Ina ne maɓoyar Bello Turji, kuma me ya hana a kama shi ?

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 3

Da zarar an samu labarin sojoji sun kai farmaki kan ƴanbindiga a yankin arewa maso yammaci, musamman a jihar Zamfara, abin da mutane ke tambaya shi ne an kama Bello Turji?

Ko a shekarar da ta gabata, bayan kashe fitacen ɗanbindiga, Halilu Sububu, babban hafsan tsaron Najeriya Janar CG Musa ya ce saura Bello Turji ya rage, inda a cewarsa sun kusa kama shi.

A makon nan da ake ciki ma, dakarun Operation Fansan Yamma tare da haɗin gwiwar jami'an tsaron farin kaya (DSS), sun ce sun ƙwace tarin makamai a ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda ta jihar Zamfara, wanda a cewarsu, makaman na Turji ne.

Dakarun sun kai samamen ne bayan samun bayanan sirri kan masu safarar makamai daga Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya, kamar yadda kakakin rundunar, Laftanar-Kanal Abubakar Abdullahi ya sanar, inda ya ce sun ƙaddamar da farmakin ne a ranar 27 ga watan Janairun 2025, abin da ya kai ga ƙwato makaman kan hanyar Namoda zuwa Zurmi.

Da yake ƙarin bayani kan nasarar da suka samu, Abubakar ya ce suna cigaba da neman inda Bello Turji yake wanda suke nema ruwa a-jallo, wanda a cewarsa yake cigaba da tsere wa sojoji ta hanyar guduwa daga wata maɓoya zuwa wata.

Ya ce suna aiki tuƙuru domin kama Turjin domin mayar da zaman lafiya a al'ummomin da suka addaba da hare-hare.

Ganin yadda aka daɗe ana batun kama ɗanbindigar ne ya sa wasu ke zargin kamar ba a ga-damar kama shi ba ne, domin wasu na ganin an ai san maɓoyarsa.

Ina ne maɓoyarsa?

Game da inda Bello Turji yake samun maɓoya, Laftanal-Kanal Abubakar ya ce ya fi zama a Fakai.

"Daga bayanan da muke samu game da Turji, yana ɓoye ne a mahaifarsa ta Fakai da ke ƙaramr hukumar Shinkafi a jihar Zamfara. Gari ne mai muhimmanci a gare shi saboda dalilai da dama."

  • A can aka haife shi, ya san kowane lungu da saƙo
  • Gari ne wanda kogi ya shata gefensa. Akwai manyan tsaunuka da koguna inda mutum zai iya ɓoyewa.
  • Mutanen yankin suna taimaka masa da bayanai da abubuwan da yake buƙata.

Ya ce yana guduwa zuwa wasu wuraren domin ya ɓuya da zarar ya ga sojoji sun kusa da shi.

A game da wuraren da ya fi ɓoya bayan Fakai da aka fi sani, ɗan jarida mai binciken ƙwaƙwaf kan harkokin tsaro, Mannir Sani Fura-Girke, ya ce Turji bai zama a wuri ɗaya "saboda matsoraci" ne.

Ya bayyana cewa Turji yakan zauna a wasu wurare:

  • Fakai a ƙaramar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara
  • Kwashabawa kusa da dajin Tunani a ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara
  • Jajjaye a Gundumar Tubali a ƙaramar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara
  • Kamarawa a ƙaramar hukumar Isa ta jihar Sokoto

Me ya sa ba a kama shi ba har yanzu?

Sai dai a game da yadda aka gaza kama shi, kakakin sojojin ya ce ɓoye-ɓoye yake yi, amma duk da haka, "jami'anmu na Fansar Yamma suna bibiyarsa kuma suna toshe hanyoyin da yake samun tallafi kuma jama'a na ƙara aminta da mu, tare da kawo mana bayanai."

Ya ce ko kama makaman da suka yi a baya na cikin yunƙurin da suke yi na hana shi sakat, sannan ya ƙara da cewa za su kai gare shi.

A nasa ɓangaren, Fura-Girke ya ce "ya san ana farautarsa ne shi ya sa ba ya zama a wuri ɗaya. Da an gan shi a wuri kaza, sai ya canja wuri tare da tawagarsa."

Fura-Girke ya ƙara da cewa akwai wasu abubuwan da suka sa yake da wahala a kama Turji kamar:

  • Rashin samun ingantattun bayanan sirri
  • Yana da masu kwarmata masa bayanai, musamman idan sojoji sun nufa inda yake
  • Da wahala ya fito a gwabza faɗa da shi.

Ya ce, "Yawancin manyan ƴanbindiga tura yara suke yi idan ana gwabzawa, amma su suna can a ɓoye."

Ya ce a iya saninsa ba a taɓa gwabzawa da Turji ba, saboda "Galibi a kafofin sadarwa ake gwabzawa da shi; ya fito ya yi bayani ya je ya ɓoye. Amma ba ya fitowa a yi faɗa da shi kamar yadda aka riƙa yi da irin su Ali Kawaje da manyan ɓarayin daji a baya. Shi ba ya yi saboda tsoro. Sa dai maganganu na neman suna."