Wane ne jagoran Hamas da aka kashe a Beirut?

Asalin hoton, REUTERS
Isra'ila ta dage cewa halaka jagoran Hamas a birnin Beirut, ba hari ba ne a kan ƙasar Lebanon, yayin da abokan gabanta ke gargaɗin "hukunci" a kan mutuwarsa.
Wani mai magana da yawun Isra'ila ya ce Saleh al-Arouri ya mutu ne a wani "hari kacokam a kan shugabancin Hamas ba tare da an taɓa 'yan ba-ruwana ba".
Hamas ta yi alla-wadai da kashe shi, yayin da ƙawarta Hezbollah ta ce abin da Isra'ila ta yi, hari ne a kan 'yancin ƙasar Lebanon.
Firaministan Lebanon, a lokaci guda, ya zargi Isra'ila da ƙoƙarin "tsunduma Lebanon cikin... fito-na-fito".
Kafofin yaɗa labaran Lebanon sun ba da rahoton cewa an kashe Arouri, mataimakin jagoran siyasa na Hamas ne, a wani harin jirgi maras matuƙi a kudancin Beirut tare da ƙarin mutum shida - kwamandojin dakarun Hamas biyu da kuma wasu 'ya'yan ƙungiyar huɗu.
Kafin mutuwarsa shi jigo ne a Rundunar Qassam, reshen soja na Hamas, kuma shi babban amini ne ga Ismail Haniyeh, shugaban Hamas. Ya kasance a Lebanon ne inda yake matsayin wani jami'i mai sadarwa tsakanin ƙungiyarsa da abokiyar ƙawancenta Hezbollah.
Wane ne shugaban Hamas da aka kashe a Beirut?
Ƙiris ya rage mai magana da yawun Isra'ila Mark Regev ya tabbatar da cewa ƙasarsu ce ta kai harin da ya yi sanadin wannan kisa, wani matsayi da jami'an Isra'ila ke ɗauka, amma dai ya faɗa wa MSNBC:
"Duk wanda ya yi hakan, a bayyane take ƙarara cewa wannan wani hari ne da aka kai ba ga ƙasar Lebanon ba.
"Ai ba ma hari ba ne a kan Hezbollah, ƙungiyar 'yan ta'adda.
"Duk wanda ya kai harin, ya kai hari ne taƙamaimai a kan shugabancin Hamas. Duk wanda ya aikata hakan, da ma yana da matsala da Hamas. Wannan a bayyane take."

Asalin hoton, AFP

Asalin hoton, AFP
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Arouri, ɗan shekara 57, shi ne jagoran Hamas mafi girma da aka kashe tun lokacin da Isra'ila ta fara yaƙi da ƙungiyar bayan harinta na ranar 7 ga watan Oktoba.
A ranar, zugar 'yan bindigan Hamas ta mamaye Isra'ila inda ta auka wa garuruwan da ke kewaye da kan iyaka, tare da halaka kimanin mutum 1,200, mafi yawansu fararen hula, kuma suka kwashe kusan 240 zuwa Gaza a matsayin garkuwa.
Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙin soja don maida martani, tare da ayyana manufar wargaza Hamas.
Saleh Al-Arouri na cikin manyan masu muƙamai a jerin shugabannin Hamas kuma jagora a kan harkokin siyasa da tsaro.
Shi ne tsohon mataimakin shugaban Hamas a ofishinta na harkokin siyasa, kuma ya taimaka wajen samar da dakarun masu gwagwarmaya da makamai na ƙungiyar ciki har da rundunar Izzedine al-Qassam.
Ya ci gaba da kasancewa cikin harkokin soji na ƙungiyar
Saleh ya shiga ƙungiyar Hamas ne tun a 1987, sannan ya taimaka wajen kafa ƙungiyar a Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye
Yana cikin manyan jami'anta da ke da alaƙa ta ƙuƙut da Iran da kuma ƙungiyar Hezbollah wadda Iran ke marawa baya a Lebanon.
Ya zauna a gidajen yarin Isra'ila bayan fitowarsa ne ya bada gudunmawa wajen ƙulla jarjejeniyar da ta yi sanadin musayar fursunoni Falasɗina guda 1,000 da sojan Isra'ila ɗaya Gilad Shalit da aka yi garkuwa da shi tsawon shekara biyar a shekarar 2011.
A ranar 23 ga watan Oktoba na shekarar da ta gabata ne sojin Isra'ila suka ruguje gidansa da ke Gaɓar Yamma a birnin Arura da ke kusa da Ramalla. Arouri yana zaune ne a Lebanon har lokacin da aka kashe shi .
Jaridar Lebanese ta ba da rahoto cewa an kashe shi ne a wani harin jirgi maras matuƙi na Isra'ila, wanda aka kai kan offishin Hamas da ke tsakiyar birnin Dahiyeh a kudancin Beirut, tare da hallaka ƙarin mutum shida da ake tunanin su ma mambobin Hamas ne.
Ba magana ake yi a kan mutumin da aka kashe ba, amma inda aka aikata kisan. An kashe babban jami'in na Hamas ne a babbar tungar Hezbollah cikin ƙasar Lebanon, abin da zai iya jawo taɓarɓarewar al'amura a wannan matakin na yaƙi .
Firaministan Lebanon Najib Mikati ya bayyana kisan a matsayin sabon laifin yaƙi da Isra'ila ta yi amfani da shi don tsunduma Lebanon cikin sabon yaƙi.
Hezbollah ta bayyana harin a matsayin babban cin mutunci ga Lebanon da mutanenta da kuma tsaron ƙasar har ma da ƴancin iyakokin ƙasar. Sannan ta yi gargaɗin cewa wannan laifin ba zai tafi a banza ba.
Izzat Al-Rishq mamba na offishin harkokin siyasar Hamas ya bayyana harin da kisan kai na matsorata da masu ra'ayin Yahudanci 'yan mamaya.
Rundunar sojin Isra'ila ba ta ce komai ba kan wannan batu, inda ta bayyana wa BBC cewa ba ta bayar da bayananta ga kafafen labarai na ƙasashen waje .











