Masifar yunwa ta tilasta wa 'yan kasar Madagascar cin ƙwari

Yara 'yan kasa da shekara biyar akalla rabin miliyan ne ke cikin hadarin kamuwa da cutar tamowa, in ji Majalisar Dinkin Duniya

Asalin hoton, WFP/Tsiory Andriantsoarana

Bayanan hoto, Yara 'yan kasa da shekara biyar akalla rabin miliyan ne ke cikin hadarin kamuwa da cutar tamowa, in ji Majalisar Dinkin Duniya
    • Marubuci, Daga Andrew Harding
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa correspondent, BBC News

Kasar Madagascar na dab da fuskantar "ja'ibar yunwa mai nasaba da sauyin yanayi" irinta ta farko a duniya, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, wanda ta ce dubban daruruwan mutane sun riga sun fada cikin "bala'i" na matsananciyar yunwa da karancin abinci bayan shafe shekaru ba tare da saukar ruwan sama ba.

Farin - mafi muni a cikin shekaru arba'in da suka gabata - ya yi wa kebantattun al'umomin manoma da ke kudancin kasar ta'annati, da ya sa iyalai da dama suka koma cin kwari don su rayu.

"Wadannan su ne abubuwan da matsananciyar yunwa kan haifar kuma sauyin yanayi ne ke haifarwa ba rikici ba,'' in ji Shelley Thakral ta Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP).

Majalisar Dinkin Duniya ta kididdige cewa mutane 30,000 ne yanzu haka ke fuskantar karancin abinci mafi girman da matakinsa ya kai yadda kasashen duniya suka san da shi - mataki na biyar - kuma akwai nuna damuwa game da karuwar yawan adadin mutanen da matsalar za ta shafa a yayin da kasar ta Madagascar ke shirin shiga "lokacin jiran tsammani" - da ke tsakanin lokacin shuka da kuma girbe amfanin gona da suka saba fuskanta a ko wace shekara

"Ba a taba ganin irin wannan yanayi ba. Wadannan mutane ba su aikata wani abu da zai haddasa sauyin yanayi ba. Ba sa amfani da kwal ko wani makamashi … amma duk da haka suna fuskantar sauyin yanayi," in ji Mis Thakral.

A kauyen Fandiova da ke gundumar Amboasary, iyalai da dama sun nuna wa tawagar hukumar abincin ta Majalisar Dinkin Duniya WFP da suka kai ziyara irin farin da suka koma ci.

In the absence of food people eat locusts to survive.

Asalin hoton, WFP/Tsiory Andriantsoarana

Bayanan hoto, Babu amfanin gona kana yanzu mutane na dogara da cin kwari da ganyayen cactus

"Nakan yi iya bakin kokarina wajen wanke kwarin amma kuma kusan babu ruwa," in ji Tamaria, wata mata mai 'ya'ya hudu.

Ta ce "Ni da 'yayana mukan ci wannan a kullum har na tsawon watanni takwas, ba mu da wani abinci kana babu ruwan sama da za mu iya girbe abin da muka shuka".

"Yanzu ba mu da abin da za mu ci sai ganyen cactus," in ji Bole, wata mai 'yaya uku, da ke zaune a kan busasshiyar kasa.

Ta ce mijinta bai dade da mutuwa ba saboda yaunwa, kamar wani makwacinta, wanda ya bar mata karin wasu 'ya'ya biyu da za ta ciyar.

"Me zan iya cewa? Rayuwarmu duk ta kare a neman ganyen cactus akai-akai don mu rayu.

Tattalin ruwa

Duk da cewa kasar ta Madagascar na yawan fuskantar fari kana matakai daban-daban na sauyin yanayi da mahaukaciyar guguwar El Nino ka haddasawa na shafar rayuwarsu, kwararru sun yi amanna za a iya danganta sauyin yanayi da halin da suka shiga a yanzu.

"Bayan rahoton da kungiyar IPCC ta fitar mun fahimci karuwar yanayin bushewar kasa a Madagascar. Kuma cewa akwai yiwuwar hakan ya kara ta'azzara muddin sauyin yanayin ya ci gaba da faruwa.

"A hanyoyi da dama za a iya ganin wannan a matsayin babban abu da zai sa mutane su sauya dabi'unsa", in ji Dakta Rondro Barimalala, wani masanin kimiyya dan kasar Madagascar da ke aiki da Jami'ar birnin Cape Town Afirka Ta Kudu.

Yayin da yake duba bayanan da aka tattara na yanayi a Jami'ar Santa Barbara a jihar California, daraktan Cibiyar Kare Hadurran Sauyin Yanayi Chris Funk, ya tabbatar da alaka da "dumamar iskar sararin sama", kana ya ce akwai bukatar kasar Madagascar su yi aiki tukuru wajen alkinta ruwa.

"Muna ganin akwai abubuwa da dama da suka kamata a yi a cikin gajeren lokaci. Za mu iya yin has ashen lokacin da za a samu saukar ruwan sama da ya wuce kima kana manoma za su iya amfani da wannan bayani wajen kara yawan amfanin gonar da suke nomawa. Ba mu da rashin karfin da ba za mu iya fuskantar sauyin yanayi ba," in ji shi.

Matsanancin fari ya busar da kasar noma a kudancin kasar

Asalin hoton, Ocha/Reuters

Bayanan hoto, Matsanancin fari ya busar da kasar noma a kudancin kasar

Yanzu haka ana fuskantar mummunan tasirin da matsalar fari ta haifar a baya-bayan nan har ma a kudancin kasar ta Madagascar, da ya tilasta wa kananan yara da dama barace-barace a kan titina don samun abinci.

"Farashin abinci a kasuwa ya yi tashin gwauron zabi - ya ninka sau uku zuwa hudu. Mutane na sayar da filayensu don sayen abinci," a cewar Tshina Endor, da ke aiki kungiyar bayar da agaji ta Seed a Tolanaro.

Abokin aikinta Lomba Hasoavana, ya ce shi da sauran mutane sun koma kwanciya a gonakin rogo don kokarin kare amfani gonar ta su daga mutanen da ke da tsananin bukatar abinci, amma kuma hakan na da hadarin gaske.

"Za ka iya jefa rayuwarka cikin hadari. Akwai matukar wahala sosai saboda dole in rika tunanin yadda zan ciyar da kai na da iyalaina,'' ya ce, yana mai karawa da cewa: "Komai ya zama ba shi da tabbas game da yanayin a yanzu. Babbar ayar tambaya ce - shin me zai fari a gobe?"