Rasha za ta sanya wa jami'an Japan takunkumi saboda Ukraine

Asalin hoton, EPA
Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce za ta hana wasu 'yan kasar Japan su 13 da ke da alaka da kungiyoyi da kamfanoni da ke da hannu a aikin sake gina Ukraine da taimaka mata , shiga kasar har sai abin da hali ya yi.
Wata kafa ta diflomasiyyar Japan ta mayar da martani da cewa matakin na Rasha ya wuce hankali, kuma hakan zai iya sanya damuwa ga kamfanonin Japan da ke duba yuwuwar taimaka wa Ukraine wajen sake gina kasar.
Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta ce ta dauki wanan mataki ne a matsayin ramuwar gayya ga Japan kan irin takunkumin da gwamnatin Japan ta bi sahu wajen sanya wa Rasha a kan mamayen da ta yi wa Ukraine.
Haramcin hana shiga kasar ya hari shugabannin harkokin kasuwanci da dama na Japan, wadanda suka hada da shugaban kamfanin kera motocin Toyota, Akio Toyoda.
Haka kuma haramcin ya hada da shugaban rukunin kamfanonin Rakuten, Hiroshi Mikitani – wanda ya je Ukraine a watan Satumba, tare da ministan harkokin wajen Japan na wancan lokacin.
Daman dai tuni Rasha ta sanya harmacin shiga kasarta na sai-baba-ta-gani a kan Firaministan Japan din Fumio Kishida, da shugabannin majalisun dokokin kasar biyu, da wasu ministoci da kuma wasu ‘yan jarida.
A watan Fabarairu Japan ta ce za ta bai wa Ukraine tallafin sama da dala miliyan dari daya, domin daukar matakan kariya daga nakiyoyi da aka binne a kasa, da bama-bamai da aka binne wadanda ba su tashi ba, da gyara wutar wutar lantarki da kuma sauran kayayyakin samar da makamashi.






