Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Pulisic na dab da komawa AC Milan
Dan wasan gaban Amurka Christian Pulisic na dab da komawa AC Milan daga chelsea kan farashin fam miliyan 20.
Pulisic, mai shekaru 24, ya rasa wuri a Stamford Bridge kuma ana shirin zai yi gwajin lafiya a asbitin Milan.
Ya koma Chelsea ne daga Borussia Dortmund a kan fam miliyan 57.6 a shekarar 2019 wanda ya sanya ya zama dan wasa mafi tsada daga Arewacin Amurka.
Pulisic ya zura kwallaye 26 a wasanni 145 kuma ya buga wasan karshe na gasar zakarun Turai a 2021 da suka doke Manchester City.
Komawarsa Seria A, na nufin zai hadu da tsohon abokin wasansa a Chelsea, Ruben Loftus-Cheek, wanda shi ma ya koma Milan cikin makonnin da suka gabata.
Chelsea ta raba jiha da manyan 'yan wasa a lokacin musayar ƴan wasa na bana wanda suka hada da Kai Havertz da ya koma Arsenal da Mateo Kovacic da zai koma Manchester City da kuma Mason Mount wanda zai koma Manchester United.
Cesar Azpilicueta ya koma Atletico Madrid, kuma Kalidou Koulibaly ya tafi Al-Hilal, Edouard Mendy ya sanya hannu kan yarjejeniya da Al-Ahli yayin da N'Golo Kante ya koma Al-Ittihad.