Najeriya ta tsallake rijiya da baya a hannun Canada

...

Asalin hoton, Getty Images

Najeriya ta sha da ƙyar a hannun Canada bayan da mai tsaron gida ta Najeriyar Chiamaka Nnadozie ta damƙe bugun fanareti a minti na 50 bayan fara wasa.

Wannan dai shi ne wasa na farko da Najeriya ta buga a gasar cin kofin duniya ta mata da ke gudana yanzu haka a ƙasashen Australia da New Zealand.

Kyaftin ɗin Canada, Christine Sinclair, wadda ta buga fanaretin na neman kafa tarihin zamma wadda ta zura ƙwallo a gasar ƙwallon ƙafa ta mata guda shida.

Alƙaliyar wasa ta bayar da bugun fanareti ɗin ne bayan samun ƙarin haske daga na'urar taimaka wa alƙalin wasa ta VAR.

Ɗaya daga cikin ƙalubalen da Najeriya ta fuskanta a wasan shi ne katin kora da aka bai wa ƴar wasa Deborah Abiodun.

Amma duk da haka Najeriya ta tsira da maki ɗaya a wasan, yayin da ita ma Canada ta tsira da maki ɗaya a rukunin B, yayin da mai masaukin baƙi Australia ke jagorantar rukunin da maki uku.

Ƴan matan na Najeriya sun yi iyakar bakin ƙoƙarinsu wajen tsare gida domin hana ƴan matan na Canada zura ƙwallo.

A wasa na gaba Najeriya za ta kara da mai masaukin baƙi Australia yayin da ita kuma Canada za ta kara da Ireland.