Yadda attajiran Rasha ke guduwa Dubai don kauce wa takunkumai

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Sameer Hashmi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Middle East business correspondent
Birnin Dubai ya zama wata matattarar da ake ajiye dukiyar attajiran Rasha domin kauce wa takunkumin kasashen Yamma kan rikicin Rasha da Ukraine.
Biloniyoyi 'yan Rasha da dama da 'yan kasuwa sun isa Hadaddiyar Daular Larabawa, kamar yadda shugabannin kasar suka shaida wa BBC.
Rahotanni sun ambato cewa sayen kadarori a Dubai ya tashi da kimanin kashi 67 cikin 100 a wata hudun farko na 2022.
Hadaddiyar Daular Larabawa ba ta sanya wa Rasha takunkumi ba, haka kuma ba ta soke ta ba kan mamayar da take yi a Ukraine.
Haka kuma tana bai wa wadanda ba a sanya wa takunkumi ba biza yayin da kasashen Yamma ke hana su.
An yi hasashen dubban 'yan Rasha sun tsere daga kasar cikin kusan wata biyu - ko da yake babu takamaiman adadin mutanen.
Wani masanin tattalin arzikin Rasha ya ce akwai kimanin mutum 200,000 da suka bar Rasha a kwana 10 na farkon fara yakin.
Kamfanin Virtuzone, wanda yake taimaka wa kamfanoni su fara aiki a Dubai, ya samu matukar ci gaba ta fuskar abokan hulda daga Rasha.
"Muna samun tambayoyi ninkin yadda muke samu a baya, sau biyar daga Rashawa tun bayan fara rikicin," in ji shugaban kamfanin George Hojeige.
"Sun damu ne game da koma-bayan tattalin arzikin da ke fuskantar su, shi ya sa suke dawowa nan domin su tsira da dukiyoyinsu," in ji shi.
Tururuwar da 'yan Rasha ke yi ta sanya ana kara samun bukatar manyan gidaje a fadin birnin wadanda za a saya. Dillalai na ambato cewa kadarori na kara tashi, lokacin da mutanen Rasha ke tururwar sayan gidaje.

Asalin hoton, Getty Images
'Ficewar kwararru'
Manyan kamfanoni da kananan masana'antun Rasha su ma suna ta komawa Hadaddiyar Daular Larabawa.
Fuad Fatullaev, wani babba ne a kamfanin WeWay da ke da rassa a Rasha da Ukraine. Bayan yakin nan ya barke, ya komar da abokan aikinsa daruruwa zuwa Dubai.
"Wannan yakin ya haifar da matukar tasiri a ayyukanmu. Ba za mu iya ci gaba da aiki yadda muke yi a baya ba, dole mu kwashe mutanenmu daga Ukraine da Rasha in ji Fuad dan kasar Rasha.
Ya ce sun gwammace su mayar da mutanensu zuwa UAE inda nan n ake da tsarin tattalin arziki mai kyau.
Ya ce kasuwanci a Rasha na samun koma baya saboda yawan takunkuman da ake sa musu. lamarin ya fi kazanta kan kamfanonin da suke mu'amala da abokan hulda na kasashen duniya, kamfanonin Yamma na ta warware huldarsu da wadanda suke zaune a Rasha.
Manyan kamfanonin duniya irin su Global Goldman Sachs da JP Morgan da kuma Google duk sun rufe ofisoshinsu a Rasha, kuma sun mayar da ma'aikatansu zuwa Dubai.
An samu tashin farashin gidaje
An dakatar da babban bankin Rasha daga taba ko kwandala daga cikin manyan kudaden da take da su a asusun ajiyarta na kasashen waje. Wasu bankunan kasashen wajen duk sun fice daga kasar.
Domin kare asusunta na kasashn ketare, gwamnatin Rasha ta sanya dokar hana daukar kudaden wajen da suka wuce dala 10,000.
Wannan ya janyo wahalar garin kudade, yasanya yan Rasha da yawa ke sayayya da kudaden intanet na cryptocurrencies.
Kasashen yankin Glf da suka hada da UAE da Saudiyya sun yi watsi da kiran gwamnatocin yammacin turai na sanyawa Rasha takunkumi.
UAE na daya daya daga cikin kasashe uku da suka kauracewa kada kuri'a a zauren Majalisar Dinkin Duniya na tsaro a watan Fabirairu kan mamayar Rasha, ciki har da Indiya da China. Ta kuma kauracewa babban taron kada kuri'a da aka yi a ranar 7 ga watan Afrilu na dakatar da Rasha daga kwamitin kare hakkin dan adam na MDD.











