Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sanusi II ya mayar wa Gwamna Ortom martani kan kisan makiyaya a Nasarawa
Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi na biyu, ya ce suna zargin gwamnatin Benue da hannu a kisan fulani makiyaya waɗanda ba su aikata laifin komai ba.
Kalifan na ɗarikar Tijjaniya ya ce bayanan da suka tattara sun nuna cewa hare-haren da ake kai wa makiyaya a jihar Nasarawa wanda ake zargin sojojin saman Najeriya da kai wa, sun fito ne daga jihar Benue.
Ya ce suna zargin gwamnan ne saboda shi ne gwamna da ya yi dokar da ta hana fulani kiwo, da kuma kafa wata kungiyar jami’an tsaro masu ɗaukar bindigogi.
Sanusi II ya ƙara da cewa “gwamna Ortom ba shi da ‘yanci ko hakki na bai wa waɗansu mutane bindigogi waɗanda su ba sojoji ba ne ko kuma ‘yan sanda.’’
“An je Nasarawa an jefa wa fulanin nan bam har sau biyar, gwamnan jihar (Nasarawa) ba shi ya ce a yi ba, babu kuma Sarki a jihar da ya ce ga wasu ‘yan ta’adda a nan a zo a jefa musu bam.”
“Dukkanin hare-haren da ake kai wa jihar Nasarawa sun fito daga Benue ne, tun da mun san ra’ayinsa a kan fulani dole mu zarge shi, babu kuma yadda za a fita daga zargi sai an yi bincike. Me zai hana a yi bincike.”
Ya ce har kawo yanzu fadar shugaban ƙasa ba ta fito ta jajanta wa iyalan waɗanda aka kashe ba balle ace za a yi maganar biyan diyya.
Ya kuma ce sun rubutawa shugaban ƙasa takarda domin ganin an yi bincike da nufin gano waɗanda ke da hannu a kisan fulani makiyayan.
Abin da Gwamna Ortom ya ce
A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, gwamna Ortom ya ce wasu mutane tare da jagorancin Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sanusi, sun yi wasu zarge-zarge a kanshi, a wani yunkuri na sanya a kai masa hare-hare.
Ortom ya ce an zarge shi da hannu a hare-haren da jirgin sojin saman Najeriya ya kai a iyakar jihohin Nasarawa da Benue, inda ya kashe wasu fulani tare da dabbobinsu.
“Hankalina ya karkato kan wata wasika da wasu kungiyoyin fulani 52 da Sanusi ke jagoranta suka rubuta wa shugaban ƙasa, inda suka yi wasu zarge-zarge a kaina a wani yunkuri na sanya mutane su tsane ni da kuma kai min hari,’’ in ji Ortom.
Ya ce Sanusi na II ya yi wani bidiyo, inda a ciki yake kokarin ɓata masa suna da kuma kiran dukkan fulani su ɗauke shi a matsayin abokin gaba.
Wasiƙar da ƙungiyar fulanin ta rubuta wa shugaban ƙasa dai ta nemi a gudanar da bincike ne kan harin jirgin sama a cikin jihar Nasarawa, wanda ya yi sanadin halaka Fulani kimanin 40.