Yadda sabon tsarin canji na CBN zai shafi darajar naira

Naira

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Naira

Wasu masana tattalin arziki sun ce matakin da Babban Bankin Najeriya CBN ya ɓullo da shi na ba da dama ga bankunan kasuwanci su sayar da dala a kan farashin da kasuwa ta ƙayyade, zai taimaka wajen daidaita farashin dala a ƙasar

Duk da yake sun ce mai yiwuwa ne a fuskanci wahalhalu da farko.

A ranar Laraba ne, Babban Bankin ya fitar da wata sanarwa da ke cewa ƙasar ta dunƙule tsarin canjin kuɗaɗen waje zuwa guda ɗaya.

A baya, Najeriya na amfani da tsarin canjin kuɗaɗen waje na hukuma da kuma na bayan fage, lamarin da ya sa ake samun farashin dalar Amurka iri biyu.

Babban Bankin ya kuma bai wa bankunan kasuwanci damar yin canjin kuɗi a kan farashin da kasuwa ta ƙayyade.

Wannan lamari ya sanya a hukumance darajar naira ta karye daga naira 477 zuwa 750 a kan duk dalar Amurka ɗaya ranar Laraba.

Abin da ke nufin darajar naira ta karye da kashi 36% a kaikaice.

Shi ne karyewar darajar naira mafi girma da aka samu a hukumance tun bayan ta 2016 gabanin CBN ya fitar da sabon farashi a 2017.

Kafin wannan mataki bankuna na canjin dalar ne a kan farashin da Babban Bankin Ƙasar (CBN) ya ƙayyade.

Matsalar tattalin arziki na ɗaya daga cikin ƙalubalen da sabon shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya gada, ya kuma yi alƙawarin shawo kanta.

Bola Tinubu

Asalin hoton, PRESIDENCY

Bayanan hoto, Bola Tinubu
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A baya dai CBN ne yake ƙayyade farashin kuɗin ƙasashen waje, matakin da wasu masana ke kallo a matsayin wata hanya da ta riƙa haddasa ƙarancin kuɗaɗe kamar dalar Amurka - wadda masu harkoki zuwa ƙasashen waje suka fi amfani da ita wajen hada-hada.

Ƙwararru a fannin tattalin arziƙi a Najeriya kamar Dakta Ahmed Adamu na jami'ar Nile ta Abuja na cewa matakin mai kyau ne, ko da yake akwai buƙatar yin taka-tsantsan.

Ya ce ɗaya daga cikin matsalolin da ke haifar da tashin farashin dala a Najeriya ita ce samun kasuwanni kuɗi biyu masu bambancin farashi, to amma idan ana so a haɗe su, kamata ya yi sai an yi la'akari da wasu abubuwa.

"Babban Bankin Najeriya kaɗai ba zai wadatar da 'yan ƙasar da ke buƙatar dala ba, don haka wannan mataki zai taimaka wajen bai wa 'yan ƙasar damar samun dala tare da sayar da ita a kan farashin da kasuwa ta ƙayyade," in ji shi.

Ya ce amfani da kasuwanni biyu masu mabambantan farashi, da zagon ƙasa ga wasu tsare-tsaren tattalin arziki ne suka taimaka wajen haddasa tashin farashin dala.

Amma dunƙule kasuwar a ƙarƙashin wani tsarin da ake kula da shi zai sanyaya gwiwar masu hasashen farashi.

A cewarsa masu hasashen sukan sa rai ne da halin da kasuwa za ta kasance a gaba, sai su ɗauki mataki yanzu. Idan suna sa ran farashin dala zai tashi, sai su saya kafin lokacin su ajiye. Idan suna sa ran dala za ta faɗi, sai su sayar da wuri. Su riba suke bi.

"Sai dai idan aka tokare tsarin canjin a wata iyaka, to farashin kuɗin ba zai yi gagarumin tashi ba.

Jadawalin canjin kuɗin na iya kasancewa ta yadda farashi ba zai wuce ƙari ko ragin darajar kashi biyu cikin 100 a kullum ba ko canjin kashi 10% duk shekara."

Ya ce: "Ana iya ci gaba da haka har zuwa lokacin da masana'antu masu fitar da kaya zuwa ƙetare, za su yi ƙarfi, har ƙasar ta riƙa samun ƙarin kuɗaɗen waje.

Daga nan gwamnati na iya ƙarawa ko rage farashin kuɗi ta hanyar da kasuwa ta ƙayyade. Hakan zai fi matuƙar tasiri tun da a lokacin akwai ɗumbin kuɗin ƙasashen waje a lalitar ƙasar".

A cewar Dakta Adamu a 1985, Naira ɗaya daidai take da dalar Amurka ɗaya.

Amma a 2023, dala ɗaya ana canzar da ita a kan N760, hakan na nufin darajar naira ta karye da kashi 75,900% a cikin shekara 38 kawai, in ji shi.

"A cikin shekara takwas da ta wuce, naira ta faɗi da kashi 265%".

"Bisa la'akari da haka, dala na iya ci gaba da ƙara tsada har ta kai ana canzar N1000 a kan dala ɗaya matuƙar ba a yi wani abu ba.

Karyewar darajar naira in ji ƙwararren na nufin kayayyakin da muke saya daga ƙasashen waje sun ƙara tsada da kashi 75,900% a cikin shekara 38 kawai."

Masanin ya ce kayan da muke saya suna ƙara tsada saboda hauhawar canjin kuɗaɗen waje. Kuma idan darajar naira ta ci gaba da faɗuwa, kuɗin shigo da kaya da abubuwan da ake sarrafa kayan, su ma suna ƙara tsada.

Daidaita farashin dala

Kudin dala

Asalin hoton, Getty Images

Dakta Ahmed Adamu sabon matakin na CBN zai taimaka wajen daidaita canjin kuɗi tare da janyo masu zuba jari.

A cewarsa ƙasashen duniya kamar su China da Brazil da Koriya ta Kudu da Afirka ta Kudu da Mexico da Isra'ila da Turkiyya da New Zealand sun daɗe suna amfani da wannan tsari, kuma kwalliya na biyan kuɗin sabulu.

Dakta Ahmed Adamu ya ce chanjin dala da naira yana shafar kuɗin da muke samu da wanda muke kashewa.

Ya ƙara da cewa idan dala ta yi tsada, kuɗin da muke kashewa za su ragu, to hakan kuma zai sa a samu ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki.

''Hakan zai sa kamfanoni su rage ma'aikata, kuma rashin aikin yi na kawo wa fannin tattalin arziki naƙasu, tare da rashin tsaro a ƙasa, dan haka faɗuwar darajar naira ka iya haddasa ɗumbin matsaloli a ƙasa'', in ji shi.

Shi ma Aliyu Da'u, wani tsohon ma'aikacin banki ya shaida wa BBC cewa ko da matakin ya haifar da wahala da farko, to a ƙarshe 'yan ƙasar za su yi maraba da shi.

''Hakan zai sa a samu daidaiton farashin dala, hakan zai sa mutanen da ke zuwa wajen gwamnati karɓo dala domin sayar da ita a kasuwar bayan fage, za su daina, domin farashin kusan ɗaya ne a ko'ina'', in ji shi.

A cewar tsohon ma'aikacin bankin, matakin zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin ƙasa, domin kuwa masu zuba jari daga ƙasashen waje za su shigo, sannan za su sayar da dalar da ke hannunsu a farashin da kasuwa ta kaya, maimakon a baya da CBN ke ƙayyade farashin dalar.

Godwin Emefile

Asalin hoton, CBN

Bayanan hoto, Godwin Emefile

Matsalar tattalin arziki na ɗaya daga cikin ƙalubanen da sabon Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya gada ya kuma yi alƙawarin shawo kansu.

Dala ta fuskanci tashin farashi da ba a taba gani ba a lokacin tsohon gwamnan CBN Godwin Emefiele wanda shugaba Tinubu ya dakatar a makon jiya.

Daidaita farashin dalar da cire tallafin mai su ne manyan matakai da Shugaba Tinubu ya ɗauka cikin gaggawa bayan rantsar da shi.

Kasuwannanin musayar kudi da dama a karkashin Godwin Emefiele sun haifar da karancin kuɗin kasashen waje kuma masu zuba jari sun sha wahala wurin fitar da kudadensu daga kasar, wadda ta fi kowace girma a Afirka.