Yadda wani ya ha'inci aminiyarsa da ƙirƙirarrun hotunan tsiraicinta

Ƴar ƙasar Australia Hannah Grundy ta yi matuƙar kaɗuwa da ta gano wani shafin Intanet da ke dauke da hotunanta na ƙarya

Asalin hoton, Nikki Short/BBC

Bayanan hoto, Ƴar ƙasar Australia Hannah Grundy ta yi matuƙar kaɗuwa da ta gano wani shafin Intanet da ke dauke da hotunanta na ƙarya
    • Marubuci, Tiffanie Turnbull
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Sydney
  • Lokacin karatu: Minti 8

Gargaɗi: Wannan labarin Ya ƙunshi kalamai masu banƙyama da kwatancen cin zarafi mai alaƙa da jima'i

A wani daren watan Fabrairu ne wani mummunan saƙo ya shiga cikin akwatin saƙon Hannah Grundy a Sydney.

"Zan ci gaba da aika miki saƙon imel saboda ina ganin wannan ya cancanci ki mayar da hanlkali a kansa," wani wanda bai bayyana sunansa ba ya rubuta.

A cikin saƙon akwai wani link, tare da gargaɗin da cewa : "[Wannan] ya ƙunshi abubuwa masu tayar da hankali."

Ta dan yi jinkiri kaɗan, tana tsoron ko wata zamba ce.

Lamarin da ya kasance a zahiri ya zame mafi muni. Shafin na Intanet ya ƙunshi shafuka ne ɗauke da hotunan batsa na ƙarya da ke nuna Hannah, da cikakkun bayanai na fyaɗe da barazanar tashin hankali.

"Ki na ɗaure a cikin hotunan," in ji ta. "Ki na cikin fargaba, ki na da hawaye a idanunki, kina kulle a cikin keji."

A kan wasu hotunan an rubuta cikakken sunan Hannah. Da adiresin shafinta na Instagram, har ma da unguwar da take zaune. Daga baya ma za ta samu labarin cewa an bayar da lambar wayarta.

Wannan imel ɗin ya kasance farkon wani abun da Hannah ta kwatanta da fim. Lamarin ya sanya ta zama wata cikakkiyar mai binciken ƙwaƙƙwaf, inda ta gano cin amanar da wani na kusa da ita ya yi, ya kuma kai ga ta gina shari'ar da ta sauya rayuwarta - da kuma ka'idojin shari'a na Australia.

'Zallar kaɗuwa'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sunan shafin intanet ɗin "The Destruction of Hannah", kuma a saman sa akwai inda ɗaruruwan mutane suka kaɗa ƙuri'a kan munanan hanyoyin da suke son a ci zarafinta.

A ƙasa akwai jerin munanan hotuna sama da 600, waɗanda aka ɗaura masu fuskar Hannah. Kuma a cikinsu an rubuta kalamai masu barazanar tashin hankali.

Rubutun da aka yi kan babban hoton na cewa "Ina daf da in afka kan wannan ƴar iskar."

"Ina so in ɓoye a cikin gidanta in jira sai ta kasance cikin kaɗaici, sai in cafke ta daga baya...ji yadda ta ke faman kufcewa."

Yau shekaru uku ke nan, amma malamar makarantar mai shekaru 35 ba ta da wata matsala ta tuno da "zallar kaɗuwar" da ta yi lokacin da ita da abokin zamanta Kris Ventura, mai shekara 33, suka buɗe shafin.

"Nan da nan sai ka ji ka fara jin ɗar-ɗar," in ji Hannah, idanunta a a buɗe fayau yayin da ta ke riƙe da kofin shayi a cikin gidanta.

Yayin da ya ke bincika shafin Kris ya kuma ci karo da hotunan abokansu na kurkusa, tare da hotuna da ke nuna aƙalla wasu mata 60, da yawa kuma daga birnin Sydney.

Cikin ƙanƙanin lokaci suka gane cewa hotunan da aka yi amfani da su don ƙirƙirar hotunan batsan sun fito ne daga shafukan sada zumunta na matan. A lokacin ne suka fahimci cewar: wannan aiki ne na wani wanda ke kusa da su.

Suna neman gano wanene, Hannah da Kris sun shafe sa'o'i, suna bincike kan matan da ke cikin hotunan, suna bincika jerin abokansu na kafofin sada zumunta don ƙoƙarin gano wani mutun ɗaya da ya san duka matan.

A cikin sa'o'i huɗu, sun sami jerin sunayen mutane uku da suke zargi.

A cikin jerin sunayen akwai abokinsu na kurkusa daga jami'ar Andrew Hayler. Amma sun yi watsi da zargin da suke yi masa. Sun dai haɗu ne yayin da suke aiki a mashaya, kuma ma'aikatan da ke wurin sun kulla abota ta ƙut da ƙut.

Kuma Andy, kamar yadda ake kira shi - shi ne kusan jagorar ƙugiyar ta su.

Hannah da Kris da Andy (dama) sun haɗu ne yayin da suke aiki a wata mashaya ta jami'ar Sydney

Asalin hoton, Supplied

Bayanan hoto, Hannah da Kris da Andy (dama) sun haɗu ne yayin da suke aiki a wata mashaya ta jami'ar Sydney

Hannah ta ce, ya kasance mai kulawa da iya magana - irin mutumin da ya ke kare mutuncin mata a mashayar kuma ya tabbatar da abokansa mata sun dawo gida lafiya bayan sun fita yawon shaƙatawa.

Dukansu suna haɗuwa akai-akai, sun tafi hutu tare, akwai ƙauna a tsakaninsu kuma sun amince da juna.

Hannah ta ce: "Na ɗauka shi a matsayin amini na."

"Muna da tabbacin cewa shi mutumin kirki ne."

Amma ba da daɗewa ba suna ɗaya ne kacal ya rage a jerin sunayen da suke zargi: sunansa.

Fargaba da jinkiri

Washe gari Hannah ta farka ta nufi ofishin ƴan sanda, baya ga halin kaɗuwa da fargaba da ta shiga ta kasance ta na da ƴar kyakkyawar fata.

"Mun yi tunanin za su kama shi da yammacin wannan rana," in ji Kris yayin da ya ke murmushi.

A madadin haka, Hannah ta ce an gamu rashin nasara.

Ta tuna cewa wani ɗansandan New South Wales ya tambaye ta abin da ta yi wa Andy. A wani mataki shawar suka bai wa Hannah cewa ta yi masa magana ya daina. Daga baya, sai suka nuna hotonta ta na sanye da wasu ƙananan kaya, suka ce "kin yi kyau a cikin wannan," in ji ta.

Ƴansandan New South Wales sun ki cewa BBC uffan game da batun Hannah.

Sai dai ta ce yadda aka tafiyar da kokenta ya sa ta ji kamar ta na "tayar da hankalinta ne kawai kan abun da bai kai ya kawo ba".

"Kuma ni ina jin cewa, wani abu ne mai sauya rayuwa," in ji Hannah.

Duk wani tunanin da ta ke yi na cewa ƴansanda za su taimake ya watse cikin ƙanƙanin lokaci.

yayin da ta ga jinkirin ya yi yawa, ta karkata zuwa ga Kwamishinan hukumar kula da shafuka intanet (eSafety) na Austiralia, amma a ƙarƙashin ikonta a matsayin ta na hukumar sanya ido, taimakon da za ta iya yi shi ne ta sauke hotunan daga intanet.

Andy ya gyara kuma ya wallafa ɗaruruwan hotunan Hannah ta hanyar amfani da fasahar ƙirƙirar bidiyo da hotuna

Asalin hoton, Supplied

Bayanan hoto, Andy ya gyara kuma ya wallafa ɗaruruwan hotunan Hannah ta hanyar amfani da fasahar ƙirƙirar bidiyo da hotuna

Cikin tashin hankali, ma'auratan sun ɗauki hayar lauya kuma suka samu wani manazarci a ɓangaren fasaha don su ga ko abubuwa za su sauya,

Syn fara zama cikin halin ɗar-ɗar.

"Sai ku ji duniyar ma ta yi muku kaɗan. Ba ku magana da mutane. Ko waje ba ku iya fita," in ji Hannah.

Rayuwar ta kasance cike da tsananin tsoro da kuma kaɗaici.

"Mun riga mun dakatar ƙoƙarin fahimtar dalilin da ya sa ya aikata waɗannan abubuwan, saboda haka tunanin cewa zai iya zuwa ya yi maka fyadɗe ko ya cutar da kai ba wani abun mamaki ba ne."

Ma'auratan sun kewaye gidansu da kyamarori kuma sun kafa manhajar bibiyar inda Hannah ta ke a duka wayoyinta. Ta fara amfani da agogon duba lafiya a kodayaushe, don haka wani zai san idan zuciyarta tana bugawa ko kuma idan ta tsaya.

Hannah ta ce "Na daina buɗe tagogi saboda tsoro...wataƙila wani yana iya kutsowa."

"Mun kwana da wuka a duka teburin mu na gefen gado saboda kawai muna tunanin: Me zai iya faruwa?"

An kai wani matakin da aka ce an dakatar da bincike kan batun, Hannah da Kris sun ƙara biyan wasu kuɗaɗe don samun cikakken rahoton binciken, kuma sun yi barazanar kai ƙara ga hukumar kula da ɗa'ar ƴansanda. Sun dai kashe sama da Fam 10,200 domin ƙoƙarin kare kansu da kuma takawa Andy birki.

Daga ƙarshe an zo an sanya wani sabon jami'in bincike kuma a cikin makonni biyu ƴan sanda sun kai farmaki gidan Andy, inda ya amsa laifin da ake zarginsa da shi.

Cike da walwala, Hannah ta fara kiran ƙawayenta don shida masu halin da ake ciki.

Jessica Stuart ta ce, "Hankali na ya yi matuƙar tashi'', tun lokacin da ta sami labarin abin da Andy ya yi da hotunanta.

Wata mata

Asalin hoton, Nikki Short/BBC

"Na ji da gaske an ci zarafi na amma… bana jin na fahimci lamarin baki ɗaya."

Abun da ya fi tayar mata da hankali shi ne cewar abokin da take ƙauna kamar "dangi" ne ya aikata laifin. Andy ya kasance kamar mutumin kirki, mai tunani - wanda ta ke neman taimakonsa idan ta shiga mawuyacin hali.

"Yana da matuƙar wahala a daidaita cewa mutanen biyu a zahiri mutum ɗaya ne."

Shari'ar da ba a taɓa ganin irin ta ba

An tuhumi Andy, mai shekara 39 da yin amfani da na'urorin sadarwa don yin barazana, da muzgunawa-mafi yawan tuhumar da ake yi wa laifuffuka da yawa na intanet - kuma an gargadi Hannah da kar ta sa rai cewa za a yi masa wani hukunci mai tsanani..

"Mun shirya mu je kotu domin ya yi masa hukunci da bai kai ya kawo ba," in ji ta.

Amma ita da sauran mata 25 da suka yanke shawarar shiga cikin shari'ar sun sha alwashin cewa Andy sai ya fuskanci hukunci. Ɗaya bayan ɗaya, da dama sun ba da shaida cike da kalamai masu muni a lokacin da aka zo yanke masa hukunci a bara.

Jess ya shaida wa kotu cewa "Ba amanar abotata kaɗai ka ci ba, amma ka wargaza yanayin kwanciyar hankalin da na ke da ita, wanda ban ɗauka a matsayin komai ba." "Duniya ba ta yi mun daɗi kuma tana da cike da haɗari, koyaushe ina cikin damuwa, ina mafarke - mafarke lokacin da na sami damar yin barci.

"Ina jin ba zan iya ƙirƙirar sababbin abokantaka ba, inda a kodayaushe na ke tambaya: 'Shin wannan mutumin zai iya zama kamar kai?"

Hannah da Jess sun rungume juna a bara, bayan da aka yanke wa Andy hukuncin zaman gidan yari

Asalin hoton, Ethan Rix/ABC News

Bayanan hoto, Hannah da Jess sun rungume juna a bara, bayan da aka yanke wa Andy hukuncin zaman gidan yari

Da aka kai lokacin da Andy zai nemi gafarar matan da ya kai wa hari, Jess da Hannah sun kasa zama a ɗakin. Sai suka tashi suka fita

Hannah ta ce: "Babu wani abu da zai iya faɗa mini da zai wanke abun da ya yi, kuma ina son ya san hakan."

Andy ya shaida wa kotun cewa ƙirƙirar hotunan ya sanya ya ji kamar ya samu "ƙarfafawa" kuma ya yi amfani da su ne don ya kore wasu munanan tutanin da ke cikin zuciyarsa , amma ba ya tunanin za su haifar da wata illa.

"A gaskiya na yi mummunan abu kuma na yi nadama sosai," in ji shi.

Mai shari'a Jane Culver ba ta gamsu da cewa ya yi nadama ba, tana mai cewa yayin da akwai "nadama kaɗan", da alama bai fahimci "irin mummunar illa da matuƙar damuwa da laifin nasa ya haifar ba.

Ta yanke wa Andy hukuncin ɗaurin shekaru tara a gidan yari - hukuncin da ba a taɓa yankea a shari'o'i irin wannan ba.

Jess ta ce: "Wannan shi ne karo na farko da na ji kamar a zahiri an saurare mu."

Andy zai cancanci damar samun afuwa a watan Disambar 2029, amma ya shaidawa kotu cewa yana da niyyar ƙalubalantar hukuncin da aka yanke masa.