Ta yaya za ku gane aboki na gaskiya?

Wasu ƴanmata a ƙasar Habasha

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Yayin da yawancin waƙoƙin soyayya ke magana kan daɗi da kuma fargaba da ke cikin soyayya, abota tsakanin mutane ita ma kan zama mai ƙarfi da kuma tsarkakiya.

Ga yawancin mutane, samun sabbin abokai ko ɗorewar daɗaɗɗiyar alaƙa kalubale ne na gaske, sannan rugujewar alaƙa da aboki na cike da raɗaɗi kamar kawo karshen soyayya tsakanin masoya.

Ɗan'adam ya ɗauki abota da muhimmanci. Kamar yadda masanin Falsafa Aristotle ya rubuta a ƙarni na huɗu, "Ba wanda zai zaɓi ya rayu ba tare da abokai ba," ko da kuwa za su samu dukkan abubuwa masu kyau da suke buƙata.

An fi sanin Aristotle kan shaharar da ya yi da kuma tasirinsa a ɓangaren kimiyya, siyasa, kayan ƙawa, amma ba ga rubuce-rubucensa kan ɓangaren abota ba.

Abota dai ta shafe tsawon lokaci kamar yadda ɗan'adam ya daɗe a doron ƙasa.

A nan, ga wasu darussa guda uku kan aboki na gaske da Aristotle ya bayyana.

1. Ana ganewa da kuma jin tasirin abokan gaskiya

Abota

Asalin hoton, Getty Images

Darasi na farko da Aristotle ya fahimtar da mu kan ma'anar abota ita ce: yarda da juna. Ba kamar iyaye ko ƴan uwantaka ba, abota tana wanzuwa ne kawai idan ɓangarorin biyu suka san muhimmancinta.

Kowanne daga cikinsu kan yi wa juna fatan alheri - hakan ne zai sa a samu kyakkyawar alaƙa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kamar yadda Aristotle ya ce: "Saboda haka, ya dace mutum ya kasance yana yi wa abokinsa fatan alheri sannan shi ma ya yi haka, kuma su fahimci wannan game da juna."

Aristotle ya misalta wannan batu da misalin alaƙar da ba ta dace ba: wani irin abota ta ɓangare ɗaya wanda a cikinta ne mutum ya ji yana son wani - ko ma su yi tunanin sun san wani mai ƙarfin faɗa a ji - wanda ba su taɓa ganinsa ba.

A cikin misalinsa, masanin falsafan ya yi misali ga masoyin ɗan wasa wanda zai yi wa gwaninsa fatan alkhairi kuma yana so ya ga ya yi nasara.

Amma tun da ɗan wasan bai gode masa ba ko ma jinjina masa, to su ba abokai bane.

Maganar Aristotle tana kan gaskiya musamman idan muka duba zamanin yau. Babu ta yadda mutum zai yi abokatanka da wani a dandalin Facebook in ba wanda yake son ya karɓi buƙatarsa ta zama aboki ba.

Sai dai, za ka iya bibiyar wani a shafukan sada zumunta ba tare da ya san ka ba.

Yana da matukar wahala a bambanta abota ta gaske da ta ƙarya a zamanin yau.

2. Ire-iren abota uku

Aristotle ya bambanta ire-iren abota guda uku: Abota ta amfani, ta jin daɗi da kuma ta hali.

Yayin da irin abota ta hali ta kasance wadda ta fi, irinsu ba su da yawa. Yana ɗaukar tsawon lokaci kafin a gane halin mutum - kuma sai an daɗe kafin a iya riƙe irin abokin.

Tun da lokaci abu ne kayyadadde, yawancin abota ta ta'allaka kan ta yau da kullum ko kuma na jin daɗi.

Wasu lokuta ɗalibai na suna kalubalanta cewa abota ta amfani, ba abokantaka ba ce. Ta yaya mutane biyu da ke amfani da juna za su zama abokai? Duk da haka, idan dukkanin ɓangarorin biyu suna kallon abokantakarsu ta fuska ɗaya, ba sa amfan da juna wajen raɗin kansu, sai dai samun alfanun juna.

Kamar yadda Aristotle ya bayyana, "Bambance-bambance tsakanin abokai yakan taso lokacin da suka gano yanayin abokantakarsu ba wanda suke so bane."

Idan abokiyar karatunka tana tunanin ku abokai ne saboda kuna tare, amma abotar ta dogara ne kan cewa ta iya lissafi, za ta iya jin zafi.

Amma idan dukkanku kuka fahimta, alal misali cewa ɗaya yana buƙatar ƙara ƙwazo wajen lissafi, ɗayan kuma a wajen iya rubutun, za ku iya samun kyakkyawar fata da mutunta juna.

A haƙiƙa, ƙayyadaddun yanayin abota mai amfani na iya zama ainihin abin da ke sa shi fa'ida.

Yi la'akari da nau'in abota mai taimako na zamani: ƙungiyoyin tallafi na kan layi.

A taƙaice, darasi na biyu da Aristotle ke koyarwa a nan shi ne akwia gurbi na kowane irin abota - kuma abota tana aiki ne idan aka fahimci tushenta.

Abota

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sanin halin da kowane ɓangare ke ciki a kodayaushe, yana da muhimmanci wajen samun abota ta gari.

3. Abota mai ɗorewa

Daga karshe, akwai abin da Aristotle ke son bayyanawa kan abin da yake sa abota ta ɗore. Ya kalubalanci cewa abota abu ne da ya kamata a kula da ita yadda ya kamata: Kamar yadda motsa jiki akai-akai ke sa lafiyar jiki ta ɗore, abota na jimawa ne idan aka riƙa yin abu a tare.

Don haka me zai faru idan kai da abokinka kuka ƙasa yin abubuwa tare?

Aristotle ya ce: "Abota....waɗanda ba sa ɗasawa yadda ya dace, amma suna da ɗabi'un yin abokantaka. Rabuwa ba ta tarwatsa abokantaka, duk da cewa tana hana ta gudana yadda ya kamata."

Binciken da aka yi a baya-bayan nan, ya tabbatar da cewa: abota za ta iya ɗorewa ko da ba a yin abubuwa tare da juna, amma idan hakan ya daɗe, zat ruguje."

Watakila ra'ayin Aristotle ya rasa darajarsa, ganin cewa tsarin sadarwa na zamani sun sauya - inda hakan ke sanya abota ta ɗore ko da ana nesa da juna.

Amma ko da rabuwa ta zahiri ba ta nufin ƙarshen abota ba, har yanzu akwai gaskiya a darasin Aristotle.

Bincike ya nuna cewa duk da fasaha, mutanen da suka rage ayyukansu a cikin shekarar farko ta cutar korona, sun ga raguwa matuka kan ingancin abokantakarsu.

A yau, kamar yadda yake a tsohuwar Athens, abokai su ci gaba da yin ayyuka tare.

Duk sauyawar zamani, rubuce-rubucen Aristotle kan abota har yanzu suna da tasiri.