'Sojoji sun kifar da gwamnatin Madagascar'

Dozens of people march in the Madagascar capital of Antananarivo, with their fists in the air.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Matasa sun fara zanga-zanga ne don nuna fushi da matsanancin ƙarancin wuta da ruwa
    • Marubuci, Sammy Awami
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
    • Aiko rahoto daga, Antananarivo
    • Marubuci, Danai Nesta Kupemba
  • Lokacin karatu: Minti 4

Wani muhimmin ɓangare na rundunar sojin Madagascar ya ce ya ƙwace iko daga gwamnatin shugaban ƙasar Andry Rajoelina, bayan kwashe makonni matasa na zanga-zanga a ƙasar.

Lokacin da suka yi jawabi a gaban fadar shugaban ƙasar, shugaban rundunar CAPSAT, Kanar Michael Randrianirina ya ce rundunar sojin za ta kafa gwamnati tare da gudanar da zaɓe a cikin nshekara biyu.

Haka nan babban sojan ya dakatar da ayyukan wasu muhimman ma'aikatun gwamnati, kamar hukumar zaɓe ta ƙasar.

Zanga-zangar matasa ƴan bana-bakwai za ta yi tasiri kan sauye-sauyen da za a yi saboda "an ƙirkiri hanƙoron ne a kan tituna, kuma wajibi ne mu martaba buƙatunsu" in ji shi.

Sojoji da sauran masu zanga-zanga sun yi ta nuna farin ciki kan matakin kifar da gwamnatin Shugaba Rajoelina, inda dubban mutane suka taru suna kaɗa tuta a Antananarivo, babban birnin ƙasar.

Kotun kundin tsarin mulki ta ƙasar ta ayyana Kanar Randrianirina a matsayin sabon jagoran ƙasar, duk kuwa da cewa wani saƙo da ya fito daga ofishin shugaban ƙasar ya ce har yanzu Rajoelina ne shugaba, tare da yin watsi da abin da ya bayyana "yunkurin juyin mulki."

Yanzu haka babu wanda ke da masaniya kan inda Rajoelina yake, sai dai ya ce yana samun mafaka a wani "wuri mai tsaro" bayan zargin sojoji da ƴan siyasa da "neman rayuwarsa", lamarin da rundunar CAPSAT ta musanta hannu a ciki.

Rahotannin da ba a tabbatar da gaskiyarsu ba sun bayyana cewa an fitar da shugaban ƙasar a wani jirgi mallakin rundunar sojin Faransa.

Kanar Randrianirina ya shaida wa BBC cewa a yanzu "Madagascar ta zamo ƙasa mai fama da tashin hankali".

"Tashin hankali saboda babu shugaban ƙasa - ya tsere waje."

Hargitsi ya tashi a ƙasar ne cikin mako biyu da suka gabata bayan da matasa suka jagoranci zanga-zangar adawa da matsanancin ƙarancin ruwa da wutar lantarki a faɗin ƙasar.

Bayanan bidiyo, Jawabin jagoran sojojin da suka yi iƙirarin karɓe iko a Madagascar

Ba da daɗewa ba ne zanga-zangar ta yaɗu, lamarin da ya nuna rashin gamsuwar al'umma da gwamnatin Rajoelina, sanadiyyar yawaitar rashin aikin yi, da rashawa da kuma tsadar rayuwa.

Masu zanga-zanga sun yi artabu da jami'na tsaro, lamarin da ya haifar da kashe aƙalla mutum 22 da kuma jikkata sama da 100, kamar yadda MDD ta bayyana.

Sai dai gwamnatin ƙasar ta yi watsi da alkaluman, inda ta ce an samar da su ne ta hanyar "jita-jita da bayanan ƙarya."

Rundunar CAPSAT wadda ta goyi bayan Rajoelina a lokacin da ya hau kan mulki a shekara ta 2009, ta shiga cikin zanga-zangar a ranar Asabar.

A baya an yi wa shugaba Rajoelina - wanda ɗan kasuwa ne - kallon mutumin da zai samar da sabuwar turbar inganta ƙasar Madagascar.

Mutumin ya zama shugaba ne yana ɗan shekara 34, inda ya zamo shugaban ƙasa mafi ƙanƙantar shekaru a nahiyar Afirka, ya jagoranci ƙasar na tsawon shekara huɗu kafin ya sake komawa kan mulki bayan lashe zaɓe a shekara ta 2018.

Video of President Andry Rajoelina on an tablet screen

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Andry Rajoelina ya yi jawabi ta shafin facebook a ranar Litinin
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rajoelina ya fara yin baƙin jini ne bayan zargin da aka yi masa na bai wa ƴan'uwa da abokai muƙaman gwamnati da kuma ayyukan rashawa, zargin da ya musanta.

Duk da alamun da suka nuna cewa iko ya sulluɓe daga hannunsa, ya ci gaba da ƙoƙarin cusa kansa cikin al'amura.

Rajoelina ya yi yunƙurin rushe majalisar dokokin ƙasar kafin ƴan adawa su kaɗa ƙuri'ar tsige shi daga muƙami bisa zargin watsar da aikinsa, sai dai yunƙurin nasa bai kai ga nasara ba.

Ƴan majalisa sun kaɗa ƙuri'ar tsige Rajoelina da ƙuri'a 130, sai guda ɗaya da ba a kaɗa ba. Hatta ƴan jam'iyyarsa ta IRMAR sun kaɗa ƙuri'ar tsige shi da gagarumin rinjaye.

Rajoelina ya yi watsi da ƙuri'ar, tare da bayyana ta a matsayin haramtacciya.

Tarayyar Afirka (AU) ta gargadi sojoji daga "tsoma baki" cikin lamurran siyasar Madagascar tare da yin watsi da "duk wani yunƙuri na kawo sauyin da ya saɓa wa kundin tsarin Mulki."

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana lamarin a matsayin "babban abin damuwa."

Madagascar ta fuskanci jerin rikita-rikitar siyasa a shekarun baya-bayan nan.

Ƙasar na daga cikin mafiya talauci a duniya, inda kashi 75% na al'ummarta ke rayuwa cikin ƙangin talauci, a cewar Bankin Duniya.