainan, inda ya yaba da jirgin da direbobinsa.
A lokacin bikin ƙaddamar da jirgin, Xi wanda ya isa wajen da kakin soja, inda ya ce, "mu yi yaƙi domin neman nasara, sannan ku yi aiki tare da amfani da doka da tsari."

Asalin hoton, Getty Images
Cibiyar nazarin tsare-tsare ta Australia ta bayyana jirgin Fujian a matsayin nasara babba da zai iya ɗaukar mayaƙa da makamansu.
Dr Chung ya shaida wa BBC cewa "idan ana zaman lafiya, jirgin ruwan yaƙin Fujian zai yi amfani ne wajen nuna ƙwanji da Amurka, amma kuma a gaba jirgin zai yi amfani matuƙa domin wataƙila a iya tura shi Gabas ta Tsakiya ko Afirka ko Turai."
China ta daɗe tana nanata cewa ƙasar Taiwan yankinta ne, inda ta nanata cewa "za ta ƙwato ta" kuma takan nuna cewa za ma ta iya amfani da ƙarfin soji.
Dr Satoru Nagao, na cibiyar masana ta Hudson da ke Washington, ta bayyana cewa jirgin Fujian na barazana ga tsaron Taiwan.
Sai dai ya ce duk da barazanar, rundunar sojin ruwan Amurka da ke jibge a Okinawa da Japan da Koriya ta Kudu da Guam da ma Philippines za su iya kai ɗauki cikin gaggawa, sannan jirgin ruwan yaƙin Amurka na US 11 mai girma tan 100,000 yana amfani ne da makamashin nukiliya.


Asalin hoton, AFP via Getty Images
Dr Chung ya nuna cewa kasancewar jirgin ruwan Fujian da man dizel yake amfani, kuma China ba ta da babban tashar jirgin ruwa na ƙasar waje, hakan na nufin dole a riƙa kai wa jirgin mai, wanda hakan na iya shafar aikinsa musamman idan ana tsaka da aiki.
A nazarin Fujian da aka wallafa a watan Oktoban 2025, Aita Moriki na cibiyar bincike da nazarin tsaro ta Japan, ya rubuta cewa, "akwai matsaloli da ƙalubale da jirgin ke fuskanta."
Dr Chung ya shaida wa BBC cewa, "baki ɗaya idan aka kwatanta yanayin aikin da Fujian zai iya yi da ma sauran jiragen yaƙin ruwan China da na Amurka, za a ga akwai bambanci saboda an taɓa ganin aikin na Amurkan a fagen yaƙi."
Shi ma wani hafsan sojan ruwan Amurka Rear Amiral Brett Mietus ya shaida wa jaridar Washington Post a watan Satumba cewa, "suna da jiragen ruwa uku, muna da guda 11 kuma mu ba sabon shiga ba ne."

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Samun cigaba wajen samar da makamai masu linzami da suke iya cin dogon zango ya rage muhimmancin amfani da jiragen ruwan yaƙi, sannan duk da cewa jirgin na iya harba jirgin sama ya tashi cikin sauƙi, dole ne sai jirgin ya ɗan yi tafiya kafin ya tashi, wanda abu ne mai hatsari.
"Idan aka samu cigaba sosai wajen amfani da ƙirƙirarriyar basari, jirage marasa matuƙa za su fi samun karɓuwa," in ji Dr Nagao.
Amma duk da haka tuni China ta fara aikin haɗa jirgin ruwan yaƙinta na huɗu, kamar yadda hotunan tauraron ɗan'adam suka nuna, inda masana suka ce ƙasar na ƙoƙarin inganta jirgin ne ya koma amfani da makamashin nukiliya, sannan masana suka ƙara da cewa hakan zai ƙara ta'azzara gogayyar da ke tsakanin ƙasashen biyu a yunƙurin zama kan gaba a makaman ruwa.











