Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kama ƴan ƙungiyar Ansaru da ake zargi da kitsa fasa gidan yarin Kuje
Gwamnatin Najeriya ta ce jami'an tsaronta sun samu nasarar kama wasu gawurtattun ƴanbindiga, ƴan tsagin ƙungiyar Ansaru da take zargi da kitsa fasa gidan yarin kuje a shekarar 2022, har wasu fursunoni suka tsare.
Mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ne ya bayyana haka ne a taron manema labarai da ya gudana a ofishinsa da ke Abuja a ranar Asabar, inda ya ce ƴanbindigan biyu na cikin waɗanda suke nema ruwa a jallo.
"A yau ina farin ciki sanar da ku cewa mun samu gagaruwamr nasara a yaƙin da muke yi da ta'addanci ta hanyar amfani da bayanan sirri, inda muka kama manyan jagororin ƙungiyar Ansaru masu alaƙa da Al-Qaeda a Najeriya."
Sanarwar ta ƙara da cewa sun samu nasarar ce a wasu samame da suka yi a tsakanin watan Mayu da Yulin bana, inda ya ce "muka kama manyan jagororin ƙungiyar Ansaru waɗanda suka kitsa kai wasu manyan hare-hare a Najeriya a shekarun baya."
Waɗanda aka kama ɗin kamar yadda ya bayyana su ne "Mahmud Muhammad Usman wanda aka fi sani da Abu Bara'a ko Abbas ko Mukhtar, wanda shi ne Amir, da kuma Mahmud al-Nigeri wanda aka fi sani da Mallam Mamuda, wanda shi ne shugaban ma'aikatan Abu Bara'a kuma mataimakinsa."
Ribadu ya ce Mamuda ya samu horo ne a ƙasar Libya a tsakanin 2013 zuwa 2015 a ƙarƙashin wasu ƴanbindiga daga ƙasashen Masar da Tunisia da Aljeriya da suka ƙware wajen amfani makamai da nakiyoyi.
Daga cikin manyan hare-haren da suka kitsa, kamar yadda Nuhu Ribadu ya bayyana akwai harin gidan yarin Kuje da aka yi a shekarar 2022 da hari a wajen haƙar ma'adinin uranium na Nijar da garkuwa da wani Bafaranshe mai suna Francis Collomp a Katsina da sace Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar Uba a shekarar 2019 da sace Sarkin Wawa.
"Haka kuma suna da alaƙa da ƴanbindiga a yankin Maghreb, musamman Mali da Nijar da Burkina Faso."
Nuhu Ribadu ya ce "kama mutanen biyu, waɗanda aka daɗe ana nemansu ruwa a ƙasashen duniya babbar nasara ce," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa kama shugabannin zai karya lagon ƙungiyar.
"Wannan na nuna yadda Najeriya ke ƙara samun nasara a yaƙi da rashin tsaro ta hanyar amfani da bayanan sirri da kimiyya da fasaha," in ji shi, sannan ya ce jami'an tsaron ƙasar sun samu nasarar ƙwato wasu makamai da wasu bayanan da ya ce za su taimaka musu wajen samun ƙarin nasarori a gaba.
Ya ce da zarar sun kammala bincike za su tabbatar mutanen sun fuskanci hukunci.
Sannan ya yi godiya ga shugaban ƙasar Bola Tinubu da jami'an tsaron ƙasar bisa jajircewarsu, "wajen aiki ba dare ba rana domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar."
A shekarar 2022 ne dai aka kai harin a gidan yarin Kuje, inda wasu ƴanbindiga da a lokacin aka yi zargin ƴan Boko Haram ne suka fasa gidan yarin, sannan hukumomi suka ce fursunoni 879 suka tsere.