Matasa na hambarar da gwamnatoci a ƙasashe amma ko za su iya kawo sauyi?

Asalin hoton, Donwilson Odhiambo / Getty Images
- Marubuci, Luis Barrucho and Tessa Wong
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 8
Daga Morocco zuwa Madagascar zuwa Paraguay zuwa Peru, matasa da ake wa lakabi da Gen Z masu shekara 13 zuwa 28, na jagorantar zanga-zangar fushinsu da gwamnati inda suke buƙatar canji.
Bayan samartaka da yawancin matasan da ke wannan zanga-zanga a ƙasashe daban-daban wani abu kuma da ya zama na bai ɗaya a tsakaninsu wanda ke ƙara angiza su boren shi ne shafukan sada zumunta - to amma ƙwararru na gargaɗin cewa wannan kafa ka iya zama tushen lalacewar matasan.
Zanga-zanga a kan ƙarancin ruwa da wutar lantarki, ta kawo ƙarshen gwamnatin Madagascar.
Zanga-zanga a kan cin hanci da rashawa na nuna son kai wajen naɗin muƙamai ta kai ga saukar firaminista a Nepal.
Matasan Kenya da ake wa lakabi da Gen Z, sun bazama a kan tituna da kuma shafukan sada zumunta don neman a yi sauye-sauye a harkokin gwamnati tare kuma da neman gwamnatin ta baje komai a faifai su gani.
Wannan rukuni na matasa na hamɓarar da gwamnatoci - to amma abin tambaya a nan shi ne ko zanga-zanga a shafukan sada zumunta ka iya kawo canjin da ake buƙata?

Asalin hoton, Klebher Vasquez / Anadolu via Getty Images
A ƙasar Peru, dandazon matasa sun yi tattaki zuwa majalisar dokoki, tare da direbobin tasi da bas-bas, domin nuna ɓacin ransu a kan badaƙalar rashawa da kuma matsalar tsaro da ke ƙaruwa a ƙasar.
Ma'aikatan wucin-gadi na zanga-zanga a Indonesia saboda yanke musu wasu tsare-tsare na jin daɗinsu.
Can a Moroko ma matasa sun yi zanga-zangar ƙin jinin gwamnati mafi girma cikin shekaru, suna bukatar a inganta fannin lafiya da ilimi, kuma suna suka kan kashe biliyoyin kuɗi a kan filayen wasan cin Kofin Duniya na ƙwallon ƙafa.

Asalin hoton, Abu Adem Muhammed / Anadolu via Getty Images
A duka wannan zanga-zanga, shafukan sada zumunta da muhawara sun taka muhimmiyar rawa a fannin bayar da labarai da goyon baya da tsare-tsare da kuma koyon abubuwa a tsakanin kasashe.
Shafukan na sada zumunta da muhawara sun kasance wata kafa ta baya-bayan nan da matasa ke amfani da ita wajen haɗa kai da gudanar da zanga-zanga in ji Janjira Sombatpoonsiri, ta cibiyar nazarin harkokin duniya da yanki ta Jamus (German Institute for Global and Area Studies).
Jerin zanga-zangar sun haɗa da ta ƙasashen Larabawa ta shekarar 2010-11, da wadda aka yi a Amurka a 2011 (Occupy Wall Street) da wadda aka yi kan fatara da talauci a Sifaniya a 2011–12, da ta rajin tabbatar da dumukuradiyya a Thailand a 2020–21, da ta Sri Lanka a 2022 da kuma wadda aka yi a Bangladesh a 2024.

Asalin hoton, Akila Jayawardana / NurPhoto via Getty Images
'Cin hanci ya samu gindin zama'
Steven Feldstein, babban masani a kungiyar kwararru ta Amurka ta wanzar da zaman lafiya ( Carnegie Endowment for International Peace), ya yi nuni ga yadda aka samu cigaba kama daga matakin aikewa da sakonnin rubuta ta waya (text), zuwa juyin-juya-hali na 2001 a Philippines.
Ya ce, ''ba wani sabon abu ba ne yadda matasa ke amfani da hanyoyin fasaha na zamani wajen shiryawa da gudanar da zanga-zanga.''
To amma bambancin a yanzu shi ne irin cigaban da ake samu na fasaha - inda a yanzu mutane da dama ke amfani da waya, da shafukan sada zumunta da muhawara, da manhajoji na aikawa sa sakonni da kuma na baya-bayan nan na kirkirarriyar basira, wanda hakan ya haifar da sauki wajen tara jama'a.

Asalin hoton, Prabin Ranabhat / AFP via Getty Images
"Wannan shi ne abin da matasa suka taso da shi - yadda suke sadarwa a tsakaninsu kenan," in ji Mista Feldstein.
Hotuna da sakonni na tafiya mai nisa kuma cikin sauri, fiye da a baya, wanda hakan ke kara fushi da goyon baya.
Athena Charanne Presto, masaniya a kan halayyar dan'Adam a Jami'ar National University, ta Australia ta ce: "Shafukan sada zumunta sun mayar da abin da ake kallo tamkar salo na rayuwa zuwa wata hanya ta siyasa, kuma yawanci matattara ta bayyana koke.
''Yawanci idan aka yi maganar rashawa a rahotanni ko a shari'a ba a daukar lamarin da muhimmanci sosai - amma idan mutane suka ga abin a wayoyinsu suna yarda da abin sosai,'' in ji Presto.

Asalin hoton, Instagram / sgtthb
Abin da ya faru a Nepal kenan a watan Satumba inda hoton dan wani dansiyasa da aka sanya a shafin Instagram, inda ya tsaya a kusa da wata bishiyar Kirsimeti da kwalaye na kayan kawa masu tsada ya janyo gagarumar zanga-zanga - lamarin bai tsaya a kasar ba har sai da ya dangana da Philippines.
''Abin ya yi naso zuwa Philippines domin matasa a can na ganin abu ne da daman suka riga suka sani - 'yansiyasarsu na rayuwa ta facaka,'' in ji Ms Presto.
"Dangane da Philippines, abin ya ta'allaka ne da yadda 'yansiyasa suke sata daga kudaden ayyukan magance matsalar ambaliya, yayin da ruwa ke ci gaba da hallaka 'yan kasar."

Asalin hoton, Delphia Ip / NurPhoto via Getty Images
Shafukan sada zumunta da muhawara sun samar da dama ta yadda masu zanga-zanga ke musayar dabaru na gudanar da gangaminsu a kasashe.
Misali a nan shi ne yadda masu zanga-zanga a Thailand suka yi dabara irin ta masu zanga-zanga a Hong Kong, inda suka yi amfani da Telegram wajen bagarar da 'yansanda da suka kasa suka tsare a inda da farko aka tsara zanga-zanga, suka sauya waje cikin dan lokaci.
Wannan dabara ta taimaka wa masu zanga-zanga kauce wa sa-ido da kame.
Kaifi biyu

Asalin hoton, Anusak Laowilas / NurPhoto via Getty Images
Yayin da mutane ke amfani da shafukan intanet waje nuna fushinsu a kan gwamnati, hukumomi da dama masu mulkin kama-karya na amfani da karfi da kuma rufe kafofin sadarwa don dakile hakan.
To amma kwararru na gargadi da cewa irin wannan mataki galibi ba ya haifar da sakamakon da aka nufa inda reshe yake juyewa da mujiya - matakin ya harzuka mutane su yi zanga-zangar da ta fi ta baya - musamman ma idan aka yada hotuna kai tsaye na yadda jami'ai ke ta'addanci a kan mutane.
Irin abin da ya faru a Bangladesh kenan a 2024, inda gwamnati ta rufe hanyoyin intanet a lokacin zanga-zangar Awami League, jami'ai kuma suka rika harbi a kan dalibai.
Hoton kisan wani dalibi Abu Sayed, da 'yansanda suka harba, ya harzuka jama'a zanga-zangar ta kara kamari.

Asalin hoton, NurPhoto via Getty Images
Haka abin ya faru a can Sri Lanka da Indonesia da kuma Nepal, inda kisan masu zanga-zanga ya harzuka mutane, suka kara tsaurara bukatunsu ga hukumomi a wasu kasashen ma har abin ya kai ga hambarar da gwamnatoci.
Duk da cewa shafukan sada zumunta na karfafa zanga-zanga to amma kuma tana iya haifar da rarrabuwar kai da danniya.
Gangamin da ba shi da kwakkwaran jagoranci na bayar da damar rarrabuwa da rauni da za a iya musu kutse da sauya akida ko ra'ayi da manufa.

Asalin hoton, Anusak Laowilas / NurPhoto via Getty Images
A Thailand, masarauta da muhawarar intanet , sun haifar da nakasu ga gangamin rajin dumukuradiyya na 2020, bayan da aka watsa wasu rubuce-rubuce da ke dauke da manufa ta kwaminisanci da ta nuna wariya ga kawayen masu zanga-zangar, inda hakan ya haddasa rarrabuwar kai.
Sannan kuma a Nepal da Bangladesh zanga-zangar da ba ta samu tsari mai kyau ba, galibi tana rikidewa ta zama tashin hankali.
Yanzu dai bincike ya nuna cewa gwamnatoci na amfani da wadannan kafafe na intanet wajen yakar masu raji da fafutuka.
''Tun bayan juyin-juya-hali na kasashen Larabawa, gwamnatoci a yanzu sun bullo da wasu hanyoyi na sa ido, da tsaurara matakan tsuke wadannan kafofi da tsauraran dokoki na takurawa a kan masu fafutuka,'' in ji Ms Sombatpoonsiri.

Asalin hoton, Patrick Baz / AFP via Getty Images
Haka kuma kwararru na muhawara a kan tasirin zanga-zangar da aka shirya ta shafukan sada zumunta da muhawara a can gaba.
A shekarun 1980 da 1990 kashi 65 cikin dari na zanga-zangar da ba ta makami ba ta yi nasara, kamar yadda wani bincike na Jami'ar Harvard ya nuna, to amma a tsakanin 2010 da 2019, wannan ya ragu zuwa kashi 34 cikin dari.
Ko da kuwa zanga-zanga ta kawo sauyi a gwamnati, ba za a iya tabbatar da dorewar canjin da sauyin gwamnatin zai yi ba.
Zanga-zanga za ta iya rikidewa ta zama yakin basasa - kamar yadda ya faru a Syria da Myanmar da Yemen - inda hakan ke sa bangarori masu gaba da juna su shiga fafutukar neman mulki.
Ko kuma masu mulkin kama-karya su dawo su kankane mulki kamar yadda aka gani a Masar da Tunisia da Serbia, kasancewar sauye-sauyen da aka yi sun kasa hambarar da tsarin da gwamnatocin baya suka kafa.
Abin ya wuce shafukan sada zumunta

Asalin hoton, FITA / AFP via Getty Images
Mista Feldstein ya ce: "Ainahi, [shafukan sada zumunta] ba a yi su domin canji na tsawon lokaci ba.
Kwararru na ganin akwai bukatar a hada dabaru na amfani da shafukan sada zumunta da kuma na da, wadanda ake amfani da su irin su zanga-zanga da yajin aiki da taruka kamar yadda Ms Sombatpoonsiri ta ce.
Akwai kuma bukatar hadaka tsakanin kungiyoyin masu fafutuka da jam'iyyun siyasa da 'yan gwagwarmaya na hukumomi da kungiyoyin shafukan sada zumunta.











