Satar garin tuwo ta tilasta ba da katin shaida a wurin niƙa a Kano

Bayanan bidiyo, Bidiyon bayanin yadda ake satar gari a wajen niƙa a Kano

A baya da wuya ka ji an ce an sace garin tuwo a wurin niƙa duk da cewa a kan samu yanayin da ake yin musaya, wato wani ya ɗauki na wani amma ya bar nasa bisa kuskure.

To amma a yanzu mazauna wasu unguwanni a birnin Kano, na ƙorafi dangane da yadda garin tuwonsu ke ɓacewa a wajen niƙa a ƴan kwanakin nan.

Wannan ne dai ya sanya wasu masu inji da ke yin niƙan suka samar da hanyar rage sace-sacen, inda suka fito da bai wa duk wanda ya kai niƙa shaidar hakan.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da wani rahoton Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce an samu karin mutum fiye da milyan guda da ke fama da karancin abinci a jihar Kano sakamakon annobar korona.

Har wa yau, wasu na alaƙanta al'amarin da irin matsin rayuwar da jama'a suka samu kansu a ciki saboda tashin gwauron zabi da farashin kayan masarufi ya yi sakamakon karin kudin man fetur da wutar lantarki da gwamnatin Najeriya ta yi.